Zee Baby Book 1 Page 9

????????9*

….ina jinshi yana waya da su Daddy muna hanya naji sauki har muka isa gida ban sake shiga sabgarsa ba bakina gum ina zaune abaya honr yayi aka bude masa get ya shige gidan rumfar ajiye motocin ya shiga motocine reras har guda guma sha ukku kala kala na Dr Sardauna biyar ne Masu masifar tsada da kyau parking yai ya bude motar ya fita bai kalli ko inda nakeba ya kama hanyar tafiya Dole na bude na fito nabi bayansa har ciki ya rigani zuwa parlo bakowa sai Daddy da Mahabeer gun Mahabeer na nufa na rike hannusa zuciyata babu dadi Daddy yace” momy zo muji ya jikinki? ” Ammin da sauki Dr Sardauna yaba, Daddy magugunan ya rankwafo yamasa kiss “Daddy good night? ” night my son Allah ma Albarka” Ameen Daddy ya fada yana tafiya zee baby ta bishi da kallo yada yake komai cikin kuzari da jarumta tamkar Soja afagen daga yanzu ma taku yake cikin isa da kasaita har ya fice daga parlon kallon inda take baiba har Mahabeer din ya debema su iska ranta duk babu dadi jitakeyi kamar tabishi ta rumgumeshi idanuta ta lumshe tana sabke ajiyar zuciya Mahabeer yace ” zainab ya dai me kike tunani jikine nutsuwarta

ta tataro tasaki murmushi ” Ahkhuya naji sauki sosai Daddy yace” momy zo na nuna miki yada zakisha magani kusan Daddy ta matso ya nuna mata ya mike ” momy je ki kwanta dare yayi shagwabewa tayi” Ammin ni da Yaya Mahabeer zamuyi hira ni bana bacci dariya yayi ” Mahabeer aiki ya ganka insha Allahu za’ayi komai da wuri shiriya ta Allah ce zata shiryu adakinta nasan zaka tsaya ka bata kulawa murmushi Mahabeer yayi zuciyarsa fari tas Daddy ya nufi bangaransa gun Aunty Amarya kusan Mahabeer ta dawo ta dore kanta kafadarsa” Akhuya jikina duk ciwo yakemun wlh dukana yayi bakaga azabar da ya ganamun ba kalli fatar jikina duk tayi ja shida budurwasa sukamun shegen duka Dan naga suna rumgume rumgume nace musu haramune shine fah takai karshan maganar tana kuka ta rumgume Mahabeer gam ransa ya baci sosai tausayinta ya cika zuciyarsa bayanta ya buga yana lallashinta” my zeena kiyi shiru banaso kukanki bari zan Rama miki duk abinda yai miki kinji? ” kai na daga ina sabke ajiyar zuciya nayi shiru ina Kara shigewa jiknsa ” zee tashi kije ki hada ruwan zafi kiyi wanka ki gaza jikinki ki kwanta insha Allah bazai sake shiga harakarki ba ” Ahkhuya harda Allura yamun yasan kuma bana so nima insha Allah bazan sake shiga sabgarsa ba ” da yafi kin kusa zuwa matakin da bazai dokeki ba kuma kibar rashin jin magana

Kinji kanwata? ” ni dai wannan ban saniba ko na bari kamun Adu’a dariya yayi yashiga lallabata har ta yada ta tashi ya rakata har kofar bedroom d’insu shikuma ya juyo ya fice daga parlon ya nufi part d’insu bai shiga bedroom dinsa ba ya nufi d’akin Dr Sardauna har yayi wanka ya shirya cikin kaya bacci ya Dora jallabiya yana tsaye saman darduma yana sallah Mahabeer ya shigo da sallama ganin yana sallah yasa ya koma bangaransa yai wanka ya shirya cikin kayan bacci shima sallah yai raka biyu yana Addu’ar Allah ya shirya zee baby ya rabata da shaye shaye Allah yasa mata sonsa da kaunarsa kamar yada yake sonta duk da yagane tana sonsa Allah yasa ita matarsa ce kamar yada yaji Daddy na fada Yajima sosai kafin ya Mike ya fito ya nufi bangaran Sardauna kofar ya murda yaji ta bude ya bartane Dan yasa Mahabeer zai dawo yana kwance ya rufe jikinsa da blanket “Dr bacci kakeyi shiru yaji bakin gadon yazo ya zauna ” Faisal tashi akwai magana ya fadi yana dadabashi Dr Sardauna da bacci ya fara fizgarsa yaji Ana tashinsa can k’asa yace”haba don Allah wace irin magana ce baza abari sai gobeba ya Mike zaune ransa abace to inaji bismillah? ” dama cewa zanyi ka daina bugun zainaba bugo bayayi tace har ku biyu kuka hadu kuka jibgeta duk nawa take dama yarinyar afige so kake kamata illla ” OK jeka Allah Baku hakuri bazamu sakeba kuma insha Allah ni kome naga tanayi bazan sake shigaba ku karata can kunemi mai saitata tunda kai tarigada tagama maidaka Dan tace babu digon tsoranka aranta tunda ka daure mata gindi sai ka dauki damara jure tijarata ni kam ba ruwana da sabgarta bana zama guru daya da mace mai munmunar d’abi’a da rashin d’a’a Dan haka ku karata wlh bata gabana yanzu haka shawara barin gidan nakeyi dan nasan Daddy bazai barniba shiyasa zanyi na shirya aure nan kusa dama iyayan sweet baby sunmun magana Dan haka kasawa zuciyarka jarumta kazama Namiji ka tsaya tsayin daka tazama mace ta dawo hanya kwanciya yayi ya shige

