Baiwata

BAIWATA 5

SADAUKARWA GA

  *AHALINA*

GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
β˜† [G. M. N. A] β˜† 📖🖊️

Bismillahir rahamanir rahim

              _5_

A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace “Me kika masa kuma yanzu?”

A raunane tace “Ba abun da na yi, irin wannan zanen ne fa nake yi.”

Ta fad’a tana nuna wuyan rigar Safiya, tab’e baki Safiya ta yi tace “Kin tabbata?”

Jinjina kai tayi tare da cewa “Allah ko.”

Jinjina kai tayi tace “Shikenan.” Juyawa tayi ita ma ta barta nan ta ci gaba da abinda take. Duk wannan shagali da abinci da aka shiga rabawa bai wani d’ad’a Saleema a k’asa ba, haka take abinda take ganin zai fisheta yayin da suma suke wanda ya fishesu, sai da dare ya yi sosai kafin su fara watsewa daga gidan.

Mamakin dalilin da yasa ya kirasu b’angarenshi take da kuma yanda ya taso Saleema a baccin ta, gashi ya musu tsaye k’erere har da wani rik’e d’amara a hannu alamar dai duka zai yi, sai dai ba ta san wa zai daka ba a cikinsu, ita ko Saleema ? Indai ita ce abun da bai tab’a faruwa ba ne, ko mari bai tab’a had’ashi da mace ba, bar shi dai ya rufeki da fad’a idan abu ya yi k’amari ya k’aurece miki, amma ban da duka.

Zuba masa ido ta yi tana jira ta ji me zai ce, sai da ya gama kumbura da kallonsu sannan ya kalli Safiya yace “Yaushe ki ka saka yarinyar nan koyon d’inki?”

Da mamaki ta kalleshi tace “D’inki kuma? Ni ban sakata koyon d’inki ba.”

Wani kallo ya jefeta da shi yace “Amma ai da saninki take zuwa ko?”

Kallon Saleema ta yi da ta fara tsuru tsuru da idonta tana kakkame jikinta a sakan biyu kuma ta kalleshi tace “Ban gane ba? Me yake faruwa ne wai?”

A d’an fusace yace “Ni ne ma zan fad’a miki abinda yake faruwa? Safiya yarinyar nan wata uku kenan ta na zuwa gidan matar can mai d’inki, kina so ki ce baki sani ba ne?”

Sake juyawa tayi ta kalli Saleema da tsantsar mamaki tace “Saleema, d’inki kike koyo?”

Mik’ewa ta yi tsaye ta ja baya tana girgiza kai cike da tsoro tace “Mam…a, da..ma.”

“Dama me ?” Ta fad’a a tsawace, zabura tayi ta fashe da kuka tace “Ki yi hak’uri Mama, ba zan sake muku k’arya ba.”

Dafe baki Safiya tayi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Saleema k’arya kika mana dama? Da kike cewa za ki tafi karatu, dama ba karatun kike zuwa ba?”

A mugun tsawace tace “Me yasa Saleema? Me yasa kika mana k’arya?”

Cikin kuka ta kalli Alhaji Yusuf dake kallon Safiya yanda ta hahhak’e ta saye bala’in ta kasa barinshi ya furta komai, da sauri ta girgiza kai tace “Kiyi hak’uri Mama, ba zan sake ba daga yau, na rantse miki da Allah.”

A hassale Safiya ta yi kanta tare da fizgar d’amarar (belt) dake hannunshi, kafin Saleema ta ankara ta damk’o hannunta rai b’ace zuciyarta na tafasa na k’arya da yanda k’aramar yarinya kamar Saleema ta yaudareta haka ta shiga labtawa jikinta bulala tana fad’in “Za ki k’ara daga yau? Ni za ki ma k’arya Saleema? Ni kika d’auka shashasha da ba ta san me take ba? Kin sake fita a gidan nan da sunan za ki je wajen d’inki ?”

Cikin kuka na bara-bara Saleema dake ta doka tsalle na azabar bulala take fad’in “A’a, A’a Mama, na tuba wallahi ba zan k’ara ba, na daina zuwa daga yau kar ki kasheni, wayyo ! Abba ka taimakeni.”

Duk da shi ma ranshi a b’ace yake na turbar da Saleemar ke neman d’auka, amma kuma haihuwa ta fi gaban wasa, sai ya ji na shi b’acin ran ya fece inda zuciyarshi ta fara suya na yanda ya ga Safiya na dukanta. A sukwane ya nufosu ai kafin ya kai mata agaji Saleema da dama neman ceto take ta yi ram da k’ugunshi ta na lab’ewa bayanshi.

