BAIWATA 2

Bismillahir rahamanir rahim
_2_
Cikin sanyayyar murya Saleema ta kalli mahaifin na ta tace “Abba ka min alk’awarin siya min kyauta nima idan na yi k’ok’ari?”
Ba tare da sakin fuska ba yace “Idan kin yi k’ok’arin zan siya.”
Washe baki tayi da farin ciki tace “Na yi ma Abba.”
Wata harara Hadeeya ta jefa mata ta ja tsaki, a tausashe Saleema ta kalleta tayi k’asa da kanta, ba wanda ya sake magana a motar har suka isa makarantar, tsabar farin ciki da sakawa ransa ‘ya’yansa za su ciri tuta ko tun yaran basu gama shagali ba ya dawo d’aukarsu, hakan yasa saida ya d’an jirasu na wasu mintoci.
Hadeeya da Hameeda na gaba sun taho da gudu da fara’ a a fuskarsu, bud’e motar sukayi suka shiga suna rige-rigen mik’a mishi sakamakon kowace na fad’in “Abba ka ga ni nayi ta farko.”
Karb’a yayi tare da kyautukan da aka basu a makarantar yana dubawa, yanda bakinshi ya kasa rufuwa tsabar farin ciki yasa shi kasa furta komai, sai da Hamdeeya ta shigo fuskarta da alamar damuwa, jawota yayi yace “Ya ne autata ?”
Dariya Hadeeya ta k’yalk’yale da ita tace “Abba wai dan ba’a bata kyauta ba ita ma, na fad’a mata ta yi hak’uri idan ta kai ajin CI (pramary 1) ita ma za’a bata.”
K’ara jawota yayi jikinshi zai yi magana sai kuma ya tuna da babbar ‘yarsa wacce ta fara kiransa da sunan Abba kafin duk wad’annan, da sauri ya d’aga Hamdeeya daga jikinshi ya kalli Hadeeya yace “Hadee, ina mai sunan Hajia?”
Saida ta yatsina fuska kamar ta ga abun k’yama kafin tace “A aji na barota ba’a kira sunanta ba.”
Maida dubanshi yayi ga k’ofa yana fad’in “Me ya hana ku jir…”
Bai k’arasa fad’a ba suka hangi Saleema na tahowa ta rufe fuskarta da hijabi da alamar kuka take, wata mummunar fad’uwa gabanshi ya yi da tunanin ko lafiya? Abun da ya fara zuwa masa shine, kar dai sakarcin Saleema ya kai k’adamin da ta fara bayan gida a jikinta da har yaran nan ke biyarta suna mata ihu da tafi? D’an sauke madubin dake b’angaren shi yayi tare da bud’e motar da niyyar fita.
Sai dai wak’en da kunnuwansa suka tsinkayo ana ma babbar ‘yarsa yasa shi dakatawa tare da rintse ido, a rayuwar duniya bai tab’a tsammanin haka za ta faru ga ahalinshi ba, a matsayinshi na wanda k’ ok’arinshi ta sa gwamnati d’aukar nauyin karatunshi har ya keta hazo saboda iliminshi, yake alfahari da kasancewarsa d’an Alhaji Saddi Jiji wanda har turawa suka shaida iliminsa ya kuma karb’i lambobin girma ta fannin ilimin kimiya, a matsayinsa na wanda ya tashi a ahalin da babu wanda gwamnati ba ta wa rana ba, hakan yasa ko a gari aka fad’i ahalin Jiji ake musu inkiya da ahalin bariki ba dan komai ba sai dan sanin mutane a kan su cewa su d’in mutane ne da suka san darajar boko kuma suke bata hakk’inta yanda ya dace, daga shekara ashirinda ta wuce zuwa yanzu da wuya ka samu wanda ba ya aikin gwamnati, ba wai dan sun dogara da ita ba, sai dai a ganinsu ta hanyarta ne kad’ai iliminsu da alfaharinsu zai bayyana jama’a su sani. Amma yau gashi kunnuwanshi na jiyo mishi ana ma babbar ‘yarsa da saboda k’auna ya saka mata sunan mahaifiyarshi wacce ita kanta ta kasance likitar da a lokacin tana d’aya daga cikin mata biyu da suka fara tiyata a k’asar Niger, yau gashi ana ma takwararta d’an kira da wacce ta zo ta kusa da k’arshe a ajinsu.
Dakatawa ya yi daga shirin fitar ya d’aga madubin ya rik’e hab’a cike da jimami, dreban da ya ga yara na bin Saleema ne ya tsawatar musu ya bud’e mata gidan gaba ta shiga ta zauna tana ci gaba da shashek’ar kuka.
Suna isa gida a fusace ya fita a motar ya nufi d’akin Safiya ba tare da ya bi ta kan kowa ba, Saleema dake kuka da sauri ta zagaya bayan gidan ta lab’e kusa da tagar d’akin mahaifiyarta dan tunaninta dukanta zai yi, sai dai daga nan inda take ta juyo muryar mahaifin na ta sanda ya fad’a d’akin Safiya yana fad’in “Na sha fad’a miki ki dinga kula da karatun yarinyar nan amma ba kya ji, yanzu dubi abinda ta jawo mana, na je d’aukarsu amma yara na binta suna mata ihun jaka.”
