LU’U LU’U 2

*2*

Abu kamar wasa sai ga k’aramar magana ta koma babba, dan kuwa fad’in k’asar Khazira da kewayenta an bincike amma babu Zafeera, a k’ank’anin lokaci sai b’atanta ya zaga duka masarautar da kewayenta, hankali ya tashi kuma ya d’ugunzuma musamman malami Dhurani da sarki Musail.

*Egypt*

Da bala’in k’arfi ya buga teburin cin abincin yana mik’ewa tsaye, a harzuk’e ya kalli dattijon dake bayanshi, ba tare da duba girma ko shekarunshi ba ya ci kwalarsa yana mai fad’in “Ina take? Ina suka kai ta? Su wa suka saceta?”

Cikin jin rad’ad’i da fafutukar k’watar kanshi ya shiga fad’in “Yallab’ai ka min rai, ban da masaniya akan komai ni ma, labari na samu daga d’an lek’en asirinmu dake masarautar Khazira.”

Sakinshi yayi da k’arfi yana sake fad’in “To su waye suka d’auke yarinyar dana jima ina jiran zuwanta? Su waye su?”

Girgiza kai yayi yace “Ban sani ba yallab’ai, kuma shi ma ya fad’a mana wasu fadawa biyu ne ake zargi da saceta, saboda su ne aka nema aka rasa a yayin da aka rasa ‘yar.”

Juyawa yayi da bala’in sauri yayi ciki yana fad’in “Ka samo min masaniya akan su, ba zan tab’a barin *lu’u lu’u* na a juji ba.”

Rusunawa yayi yace “To ranka shi dad’e.”

Saida ya ga b’acewarsa ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya juya ya fita a tank’amemen falon.

*Bayan wasu shekaru*

Sarki Musail ya sake zama mugu a gun jama’arsa, ba za’a ce yana mulkin kama-karya ba, sai dai ko ya ya mu’amula ta had’aku zaka ji ba dad’i, zalinci ne tsagwaro a cikin mulkinsa.

Kamar yanda ya zamar masa jiki yanzu ma barasar shi yake ta d’irka, babban dakarenshi na gefe a tsaye yana kallon irin tanb’elen da yake, da k’arfi aka bud’o k’ofar wanda hakan yasa dogarin saurin d’ora hannunshi akan takobinshi yana sake had’e fuska, ganin Zafreen yasa shi d’auke hannu a takobin tare da d’an rusuna mata, a wulak’ance ta wurga masa harara tare da nufa wajen mahaifinta.

Tana isa kusanshi ta tsaya duk da tana kallon bayanshi ne, cike da rashin kunya da tijara tace “Baa, wai me yasa kake neman lalata sunan masarautar nan ne akan wata b’atacciyar yarinya? Ka manta da ita mana tunda ta mutu.”

A sangarce ya juyo ya Kalle ta cikin halin maye, duk da yana namiji kuma dattijo amma kyakyawa, cikin layi yace “Ke…sha-sha-sha ce, kuma..mahaukaciya, ba za…ki gane…ba.”

Da mamaki da kuma rashin jin dad’i tace “Baa ni ce mahaukaciya? 脌 kan wannan abar?”

D’an tsaki kawai yayi tare da tureta gefe ya zauna kan kujera mai kyan gaske, a hassale ta bi bayanshi ita ma cikin shigarta ta riga da wando k’anana, sai yalwataccen gashinta data d’aure tamau a kai wanda ya fito da kyakyawar fuskarta, cike da tsiwa ta shiga fad’in “Baa wai me yasa kuke min haka? Kai da Maa gaba d’aya ba kwa kulani, babu ruwanku da damuwata bare matsalata, shin Zafeera ita kad’ai ce kuka haifa?”

D’aga kanshi yayi ya kalleta cikin muryar maye yace “Ba zaki gane ba gimbiya, da namiji ce ke da kin fahimci abinda nake ji.”

Da sauri ta matsa kusanshi ta dafa kafad’arshi tace “Baa, ka fad’a min matsalar ka zan fahimta, ni ma kamar namiji ce tunda zan iya yin komai da namiji zaiyi.”

Wani malalacin murmushi yayi yace “Ke yarinya ce gimbiya, ki je d’akinki ki kwanta kawai.”

Durk’usawa tayi tace “A’a Baa, ka fad’a min ni zan maka maganin matsalar ka, na gaji da ganinku kai da Maa kullum cikin tunanin yarinyar data jima da mutuwa.”

Cike da damuwa 脿 fuskarshi yace “Ba zaki iya ba gimbiya Zafreen, ki b’ace min daga nan.”

Mik’ewa tayi tsaye cikin sauri ta nufi in da dogarin nan yake, duk girmansa na jiki da kuma shekaru bai hanata saka k’afa ta hanb’areshi ba, sakamakon zuwan abun a bazata sai ya samu kanshi da fad’uwa k’asa, da sauri sarki Musail ya mik’e tsaye cikin layi kamar zai fad’i yace “Ke… Wai !”

