KYAWUNA JARAFTA TA Page 21 to 30

Zama yayi kan kujera daidai lokacin Ammi tafito daga kitchen rikeda flask tana kallon fuskanshi tace “sannu da aiki superman mai shiga rijiya, yanzun nan nagama hadamaka tea dinan zokasha koya kori sanyin daya shiga jikinka” dan murmushi yamata daidai tamikomai cup din shayin dayaji kayan kamshi karba yayi itakuma taja kujera kusadashi tace “Ya hanya” ahankali yace “Ammi yaushe zamu koma gidanmu”? “to marason zumunci anan kano zaku cigaba da zama” dasauri yadago kanshi wata hadaddiyar mata ce kyakkyawan gaske tana sanye da bakin jallabiya kesaukowa, ahankali yace “ina yini Anty” hararan shi tayi sosai tace “kai yaron nan ina kanwar mahaifinka kana kirana da Anty, abinda kike koyamai kenan Maryama? Kaf family nan bamuda yaro mara tarbiya irin Asad” sanin halinta yasa Ammi tace “stand up and greet her properly Asad” kallon Ammi yayi yanda ta gyadamai idanu yasa yatashi ahankali yana kallon kasa yace “ina yini M…um” washebaki tayi takaraso inda yake hannunta takai kan fuskanshi tace “ko kaifa Asad, kadawo lpy” kanshi akasa yace “lpy” murmushi tayi tace “ance kadawo kayi aikin nanne na youth start up forum ko da government sukai establishing right?” gyadamata kai yayi batare daya kalleta ba, cikeda gamsuwa tace “awani tasha zakuyi Channels television news” murya chan kasa yace “kowani TV station zasusa har nagama na 7days” gyadamai kai tayi tace “Masha Allah, Allah yataimaka, saikuma batun aure ko” shiru yayi sakinshi tayi tace “anyway nadawo mayi maganan da kyau, let’s go girls” tashi matan sukayi suka bita suka fice.
Daure fuska yayi sosai yanajan cup din tea dinshi zaikai baki yace “saisa banason zuwa gidan nan I don’t like her Ammi, this Anty Turai” shareshi Ammi tayi tajuya takalli Sharif dakecin abincin shi tace “you want more Sharif” “Ammi am full” kallon Asad din tayi tace “mezakaci”? kallon abincin data bubbudemai yayi sanan idanunshi suka sauka kan spaghetti da meat balls da hannu yanuna mata zubamai tayi ya karba yashiga ci ahankali bin dan nata take da kallo take, anytime taganshi mahaifinshi kawai take gani halinshi sak dana ubanshi, juyowa tayi takalli Sharif tace “baku bani labarin ciro yarinyar dakukayi daga rijiya ba” kaman jira Sharif yake yace ” Ammi I was driving fa kawai wata mata tasha gabanmu tana kuka wai mutaimaketa yarinya tafada rijiya, Ammi I was begging Asad fa yaje mucirota wai bazaiyiba gashi ba maza sai tulin uban mata kaman gidan biki duk suna kuka, shine nace musu mujeni nacirota dan nasan that’s the only thing dazai fitoda Asad daga cikin motan nan danni kadai nasan irin mugun halinshi, aiko ina shiga saigashi yataho ashedai yana sona yasan ban iya ruwaba fear of my death yasa yazo bawaidan he meant to save the girl ba, shine yashiga fa yacirota, Ammi kinsan menene” yay maganan yanajan kujera da sauri yana zama sanan yakalli Ammi dake kallonshi yace “Ammi nifa dasuketa yarinya I thought small girl ce fa tafada rijiyan saigashi Asad yafito da zankadediyan budurwa innalillahi Ammi kinga kyanta kuwa” Ammi dake sauraronshi tace “haba” dasauri yakalli Asad dake cin abincin anatse yana danna waya yace “Asad isn’t the girl beautiful” batare daya kallesu ba yace “I don’t know bankalleta ba” wani mugun tsaki yaja yace “Ammi wlh Asad dan rainin wayau ne” dan dariya Ammi tayi ganin yanda Sharif ya tunzura sosai tace “don’t mind him kaji cigaba da bani labarin” murmushi yama Ammi yace “wlh Ammi tunda nake Allah Ammi harna gama yawona across the globe ni bantaba ganin kyakkyawa irin yarinyar nanba Ammi she don’t even look Nigerian, hala half cast ce, Ammi she’s so pretty gashinta har waist, she’s so pretty I wish I can even see her again” ture plate din abincin dayagama ci Asad yayi yamike Ammi dasauri ta kalleshi tace “harka koshi? Baka cinye ba ai” gyadamata kai yayi yace “ya isheni, natafi wajen Dadda” dasauri Sharif yatashi yace “wait for me Asad” ko kallonshi baiyiba yawuce Ammi tabisu da kallo tana murmushi, Sharif is such a gentle man with a very very forgiven spirit, shikuma Asad is opposite na hakan, churarren mutum ne baka gane gabanshi da bayanshi ko itama sabida ita tahaifeshi ne saisa take iya fahimtan halinshi tass,.