D’aga bulalar da Safiya ta yi za ta sake zuba mata yasa shi rik’e hannunta ram tare da jawota gaba d’ayanta ta fad’a jikinshi, tsit ! D’akin ya d’auka har Saleema dake kuka ma wacce ta tsura musu ido da tunanin kar dai dukan Mamanta zai yi? Ido cikin ido suka kalli juna duk idonsu sun yi jajir na mabambamta b’acin rai, sake damk’e hannunta ya yi sosai hakan ya tilasta mata sakin d’amarar ta na d’an rintse ido na zafin da ta ji, cikin tattausan murya yace mata “Dukan ya isa haka, kamar kin samu wata jaka za ki dinga narkar min ‘ya a gabana, to kar ki k’ara.”

Zamewa ta yi daga jikinshi cike da kunya tace “Ka ga ka mik’o min yarinyar nan na farfasa mata jikinta, gobe ba za ta sake min k’arya ba.”

Harara ta dalla mata yace “Wallahi kika sake tab’a min yarinya ranki zai b’ace, ko ma me ta yi ai laifinki ne, shi ne za ki wani zak’alk’ale ki juye a kan ta dan kar na hukuntaki.”

Kawar da kanta tayi gefe tana d’an gunguni, d’an k’aramin bakin na ta ya bi da kallo tare da lashe leb’enshi na k’asa, dafa kafad’ar Saleema ya yi ya mata alamar ta fita, dan ya kula yau Safiyar namansa take da fitina, har shi ne ma take ma gunguni haka? Cikin shashek’ar kuka Saleema ta ari na kare ta bayan mahaifinta ta fice a d’akin da gudu.

Bin ta da kallo Safiya ta yi tace ta nunata da yatsa cikin d’aga murya tace “Ai zan sameki d’akin dan ubankkkk….”

Tsit! Ta yi dan sai da ta tasan ma fad’a ta tuna irin sub’ul da bakan da ta yi, wato a gaban shi ta zageta. K’in juyowa ta yi a hankali ta fara jan jikinta za ta fice a d’akin da sauri ya nufeta ya k’ara jawota jikinshi, tsura ma fuskarta ido yayi yace” Sofee dama tsaurin idonki ya kai haka? Hajiar ta wa? Kuma a gabana?”

Marairaicewa ta yi tace” Ka yi hak’uri dan Allah, wallahi sub’utar baki ce na manta.”

Jinjina kai yayi yace” Ni dai ko? Hajia ta kika zaga a gabana, ba komai.” Ya fad’a yana sakinta tare da fad’in” Je ki yi shirin bacci ki zo, na gode Allah da ya sa ranar kwananki ne kika zagar min uwata, hakn shi zai bani damar d’aukar fansata.”

Turo baki ta yi ta juya za ta fita dan zuwa d’akinta ta shirya ta zo kamar yanda ya ce. Da kallo ya bita kafin ya girgiza kai ya na murmushi ya zauna bakin gadon.

     *Washe gari*

A ladabce ta shigo d’akin tana fad’in “Asaalama alaikum.”

Safiya dake kwance da k’yar ta tashi zaune tana amsawa da “Wa’alaiki salam.”

Kusan gadon ta k’arasa ta tsuguna tace “Mama, kin ga safiya ta yi kuma ba inda muke zuwa, yanzu kinga na fad’a miki gaskiya, zan iya tafiya wajen aunty Hafsatu?”

Harara ta watso mata tace “Saleema jiya ya mukayi da ke? Ban ce kar na sake ji ko gani ba?”

A shagwab’e Saleema tace “Dan Allah Mama ki barni na tafi.”

A tsawace tace “Ke tashi, tashi ki bani wuri, kuma wallahi kika sake min maganar nan ranki zai b’ace.”

Mik’ewa tayi ta juya za ta fita ta bita da harara ta na fad’in “Ka ga min yarinya, ina zaman zamana ki hassalani kuma ba daman na zageki yanzun nan ubanki ya sake titsiyeni.”

Gyara kwanciyarta ta yi tunda dai yau ba aikinta ba ne tana fad’in “A bar ni na ji da abinda ke damuna mana.”

Alhaji Yusuf da ke jinme take fad’a yana daf da shigowa ne yace “A ma sake kuskuren zagar min uwata wallahi.”

Harara ya dalla mata yace “Yar rainin wayo.” Da mamaki ta kalleshi tace “Ni d’in?”

“Ke d’in mana, ko akwai magana ne?” Girgiza kai ta yi alamar a’a, Saleema da ba ta yi nisa ba ya k’wala ma kira ta dawo d’akin, tana zuwa ta tsaya tana kallonshi, cike da gargad’i da jan kunne ya zaro mata ido yace “Kina ji na? Daga yau sai yau kar na sake jin kin yi maganar zuwa wajen koyon d’inki, idan ba haka ba kuma wallahi da kaina zan hukuntaki.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button