Sai kuma yayi shiru saboda wuk’ar dogarin data d’auka a jikinshi ta d’orata a mak’ogwaron dogarin, hankali tashe dogarin ya zare ido dan yasan tsaf Zafreen zata huda wuyanshi, dan kuwa halin mahaifinta babu wanda ta rage bata kwasa ba na mugunta.

Juyowa tayi ta kalli mahaifin na ta tace “Na fad’a ma ka zan iya, ni ma namiji ce kuma zan ma ka anfanin da namiji ba zai maka ba.”

D’aga mata hannu yayi ya k’yafato ta alamar ta zo, maida kallon ta tayi ga dogarin ta aje masa wuk’ar sannan ta nufeshi, kafad’arta ya dafa yana kallon fuskarta yace” Kin tabbata zaki iya?”

Jinjina kai tayi tace” Ka fad’i abinda kake so, ni kuma zan maka.”

D’auke hannunshi yayi 脿 kafad’arta yace” Zafeera nake son gani a gabana, zaki iya kawo min ita?”

Mamaki ne ya bayyana a fuskarta tace” Mutanen gari suna cewa tun a ranar da aka saceta aka kasheta, ina ji 脿 jikina ta mutu.”

Girgiza kai yayi yace” Bata mutu ba, ina jin haka a jikina.”

Da wani mamakin tace” To amma tana ina? Na ga babu inda fadawanka basu zagaya ba a birni da k’auyukan k’asar nan, kuma yanzu haka an saka sanarwa ga duk wanda ya kawota zai tafi da arzik’in da har jikokinshi ba zasu k’arar da shi ba.”

Gyara tsayuwa tayi tace” Ka na ganin idan har tana raye wani zai kasa kawota ne ko dan kud’in nan.”

Wani kallo ya mata sai kuma yayi k’aramin tsaki yace” Zafreen wannan aikin na maza, ki je ki kwanta ki barni zan ci gaba da nemanta da kai na.”

Da sauri tace” A’a Baa zanyi, zan je nemanta ni da kai na, zan tafi kaji Baa.”

Wani kallo ya mata yace” Ta ina zaki fara?”

Turo k’aramin bakinta tayi tace” Baa na fad’a ma ka ina son aikin d’an sanda, zan je inda dayawa daga cikin abokanai na suke karb’ar horonsu, hakan zai taimaka min sosai wajen samota.”

Dafa kanta yayi yana lumshe ido alamun bacci a idonshi sosai sannan yace “Kin tabbatar?”

Waina idonta tayi tace ” Baa, ya kake neman nuna kasawata ne tun ban shiga aikin ba?”

D’an murmushin yak’e ya mata kawai ya juya zai shiga kusurwar da zata sadashi da d’akin baccinshi, saida yayi daf da shiga ta bishi da kallo tace “Amma ta ya zan ganeta bayan ko fuskarta ban gani ba da tana jaririya?”

Cak ya tsaya tare da juyawa ya kalleta, 脿 sanyaye yace “Ki samu babban malami Dhurani, zai fad’a miki komai a kan ta.”

Nunota yayi da yatsa alamar gargad’i yace “Amma ki tabbatar kinyi nasara, idan kuma kika min wasa da hankali…”

K’wafa yayi ya juya zai shige ta sake fad’in “Baa wai me yasa ka damu da ita haka sosai? Ni baku so na ne?”

Wani murmushi yayi a tausashe wanda ya sake bayyanar da kyawun fuskarshi sannan yace “Idan Zafeera bata shigo hannunmu ba, daga ni har ke mun kad’e, dan babu makawa sai ta ga bayanmu.”

Da wani mad’aukakin mamaki ta ci gaba da kallonshi tace “Kuma a haka kake son ganinta? Me zai hana ba zamu kasheta ba kafin ita ta kashemu?”

Da sauri sarki Musail da amintaccen dogarinshi suka zuba mata ido, kamar ba zai daina kallon ta ba sai kawai ya girgiza kai ya shige ciki, dogarin ma da sauri ya k’arasa gaban teburin ya kwashi k’aramar wayar hannun sarkin da kuma kwalbar barasarshi shi ma ya shiga d’akin kai tsaye.
Ita kam 脿 fusace ta fita tana jin lallai in ta had’u da ita kasheta ma zatayi kawai saidai ta kawo mishi gawarta, dan ba zata yarda yarinyar ta rabata da komai nata ba. Sanda cikinta ya bayyana haka gaba d’aya gari ake magana a kan ta, iyayeensu suke nuna mata soyayya fiye da ita, an haifeta ta b’ata amma a ce bata tsira ba? Sam ba zai yiwu ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button