A razane Safiya ta mik’e tana kallonshi a mamakance tace “Jaka kuma?”
A hassale yace “Jaka mana, idan ba jakar ba mecece? Wacce ke zuwa k’arshe a komai, yarinya ban da majina ba komai a kan ta.”
A raunane ta girgiza kanta ta sanyaya murya tace “To yanzu da kake fad’a min ya kake so na yi? Na bud’a k’wak’walwarta na tusa mata ilimi? Ko kuma na kasheta saboda bata ganewa?”
Dafe k’ugu yayi yace “Au ! Haka ma za ki ce?”
Jinjina kai yayi yace “Ya yi kyau.”
Juyawa yayi ya fice a d’akin, wata nauyayyar ajiyar zuciya Safiya ta sauke ta koma ta zauna tana dafe k’irjinta dake doka mata da mugun k’arfi.
*Washe gari*
Da gudu yaran suka tarbeshi inda ya dinga rumgumesu a jikinshi yana sumbatarsu, cike da kissa da karairaya Ardayi a ta k’arasa gareshi, ba tare da jin nauyin komai ba suka rumgume junansu tare da sumbatar kumatunsu.
Safiya dake jera abinci akan tebur bata kallesu ba dan dama abinda ta san zai faru ne, inda Saleema dake zaune k’asan carpet ta bisu da kallo a ranta take ayyana “Ko me yasa Abba bai da kunya?”
Manyan ledojin hannunshi ya ciro kwalayan dake ciki na wasu mahaukatan dogayen riguna da k’ananan wayoyi masu kyau ya ba wa Hameeda da Haddeya, inda Hamdeeya ya bata riga da wani k’aton abun wasa da sunan kyautarsu, da sauri Saleema ta mik’e abun ka ga yaro jikinta har b’ari yake ta ajiye k’aramin almakashin hannunta ta tunkareshi tace “Abba ni ina nawa? Baka ban ba fa.”
Wani kallon raini ya mata yace “Ni d’in zan kashe miki kud’i? Wace tsiyar kika tsinana? Wannan shirmen da kike?”
Ya fad’a yana nuna tsummokaran data tara gabanta kala kala na atamfa, leshi, shadda da saurensu ita a dole d’inki take, juyawa tayi ta kalli kayan sannan ta kalleshi tace “Abba d’inki ne fa nake yi.”
Kallon Safiya yayi da ke ci gaba da aikinta duk da tana jin me ke faruwa amma ta dake kamar ba ta ji ba. Yace “Kina ganin irin shirmen da take tara min a gida ? Madadin wannan me zai hana ta d’auko littafinta tayi karatu?”
Shiru ta masa dan tun jiya yake nemanta da rigima ido bud’e, dan haka ba ta kulashi ba, Ardayi dake d’an gyara matsatsan rigarta mai k’ananan hannaye ce ta d’an tab’e baki tace” To ita kanta karatun ya sha mata kai ne bare kuma ta koya ma ‘yarta?”
Sai lokacin kad’ai Safiya ta kalleta tace” Kinga, idan muna magana tsakaninmu ki daina saka min bakinki, bana so.”
Kallonshi tayi fuskarta a d’aure tace” Me ya sa ka hanata kyautar ita ma?”
K’ ank’ance ido yayi da mamakin tambayarta yana d’an gyara rigarshi ta shadda da aka ma k’aramin d’inki kasancewarshi d’an zamani bai cika son manyan kaya ba yace” Ban gane ba? Ke baki ji abinda na ce ba ce?”
D’auke kanta tayi daga gareshi sannan tace” Gaskiya ba ka adalci ko kad’an, ita ma fa haihuwarta kayi kamar sauran, me yasa za ka dinga fifitasu a kan ta?”
” Saboda sun fita. ” Ya fad’a cikin d’aga murya, ido cikin ido ta kalleshi kafin ta kalli Saleema tace” Zo nan.”
Da sauri Saleema ta k’arasa gareta tana matso k’walar da suka taru a idonta, kama hannunta tayi suka juya a wurin suka barsu nan, tab’e baki yayi irin ko a jikinshi kafin ya shiga wata sabgar.
Kwana uku kenan da faruwar wannan abu ya ga sauyi sosai daga Safiyar, dan ta daina walwala haka ma Saleema ba ya ganinta a falon tana wasarta, wanda dama ko can ita kad’ai takr wasar suma su Hadeeya suna ta su, k’arara duk mai ido ya ke gane da bambaci a tsakanin matan, wanda ba komai ya jawo haka ba sai fifikon da amarya ta samu fiye da uwar gida, ita ma kumata same shi ne dalilin dogon karatun da tayi wanda a yanzun take cin gajiyarshi ta hanyar aiki a banki.