Lu’u Lu’u 3

*3*

*29/12/2020*

*Larhjadin*

Da gudu ta fito daga motar ta tunkari dattijuwar dake tsaye da alama jiranta take, ihu ta saki tana fad’in “Mommaaaaa.”

Da fara’a matar ta tunkareta, amma sarautar Allah kawai sa茂 ta rusuna dake nuna girmamawa ga matashiyar, cak yarinyar ta tsaya ta had’e fuska cikin shagwab’a tace “Momma, ya kike abu haka kamar zaki rusuna min?”

Cikin dubara da wayancewa ta saki murmushi tana mai dafa kafad’arta tace “Haba dai *princezna* (gimbiya), abu ne naji na taka k’afata.”

Dariya budurwar tayi ta rumgume maman na ta tana fad’in “Momma na nayi kewarki.”

“Ni ma haka.” Ta fad’a tana lumshe ido wani dad’i na ratsata sakamakon had’a jikinta da tayi da sanyin idaniyar ta ta, sun jima haka kafin su raba jikinsu, kallonta dattijuwar ta dinga yi daga k’asa har sama.

Dogon wando ne matsatse bak’i sai farar riga mai k’ananan hannu, takalminta flat ne masu d’amara fara, k’aramar jaka ce a kafad’arta bak’a sai hular dake kanta ta sanyi, baya ga haka babu wani abu mai kama da kwalliya ko ado a tare da ita bayan wata siririyar sark’a dake wuyanta mai kalar d’anyan gwal sai wani zagaye kamar ziro.

Kyab’e fuska matar tayi tace “Gimbiya ta, ya naga kin k’ara ramewa? Dubeki fa.”

Dariya tayi data bayyanar da ‘yan hak’oranta na gaba kamar na b’era tace “Momma kin manta karatu na ne? Ina shekarata ta k’arshe ne, shiyasa na dage nake so na ga na fito a major ta foresti猫re.”

Girgiza kai matar tayi tace “K’iriniya irin ta ki sai nema gimbiya.”

K’yalk’yakewa tayi da dariya ta dafa kafad’arta tana fad’in “Gimbiya gibimya kullum, wai ni Momma ko dai mijinki sarki ne ban sani ba?”

Yanda tayi maganar cikin zolaya yasa matar yin dariya ita ma sannan tace “Maza ki samesu ku wuce, bana so ki k’ara ja min maganar da zan je bayar da hak’uri.”

Turo baki tayi tace “Momma dama kin gaji dani?”

Dogo kuma siririn hancinta ta kama ta ja sosai tare da juyawa da ita suka nufi motar dake tsaye k’ofar gida, cikin kukan sangarta take fad’in “Momma ba zaki barni na ga Papa ba? Please.”

Dungure mata kai tayi tace ” Ban hanaki yi min yaren da ba namu ba?”

Da yatsunta tayi alamar sakata a bakinta tare da cewa “Nayi shiru, ni na tafi, sai na dawo, ki gaida Papa.”

Duk tayi maganar ne tana hawa matakalar motar k’waya uku sannan ta juyo, da mamaki maman tace “Amma ba kin zo ne dan muyi magana ba?”

Dariya tayi tace “Momma zan fad’a miki.”

“Yaushe kuma?” Ta fad’a da jimami, dariya ta sake yi tace “Momma zan kiraki idan na koma.”

Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba, juyawa tayi zata k’arasa shiga sa茂 kuma ta juyo ta kalli maman na ta, ganin Maman na ta tayi ta sake irin sunkuyawar d’azu tace “Sauka lafiya princezna.”

Sam bata yi tunanin komai ba har motar ta su ta fara tafiya, kujerarta dake baya ta wuce ta zauna tare da cire hularta, hakan ya bayyanar da kanta wanda gashi ya fara tohowa, dan dukansu yan matan dake motar kowace kan ta k’wal kwabo ne sakamakon aikin da suke da burin yi.

Wata budurwa ce tace “Hankalinmu zai kwanta yanzu tunda an kawoki gidanku kin ga Momma.”

