NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 19-20
🅿️19&20
Atare suka kalli k’ofar”hindatu ce tashigo da sallama”fuskarta bbu walwala”Aysha ce ta amsa ta tana kallonta tace”.ina kwana?”
Lafiya qlau”itace wannan yaya zamuje da ita?”eh “yabata amsa yana duba wasu books”
yanzun yaya har kusan 6weeks katafi kabarnu har ingila?baby zan b’ata miki rai wlh”surutu zakizo kinamun ko kuwa gidan zaku tafi?”ke kuma kinyi wani zaune kina sauraren mutane”yafad’a yana gallawa Aysha harara”
batace komaiba ta sunkuyar da kanta k’asa”sosai hindatu taji tabata tsausayi”sbd tasan halin yayan nata sarai..
zomuje to kinji?”cewar hindatu tana kallon Aysha”zanje gun anty dan Allah”saina sameta aget”tafad’a tana kallon dr sadeeq”banza yamata saidai hindatu tace”.okay bbu damuwa”
Aysha na fita hindatu ta kallesa tace”.yaya yasunanta wai?”kitambayeta idan tadawo mana”yana fad’in hakan yad’auki abinda zai d’auka yace”.muje “meetings zanyi da duka ma’aikatana sannan natafi”tunda jirgin k’arfe 12:pm zan hau”
Dato ta amsa suka fito”yarufe office d’in ya wuce gunda za’a yi meeting d’in”ita kuma hindatu ta nufi get”
Aysha kuwa kuka tasakawa anty murja” bayan ta amshi kud’in ta na albashi 30k”akan ita bazata je gidansu dr sadeeq ba”
Anty na kallonta tace”.inaji ajikina alkhairi ne zuwanki gidansu Aysha”abu na farko dazan baki shawara akansa”ki rik’e gsky da amana”dakuma mutuncinki”insha Allah zakiyi alfahari da hakan wata rana”zancen skul a last year kike”karki damu idan yadawo da kaina zan masa mgn kicigaba da zuwa kisamu kihad’a takardunki”zuwa gidansu kuma ai ba kyauta zakiyi ba”biyanki zaiyi”
godiya Aysha tayiwa anty tana share hawayenta ta nufi get”hindatu na hangota tabud’e mata front sit tashiga”sannan taja motar”
yaya sadeeq ne yasaki kuka ko?”saurin girgiza kanta tayi tace”.ah ah bashi bane”to meyasa kikayi kuka?”mahaifina na tuna daya rasu”
Ayya kice d’aya muke dake”nima daddynmu yarasu”Allah yajikansa”Ameen”amma yasunanki?”Aysha sunana!
nice name”sunan amminmu kenan”saidai nakiraki da wani sunan”to shikenan bbu damuwa”dg haka motar tayi shiru”bbu me mgn har suka iso katafaren gidan ALH ALIYU”sosai Aysha tayi mamakin had’uwar gidan”ta tabbatar dr sadeeq sunada dukiya bata wasaba”
Tunda Aysha tasaka k’afarta cikin parlourn taji fad’uwar gaba”sannan girarta ta dama sai fat fat takeyi”
ammi na zaune kan kujera anjingina mata jikinta akan pillow”wata dattijuwar mata (mai aikinsu)tanata matsa mata k’afafuwanta”
amsa sallamar su matar tayi”Aysha nata kallon ammi da idanuwanta ke rufe”ta zauna k’asa kan carpet”
Iya sannu da aiki”yauwa hindatu kindawo?”Eh nadawo”bud’e idanuwanta ammi tayi”cikin sa’a suka had’a ido da Aysha”sosai gaban ammi yafad’i”
Ina kwana?cewar Aysha tana kallon ammin”ayya baby bata mgn ai”cewar hindatu”
Aysha ta gaida iya cike d mamakin meyasa ammin bata mgn?”takuma lura kamar saima yadda akayi da ita.
Ammi wannan itace wacce yaya d’azun yace”.zatazo”juya idanuwan ta ammi tayi alamar ta gane”
Tashi tsaye iya tayi tafice dg parlourn”
kan Aysha ak’asa tana wasa da yatsun hannunta”wayar hindatu tayi ringing”
murmushi tayi tana kallon fuskar wayar”tashi tsaye tayi tabar parlourn sbd mijinta ne yakirata”
Parlourn yayi saura dg ammi sai Aysha”sosai ammi ke lura da duk wani motsin Aysha”
Ta fahimci yarinya ce k’arama”kuma akwai damuwa atare da ita”fatanta ba sadeeq bane sanadin damuwar y’ar mutane.
