BAIWATA 8
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
SADAUKARWA GA
*AHALINA*
GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
☆ [G. M. N. A] ☆ 📖🖊️
Bismillahir rahamanir rahim
_8_
Kiran da aka mana cewa mu zo mu ci abinci ya sa Saleema fitowa daga ɗakin bayan idar da sallah isha’i, rufe ƙofar ɗakin ta yi ta fara takawa a hankali, cikin nutsuwa ta ke saukowa daga matakalar benen har ta sauko ƙasa, za ta nufi teburin cin abincin da ta hangi mutanen gidan ta dan tsaya saboda jerawa da sukayi da Mu’az shi ma zai nufi teburin.
Ɗan satar kallonshi ta yi ta gefen ido ta taɓe baki, Mu’az dake kallonta ya na so ya san wacece wannan? Cikin shan-ƙamshi da tsareta da ido yace “Sannu.”
Kallonshi ta yi sosai, haɗaɗɗen saurayi mai ilimin boko da wayewa irin ta zamani, sa kawai ta ɗan ɗaga masa kai alamar “Kai ma sannu.”
Da mamakin yanda ta amsa mi shi ya bita da kallo sanda take ƙarasawa wajen teburin, tana isa ta dan dakata tare da faɗin”Ina wuninku.”
Alhaji Auwal ne ya fara amsawa da fara’a yace” Lafiya lau ma puce, kin sauko?”
Cike da kunyar sunan da ya kirata da shi ta ɗan jinjina kai sannan ta ja kujerar da Hajia babba ta nuna mata ta zauna. Dara-daran idonta ta ɗaga ta kalli Mu’az da shi ma ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna ya na binta da ido kamar maye, ɗauke kai ta yi tana ɗan gunguni ciki-ciki.
Ummeeta ta kalla da suke maƙale da juna ita da Hadeeya tace “Sannu Ummee.”
Yatsina fuska Ummee ta yi tace “Sannu.”
“Abba ita ma wannan ƴar tonton ce?”
A sanyaye sosai ta maida dubanga zuwa ga wanda ya yi maganar, wato ɗaya sheɗanin ne ba? Mu’awwaz ko? Haɗa ido su ka yi hakan yasa ta yi saurin ɗauke kanta, Alhaji Auwal da ke murmushi ne yace “Wai ba ka ganeta ba abokina? Mai sunan Hajia ce fa.”
Waro ido sosai Mu’awwaz ya yi yana kallon Saleema yace “Abba Saleema fa? Ita ce ta koma haka?”
Wani mugun kallo ta aika masa cike da takaicin rashin sako hijab ɗinta da ba ta yi ba, hakan kuma ya faru ne da tunanin doguwar riga ce jikinta kuma ban da samari ake cin abincin, murguɗa masa baki tayi duba da shi kan shi fa shekara biyu zuwa uku ne ya bata, amma abu ga ɗan hutu ya zama wani karbcece masha Allah, ka rantse ba su yi wasar ƙasa tare ba.
Hajia babba ma dake murmushi cike da dattako tace “Girman mace ai ba wuya, kai ma da ke namiji ba gashi ka haɗemu wajen tsayi ba.”
Mu’az da ke ta kallonta yana taunar leɓe ne yace “Gaskiya kam, gashi ta girma…sosai.”
Da sauri Saleema ta kalleshi, amma sai ya dinga aiko mata da wani kallo irin na iskanci a ganinta yana kashe mata ido ɗaya, ɗan cire takalminshi ya yi daga ƙafa ya zuro ƙafar ta ƙasan teburin ya zunguri ƙafarta, da sauri ta jaye ƙafar ta na waro ido ta kalleshi sosai, sake kashe mata ido ya yi hakan ya hassalata ta wurga masa harara.
Hajia ƙarama da ta miƙo masa abinci amma bai kula ba ne tace “Mu’az.”
Da sauri ya kalleta sai kuma ya girgiza kai yace “Um um! Zan sha kayan marmarin nan kawai, kun san sun fi…”
Sai kuma ya kalli Saleema yana ɗaukar tuffa dake kusanshi sannan yace “Sun fi daɗi da ƙara lafiya ko ya ki ka ce mai sunan tsofaffi?”
Buɗe ɗan bakinta tayi kamar za ta yi magana, sai kuma ta yi shiru dan bata san me yake nufi da abinda ya faɗa ba. Hadeeya da kujerarta ke kusa da ta shi a ɓangaren ce ta kalleshi tace “Yaya ka ci abinci fa, wannan ba zai riƙeka ba.”
Kallonta yayi da fara’a a fuskarshi yace “Hadeeya ko?” Jinjina kai tayi alamar e tare da sakin murmushi, hannu ya miƙa mata alamar su gaisa yana faɗin “Kina lafiya?”
