ZAIN ABEED 3
Page 3
Zain dake shigowa cikin bedroom ɗin yace “Me ake a Club?” Da ɗan sauri Abeed ya juya yana shafa kwatacciyar sumar kansa, tare da ya tsuna fuska kamar ba zai magana ba, sai kuma yace “Yaushe nace Club?” Zain yace “Yanzu naji ka faɗa mana” ƙara haɗe fuska Abeed ya yi yace “Ba kaji daidai ba” Zain yace “Oh! Ƙilan, what about the show, kasan dan shi na rakoka daka matsamin ko? Kuma naga kamar baka da niyya” Zama Abeed ya yi akan kujerar dake gefen bed ɗin su, tare da harɗe ƙafarsa kamar yadda Zain ɗin ya yi shima yana faɗin “Gobe ne” Zain yace “Ok, Allah ya kaimu, Ni ma ina da Shari’a after we get back to Nijeriya” A hankali Abeed ya ce “Ok” Zain yana jan system yace “Baka tambayi wacce Shari’a bace” Abeed na ya tsuna fuska yace “Sorry mene?” Zain yace “Shari’a ce, akan matar da ake zargin ta kashe mijinta for no reason” shiru Abeed ya yi tamkar bai ji abinda Zain yace ba,kai Zain ya ɗaga tare da kallon Abeed gani ya yi ya harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa, ya jima yana kallonsa kamar mai masa kallon ƙarshe can yace “Kaji me nace ai” a gajarce Abeed yace “Ko sake ta” da mmki Zain yace “A saketa kamarya, kisa fa tayi?” Abeed ya ware idanunsa tass tare da kallon Biyunin nasa ya numfasa yace “To kace zargi?” Zain yace “Gaskiya ne, amma zargi zan ce tunda ba’a haɗa hujja ba” taɓe baki Abeed ya yi yace “Kana bani sahihin labari mara ƙarya” yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa Toilet, girgiza kai kawai Zain ya yi shima ya miƙe ya shiga toilet. Da daddare misalin 10 duk suna zaune a Parlo suna kallon wani show da Abeed ɗin ya yi kwanaki, dake waƙar tasa cikin harsuna biyu yake, hausa da English a wannan karan waƙar Hausa aka sako mai taken Babu Kamarka Asalin waƙar kuma Zain ya yiwa, gyara zama Zain ya yi yace “kasan duk cikin waƙar ka, Babu kamarka itace bakandamiyya ta” idanun Abeed akan iphone ɗinsa yana duba wani tweet da Arman Malik ya yi a Twitter, akan wata waƙarsa da ya yi show ɗinta, lumshe idanunsa yay alamar posting ɗin ya yi masa daɗi, a hankali ya shiga typing ya ruhutu The show was so amazing, i like it not too long Arman Malik yay masa reply da Buhut Buhut shukriya kashe datar ya yi, kana ya kalli Zain yana ɗan shafa kansa yace “kamar mgn kayi” Zain yace “Ohhu, this week zamu koma Masarautar Bilhira, be ready Mai martaba yace tare yake son ganin mu, na gaji da haɗin bakin nan naka, sai kasa inawa Mai martaba pretending cewa nine kai, idan kaso ƙin komawa 9ja” Murmushi Abeed ke son yi, sai kawai ya cije baki, yace “Oops, Ana show ɗin zamu tafi” Zain yace “when” A hankali Abeed yace “By tommorow morning” Zain ya harɗe ƙafarsa kamar yadda Abeed ya yi yace “owk, Ni ɗin zani?” Gently Abeed ya ɗaga kai, Murmushi Zain yay yace “Muyi ta rainawa jama’a hankali, sbd ba kowa yasan mu Twins bane, mene tittle n song ɗin?” Gyara zama Abeed ya yi yace “Waƙar biki ce, 5.m suka bada, gashi…” A hankali ya saita muryarsa, Zain kuma ya fara kiɗa da hannunsa, cikin golden voice ɗin ya fara baitin waƙar bikin..
Fifita ga amare..,
Sassaita ga angwaye..,
Najwa ta zama amarya…
Khalee ne angonta.