Cikin blanket Mahabeer yaji zafin maganganun da Dr ya fadawa zee harma dashi ya dai basar ne” Faisal baka fahimceni bane Dole gyaruwar zaeenab saida sa hannuka aciki ni dukanne nace kabar mata shiru Sardauna ya masa ko ci kanki bai kuma cewaba har Mahabeer yagaji da surutunsa ya Mike Dan yasan ba sake kulashiba zaiyi ya fice yaje ya kwanta tsaki Dr Sardauna yayi ” munanan badai wannan yar Agullar bace ka daurewa gindi ba sai ta sakama ciwon zuciya watsi yayi da maganar Adu’ar bacci dauke bakinsa ya lumshe idanunsa dan mugun bacci yakeji sosai, bai jimaba ko ya daukeshi, zee ruwan gumi ta hada ta gasa jikinta sosai tayi wanka dama tayi sallolinta akwatinta ta ciro rigar bacci yar guntuwa ta saka juyowa tayi taga suna bacci ta fito da kwallaba guda ta bude tasha rabi ta boye rabin ta watsa kwayoyi bakinta ta tauna wuleliyar wayarta ta dauko ta kunna wakar larabci ta kunna tashiga tikar rawa da juyi ba kakautawa sai ihu takeyi taje ta tashi khalisat da take sharara bacci cike da mafarkin Sardauna firgigit ta farka ” taso muyi rawa ita tsoratama tayi ta kara shigewa bargo dariya zee ta bushe da ita ta koma gun Hafeeza dukanta tayi itama da karfi Dole ta Mike zaune tana murtsika idanu ” sister lfy ” taso na koya miki rawa idanu ta zaro ganin karfe ukku saura ” wlh ba daniba bargo ta koma khalisat najinsu haushin zee ya cikata ta datse mata mafarkin Dr Sardauna na nuna mata wani mahaukacin love Allah ya isa tajama zee itako ganin sun ki kulata yasa, ta rika kwarara ihu tun karfi tana tsalle da rawa Dole suka tashi zaune suna zaro idanuwa khalisat banda Allah ya isa babu abinda take jama zee duk nisan dake tsakanin dakin ghaisha da nasu saida taji su Daddy sunji shida Aunty amarya to lokacin suna cikin raya sunna ne ba halin fitowa ghaisha fitowa tayi ta nufo d’akin dan taji murya zee baby kofar ta tura ta shigo idanu ta zaro ” oh ni Nana khadija Momy meyazo garin rawa karfe kusan ukku na dare tuni abinda tasha ya fara aiki har ta fara tangadi ” ummi zo muyi rawa su sunkiya kinga wacca har zagina takeyi ta nuna khalisat idanu khalisat ta zaro kamota ghaisha tayi ” yi hakuri gobe zamuyi yanzu kwanta ki huta zo mutafi ma d’akina, kamota tayi suka fito su hafeeza suka rufe kofarsu can suka tafi bangaran ghaisha kana ganinta kasan tasha wani Abu amma ita ghaisha sam bata ganeba bedroom suka shiga saman gadonta ta kwantar da ita itama ta Haye gadon sai shirme take zantutuka iri iri ita gahaisha tunaninta jinnu ke damunta rumgumeta tayi tana buga bayanta ” ummina kinsan me My Sardauna ya mun yau wlh ummi Aduniya babu jarumin Namiji irin my Dr Sardauna ummi kome NASA daban Allah ya masa inason gwarzon Namiji jajirtacce tsayaye My Faisal kai na daban ne please zo ka karamun wollah inaso sosai ta rika daga hannuwa tana lumshe idanunta shiru ghaisha tayi dan Adu’a take tofa mata zan tutukan da ta fadima ba wani jinsu tayiba ” ummina ki kiramun My Dr nah shiru dai bata kulataba tasake kiranta ta” ummina” na’am momy yi shiru da bakinki kiyi bacci kinji? kai ta daga cikin ikon Allah shirun tayi ta kara shigewa jikin ghaisha bacci ya dauketa da Addu’a ta tofeta ta rumgumeta gam itama ta koma baccin atashi lfy

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button