Wani kallo ta watsa mata lokaci d’aya ta d’auke kan ta, tab’e baki budurwar tayi ta d’auke kanta ita ma, tafiya suka yi mai nisan gaske kafin suka isa nesa da garin, wani babban k’ofa wacce aka rubuta sunan makarantar *Skola skoli novych smestnancov* (makarantar horar da sababbin ma’aikata) da yaren slovaque suka tsaya tare da yin oda, jim kad’an aka bud’e musu suka shiga.

Makaranta ce amma kamar gari guda, zaka tabbatar da girmanta ne kawai idan ka ga b’angarorin dake ciki, duk wani mai sha’awar karatun aikin saka kaki to nan yake ziyarta, kuma wanda ke karb’ar horon aikin soja ba zai san da zaman mai karantar horon police ba har sai in k’arshen sati ne da ake basu damar fitowa farfajiya har ma mai buk’ata ya fita waje.

Yanzu ma a b’angaren masu karantar ilimin *eaux et for锚ts* (gandun daji/ruwa da daji) motar ta aje su suka dinga shiga ciki, kowace na ta d’akin ta nufa mai d’auke da gado guda hud’u.

Kan gadonta ta zauna dan tasan yanzu wanka zasu fara dashi, ita kuma ba zata tsaya bin layi ko kuma zaman jira babu kaya a jikinta ba.

D’aya daga cikinsu ce ta shiga wanka sai biyun da suka cire kayansu suka d’aura towel, d’aya daga ciki ne ta kalleta tace ” *Ayam*, wai me yasa kullum Mommanki take rusuna miki kamar wata shugabarta? Ko al’adarku ce haka?”

D’aga kai tayi ta kalli *Deeyam* d’in tare da gyara zamanta, saidai ba tace komai ba face k’ura mata ido, a zuciyarta kuma tunani take ita kanta ta fara ankara da haka, sau da dama idan ta lura tayi magana sai Momma ta kawo mata uzirinta.

Ganin ba tayi magana ba kawai yasa Deeyam share zancen tare da kallon gashin Ayam d’in tace “Amma Ayam ba kya tsoron hukumar makaranta ta ganki kin ajiye gashin nan? Za fa su iya korarki dan kin taka musu doka kuma da gangan.”

Mik’ewa tayi tsaye tana sauke numfashi, hannu biyu tasa ta tattaro gashin kan na ta ta had’e wuri d’aya sannan ta kalleta tace “Kinga fa jibi ne shagalin k’arin haihuwata, nayi niyya 脿 wannan shekarar ba zan yi bikin k’arin shekarar nan da sulb’eb’en kai ba, dan haka in zaki iya ki je ki fad’a musu na tara gashi.”

Dariya Deeyam tayi tace “Amma dai zaki mana babban shagali a wannan shekarar ko?”

Kanne mata ido tayi tace “Dole mana, shekarar mu ta k’arshe ce fa.”

*Giobarh*

Kalar fatarshi kawai zata nuna maka lallai shi d’in daga gidan hutu yake, duk da yana da duhun fata amma kuma bak’inshi mai birgewa ne da d’aukar ido, tsiri-tsirin gashin kansa dake ta k’yalli yayi wara-wara alamar ana b’ata lokaci sosai wajen gyarashi.

Leb’enshi na k’asa ya lashe yana kallon abokin na shi da k’ananan idonshi masu zurfi, kyakyawan abokin na shi kam dariya ya saki tare da k’ok’arin gimtseta 脿 harshensu na Gallois yana fad’in “Haba abokina, ka bari a rage maka sumar nan mana, taya kake tunanin zuwa wannan wajen a haka kuma da sunan kai malami ne?”

A mugun hassale ya mik’e daga kujerar yana sake murtuke fuska, kallon mutumin dake tsaye gefensu yayi rik’e da jakar kayan aikinshi, a dak’ile yace masa” Fita a nan.”

Da sauri ya sunkuya ya juya zai fita, abokin ne yayi saurin fad’in” Kaga, jirani 脿 waje.”

Wata harara ya zabga masa ya nunashi da yatsa yace” *Haman* ka daina min haka bana so.”

Shima fuska a had’e yace” Na k’i na daina maka hakan *Umad*, me kake nufi ne wai?”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button