Tsayawa ya yi, yana jan numfashi, Zain kuma ya shiga yi masa tafi yana faɗin “Bravo, kasan idan zanyi aure waƙa 10 zakai min” kamar daga sama haka Abeed yaji kalma tayi masa dirar mikiya da mmki yace “Aure zakai?” Zain yace “ka samu matsala sai nace maka ba zan aure ba? Sai ka fara yi zanyi” taɓe baki Abeed ya yi kana yace “Ashe ba zakai ba” cikin rashin fahimta Zain yace “A saboda ni ba namiji bane?” Ka faɗa Abeed ya watsa yace “Go Ahead” dry Zain ya yi yace “Anya kana da lafiya? Kai ba ruwanka da batun aure mata basa gabanka, kuma kai ne ma ya dace ace kana sabga da ƴan mata saboda waƙar da kake” gently Abeed ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a cikin Aljihu shima Zain Miƙewa ya yi, tare dayin the same da abinda Abeed ya yi, cikin nutsuwa walking slowly Abeed yace “Ai nama fika lafiya”… “Kuma shine ba zakai aure ba, bayan age ɗinka ya kai, kuma babu abinda Mai martaba yake ƙauna sama da yaga duk munyi aure” Abeed yace “To! Kayi mn, tunda kana da ra’ayi” Cikin serious talking Zain yace “Kasan ai ba zan iya aure na barka ba” Abeed yace “then ka jira nan da 5mnt” cikin farin ciki Zain yace “Are You sure? Za muyi aure to suwa zamu aura, kasan matsala duk abinda zuciyata take so yanzu kai ma za kaji kana son sa, bana manta sanda mutunci da wata something like soyayya wlh ji nayi Nima ina sonta, duk inda identical twins suke mata dole mu samu so” kallon Zain kawai Abeed yake, wlh da gske ya lura Biyunin nasa aure ya keso, shi kuma wlh ya manta ana wani abu aure, infact bai ma san wacce kalar rayuwa ake idan an yi auren ba, ganin Zain na ƙoƙarin cewa wani abu, yasa da Sauri Abeed ya kama hannunsa suka nufi wajan gmy….Cikin dare bayan sunyi sallar Issha sun kwanta gaba ɗaya suna sanye da kayan bacci iri ɗaya, hatta yanayin kwanciyar su komai ɗaya, buɗe ido Abeed ya yi, ganin Zain na bacci yasa ya miƙe tsaye a hankali ya fice daga bedroom ɗin, bai tsaya sauya kaya ba, key car kawai ya ɗauka ya nufi compound na hotel ɗin, lokacin wajan 1:30 gashi ana bala’in sanyi, ya manta ko sweater bai ɗauka ba da mars, motar ya shiga ya yiwa key bai tsaya ko’ina ba sai cikin wani haɗaɗɗan club, wanda Tun daga waje kiɗa ke tashi, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara sama da glass ɗin motar wani mugun sanyi ne ke ratsa masa jiki, saboda duk fararan cinyoyinsa suna a waje ne, gaba ɗaya snow ta fara lullube motar, runtse idanunsa ya yi sosai yana mai datse laɓɓansa jin Numfashinsa ya fara wani bala’in sarƙewa, tuni daman gargasar jikinsa ta buɗe tsananin whlar da yaji yasa shi faɗin “Ya Rabbi, Ya Mujibudda’awati” ya faɗa yana ƙanƙame jikinsa waje guda, ganin zai iya rasa rai yasa cikin fitar hayyaci yaja motar da gudu ya koma hotel, yana zuwa ya hangi wani securitie, horn ya danna masa yazo da sauri, magana ya yi masa kaɗan, sai gashi ya dawo da wani ƙaton bargo na sanyi, amsa ya yi ya saka jikinsa, jiri na kwasar sa ya nufi room ɗin su.. Yana zuwa ya samu Zain tsaye hannunsa goye a bayansa sai zirga-zirga yake tsakanin parlo da bedroom, da sauri yace “Daga ina kake?” Kai tsaye Abeed yace “Club” he was shock da jin abinda Abeed ya faɗa, mene zai kai Biyunin nasa club ko dai ƙarya yake, amma Abeed baya ƙarya tunda yace haka Tabbas daga club ɗin yake, da wani irin kallo ya fara binsa ko dai ya fara bin mata ne? Cikin ransa yace “No!” Hannunsa kawai ya kama suka shiga ciki, har bakin bed ya kawo sa tare da kwantar dashi ya rufe sa da duvet, heater ya kunna kana ya ɗauko masa Inhaler nasa, a daran Zain bai bacci ba kamar yadda Abeed ya kwana da ciwo, gaba ɗaya basu samu bacci ba sai da sukai sallar Subhi, kana suka kwanta kan Abeed a hannun Zain a haka sukai baccin….