Ba tare da tunanin komai ba ta miƙa masa hannun suka gaisa, hannayen na su Saleema ta kalla sai kuma ta kalli Hadeeya, girgiza kai ta yi ta sunkuyar da kanta ta fara wasa da cokalin hannunta, babban abun takaici shine yanda ya yi haka a gaban iyayenshi amma ba wanda ya nuna ya damu.
Muryar Alhaji Auwal ce ta saka ta ɗaga kanta sanda yake faɗin “Mu’awwaz idan kun kamala ka tafi da su alimentation idan akwai abunda suke da buƙata sai ku siyo.”
Jinjina kai Mu’awwaz yayi yace “To Abba.”
“Ka barshi ma ni zan kaisu.” Cewar Mu’az yana ci gaba da kallon Saleema, bai san me yake ji ba a kanta ba, sai dai ya ji yana sha’awar komai na jikinta, duk da ba kyawun fuska ne da ita ba na nunawa a jarida, ba kuma jar fata gareta ba kamar ƴan uwanta, amma dai komai na ta ya birgeshi musamman da ya fahimci ya fi sauran ƴan uwan na ta nutsuwa da kamun kai.
Wani kallo Mu’awwaz ya masa dake nuni da bai ji daɗin abinda Yayan na shi ya masa ba, wannan ai katse hanzari ne, ya na tunanin ya fita da ƴan mata su shanawarsu, musamman ma Hameeda da ta fi ɗaukar hankalinshi, sai kawai ya ce shi zai kaisu? Wallahi ba dan ya na tsoron ya yi magana ya kabta masa mari ba, da ya masa magana sai dai a yi duk wacce za’a yi. Da harara ya bi Mu’az ɗin da ya miƙe yana faɗin “Ummee ina jiranku a waje.”
Saida ya ƙara matsowa kusan Saleema ya ɗora hannayenshi a kan teburin ya sunkuyo sosai kamar zai sumbaceta, jaye fuskarta tayi daga kallonshi tana yatsina fuska cike da kunya, duka mutanen kallonsu suke, su Hadeeya mamakin yanda ya ke ma Saleemar su ke, ko bai gane ita ɗin ba mai aji ba ce? Yayin da amarya ta ke taɓe baki da tunanin “Ɗan iska kawai, a gaban mutane ma sai ya nuna halin iskancin da tambaɗewa.”
Hajia babba kuma murmushi take a ran ta tana ayyana “In har Saleema za ta zama alkairi gareka zan fi kowa farin ciki.” Dan kuwa ta fi kowa sanin ɗanta, ba ta taɓa ganin ya wa mace haka ba, shi Alhaji Auwal kuma murmushi kawai ya ke saki a fuskarshi, ko ba komai ƴaƴan Alhaji Yusuf za su ji daɗin zama gidan.
Cikin sanyin murya Mu’az yace mata” Ina jiranki, ki fito da wuri.”
Juyawa ya yi kawai ya fice a falon, kasa ɗaga kanta tayi bare ta kalli mutanen wurin, sai da ta ji sun maida hankulansu kan abincin sannan ta ɗan ɗago ta kalli Alhaji Auwal, cikin taushin murya da ladabi tace” Am! Abba.”
Cike da kulawa ya kalleta yace” Na’am ƴata.”
A sanyaye tace” Ina ganin su tafi kawai, ni zan zauna a gida.”
Da mamaki a fuskarshi yace” Me yasa? Ke ba kya buƙatar komai ne?”
Ɗaga kai tayi alamar e, wata harara Hadeeya ta jefo mata cike da takaicin me yasa wau ita take da kidahumanci ne? Kuɗi ne fa za’a kashe musu, ɗauke kai ta yi cike da baƙin ciki, Saleema kuma da ta kula da kallon ba ta biyata ba bare ta samu damar faɗa mata wata maganar marar daɗi.
Hameeda a da saida ta harari Saleema cike da rashin kunya tace “Abba ka ƙyaleta ita dama haka take, mu za mu je mu siyo abinda mu ke so.”
Kallon Hameeda ya yi da mamakin yanda ta ke magana akan Yayarta haka, shi fa duk bokonshi da iskancinshi ya na so ya ga ƙarami na girmama babba, girman da ubansu ya ke bashi ne matsayinshi na wanda ke sama da shi a komai ya sa suke kamar abokai, ko Mu’awwaz da ke namiji bai yarda ya raina Mu’az ba tunda ya na gaba da shi, bare ita wannan da ba ita ke bi ma Saleema ba. Ɗauke kai kawai ya yi da tunanin idan ya ƙara ganin haka zai tsawatar mata, dan sam ba ya lamuntar irin haka.
Shigowar wata matashiyar yarinya da ba za ta wyce tsarar Hameeda ba yasa Saleema kallon ƙofar, Alhaji Auwal ma cike da kulawa ya kalleta yace “Kin kai musu abincinsu?”
A ladabce yarinyar da sai yanzu Saleema ta fahimci ƴar aiki ce tace “E Alhaji na kai musu, sun tafi masallaci ma sai da na jirasu.”