tajima hindatu sannan ta dawo ta ja hannun Aysha suka wuce bed room d’in ammi”
Naji na yarda dake baby”cewar hindatu”ammina bata lafiya kusan wata 3 kenan”har yanzun ankasa gane meye ke damunta”har k’asar waje yaya yakaita,yakuma iya bakin k’ok’arin sa ganin yagano matsalar da kansa”amma shiru bbu sa’a”danginmu sunce ciwonta bana asibiti bane na gidane amma yaya yace”.bai yardaba”yanzun haka wani course ne zaije yyi wata d’aya ko 40days akqn matsalar ammi”
Ajiyar zuciya Aysha tasaki tace”. subahanallahi Allah yabata lafiya”
Ameen yah Allah”akwai aikin dazanyine anty hindatu ?”inaso k’arfe 2 natafi gida”
kidinga bari sai 3pm oh 4 pls”gidan bbu kowa saini da masu aiki”sai jefi jefi masu zuwa dubiya”
Dato Aysha ta amsa”hindatu ta tashi zata shirya kayan ammi a ward rope”Aysha ta tashi ta amsa ta jerosu tas”sannan ta gyara d’akin”agabanta hindatu ta shigo da ammi ta kwantar da ita kan bed”sannan tabata frash milk”sosai Aysha ke binta da kallon tausayi”afili tace”.gsky anty hindatu wannan ciwon bana asibiti bane”domin a islamiya mlm yakoyar damu wasu addu’o nacikin alk’ur’ani me girma”idan mutum na fama da irin wannan laluran yyi”kinsan shi alk’ur’ani warakane ga dukkan cuta.
wannan gsky ne baby”yayane sai yace ai bana….wayar hindatu tayi ringing”hakan yasa tayi shiru”tana d’aga wayar”hellow yaya”Eh munzo gatanan”Idonta biyu”okay”tafad’a tana karawa ammi wayar akunne”sosai dr sadeeq yayita mgn sannan hindatu ta janye wayar”ta k’ara akunnanta”hellow yaya kun shiga jirgin?”okay kayi addu’a”ai tun jiya rabonsa da gidan nan”tanada kirki bbu wata matsala atare da ita.aysha aranta tace”.gulmata yakeyi”kashe wayar hindatu tayi tana murmushi ta kalli Aysha tace”.cewa yaya yayi wai bakya rashin ji daiko?”nace masa ah ah”murmushin kawai Aysha tayi batace komaiba”ammi dai nata kallonsu”
Time d’in sallah nayi suka gabatar”sannan sukaci abinci”wanda Aysha tak’i sakin jikinta taci”
saida hindatu tamata da gske sannan tad’an ci”ammi kuwa Aysha da kanta tace”.zata bata abincin”wani irin tausayi sosai ammin ke bawa Aysha”kallon hindatu Aysha tayi tace”.akwai zam zam anan gidan?”eh munadashi”to ganyan magarya da ma’ul khal fa?”
babu gsky”idan bbu damuwa anty hindatu asiyosu yanzun a islamic chemist”inaso idan ammin ta amince ,kuma banyi shishshigiba zan had’a su nayi wasu addu’oi aciki”abata tasha ashafe mata jikinta”sannan insha Allah zanmata saukar alk’ur’ani me girma”ana rubuta mata ta shanye”insha Allah komeye zata samu lafiya darajar annabi muhammad (S A W)
Sosai ammi ke kallon Aysha tana jinjina baiwar yarinyar"ta kuma fahimci tanada ilimin addini sosai"
kallon ammi hindatu tayi”juya mata ido ammin tayi alamar ta yarda”sannan ta kalli wayar hintadu tayi sama da k’asa da Idonta…..alamar kar hindatu tasanarwa dr sadeeq koda ta wayane”
Ita kanta ammin tana zaton ciwonta bana asibiti bane”sbd kawai tashi tayi jikinta ahaka cikin wannan yanayin”
Tasan dai k’addara ce”amma bata sakaki da addu’a da azkhar”
Hindatu tace”.karki damu ta amince bara naje na saka masu bawa shukoki ruwa su siyo”dg haka tabar d’akin”
Ammi ta k’ware”saiga abincin wani yadawo harda ta hanci”k’wallah ta taso mata”gashi bata iya tarin.
Tsabar tausayinta kuka Aysha tasaka tana cewa”insha Allah zaki samu lafiya”tafad’a tana warwaran tissue zata goge mata hindatu ta shigo.
Da sauri ta nufosu tana cewa k’warewa tayine?”Eh wlh”tafad’a tana goge mata fuskar”hindatu na kallon ammin cike da kulawa da tausayi tace”.sannu ammina”Allah yasa kaffarane wannan ciwon naki”
hindatu tace”.Aysha dama haka kike da tausayi?”ai dole duk me imani ya tausaya mata”cewar Aysha tana goge hawayenta”
suna nan azaune aka kawo komai”tafasa ganyen magaryar akayi”sannan aka zuba ma’ul khal da zamzam aciki”
sannan Aysha ta dinga karanto addu'o I na tsari da wanda su ammin suka sani da wad'anda basu saniba"
Bayan ta idar aka bawa ammin tasha”aka shafe mata jikinta”sannan aka fidda wad’anda bbu zamzam aciki tace”.ayiwa ammin wanka dashi”
Atake ammin tadinga atishawa”rabon datayi ko tari harma su hindatu sun manta…sai kuma tayita zufa dg nan sai bacci yakwasheta.