Gajiya sukai da tafiya, Sairah ta kalli Sara tace “Twin na gaji, yunwa ishi, I’m felling hungry” Juya Sara tayi can ta hangi wata ƙorama tace “Follow me” bayan Sara Sairah tabi, har zuwa wajan ƙoramar gaba ɗaya suka tsuguna, Sara tace “Open your hands twin” buɗe hannunta Sairah tayi daidai bakinta, ita kuma Sara ta dinga ɗebo ruwan tana zuba mata a hannu tana sha, bayan duk sun sha ruwan, Sara ta kalli Sairah tace “stay here, I’ll be back” Girgiza kai Sairah tayi tace “Zan biki” Girgiza kai itama Sara tayi tace “Ba kince yunwa kina ji ba? To Abinci zai nemo maki ok, bana son ki Wahala” idanun Sairah ne ya cika da hawaye tace “to baki da lafiya fa” zaro manyan idanunta waje Sara tayi tace “Kai twin lafiya lou nake, yanzu zan dawo” kamar yarinya haka Sairah ta miƙa wa Sara hannu tace “promise?” Wani cute smile Sara tayi tun bayan zuwan su wajan tace “Promise, ohya come closer” juna suka rungome Sairah tace “I luv u twin” Sara tace “luv u too twin” Zame jikinta Sara tayi tare da ɗauko zoben hannunta ta bawa Sairah tace “Ajjiya, bye sai na dawo zan kawo maki abinci da yawa” Bye sukaiwa junansu, Sara ta tafi ita kuma Sairah ta zauna bakin ruwan tana jiran dawowarta. Ta shafe awanni tana tafiya cikin tsakiyar jejin amma babu wani abu da ya yi kama da abinci, Banda ganye, yunwar daya isheta yasa, ta fara ciyar ganye tana ci, sai ajjiyar zuciya take saukewa, Sara sam bata yadda tayi kuka ba a rayuwarta, No matter what happen to her she will never cry, tace kuka alamar raƙwanta ce, babu wanda take tunanin zai iya sata kuka, tana cikin cin gayen taji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, runtse idanunta tayi tana kiran sunansa Allah, a hankali kuma jini ya fara biyowa ta hancinta, karo na farko data fara karaya da abinda yake damunta, tunanin komawa wajan Sairah tayi kada ta mutum a nan, ta juya ke nan zata tafi taji daga bayanta ance “Kaiiii” da ɗan sauri ta juya wasu maza ne manya majiya ƙarfi, kayan jikinsu duk iri guda kamar arnan daji kamar maguzawa, gaba ɗayansu suna kan doki, hannunsu riƙe da igiya, shiru tayi kanta a kasa, ɗaya daga cikin mutanen yace “Wannan kamar tayi ko?” Ya faɗa cikin wata iriyar gurɓatacciyar Hausa, Wani yace “Eh tayi, kai ko ba tayi ba haka zamu kai ta, dan idan muka koma babu wata mace to kisan gilla MABUS zai mana” dry duk sukai wani yace “Mutuwa ba yanzu ba kowa, Sai abar Bauta ta sahale mana” Jin haka yasa Sara tace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, Am sorry twin, na kasa kula dake kamar yadda nai maki Al’ƙawari, ina tunanin lokacin mutuwa ta ya yi, ki yafe min zaki rayu a jeji babu uwa babu uba, babu ni” ta faɗa acikin zuciyarta tana jan wani irin ajjiyar zuciya, necklace ɗinta ta cire ta wurgar a wajan, kana ta zame ribbon ɗinta shima ta yar a wajan, ƙafa ta ɗaga da niyyar guduwa taji an naɗeta da igiya tare da yin sama da ita….