ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA QAQAI COMPLETE HAUSA NOVEL

DAYA 1
Wata ranar lahadi aka tashi da gagarumin hadari wanda yakan firgita birrai. Kodayake a safiyar ranar ba’a tashi da alamun hadarin ba. Sararin samaniyar tarwai yake babu alamar gajimare ko kankani wannan shi ya baiwa rana lasisin ci gaba da dumama rufin gidaje da kayuwan bani adama tun daga karfe goma na safiyar har zuwa karfe daya na ranar. Abin bai zowa mutane a bazata ba musamman ma wadanda suka sha miya da yawa domin sun dade da yin amannar cewa duk sa’ar da zafi ya tsananta alokacin damuna to hadari ne ke son haduwa.
Haka kuwa akayi babu zato ba tsammani sai hadarin ya fara haduwa sahu sahu sannu ahankali har ya dakushe hasken ranar ba’a dade ba sai iska gamida feshin tsattsafar ruwa nan da nan jama’a suka fara tserere akan tituna domin su sami gurin fakewa acikinsu harda Ni wanda rabona da ofishina tun karfe tara na safe da wani mutum yazo karbar bashinsa na gudu.
.
Wannan bashine karo na farko ba dana fara tserewa masu bina bashi kusan watanni tara kenan da harkar fim ta juya min baya tun fitowar fim dina na DAREN MUTUWA shikenan sai mutane suka dau karan tsana suka dora min.
Iskar hadarin ta fara tsananta dan haka sai nayi sallama da mai shagon dinkin da nake boye aciki tun safe nace dashi.
ISYAKU zan koma ofishina. Isyaku tela ya dubeni cikin damuwa daman yasan irin matsanancin halin danake ciki
Gara ka tafi gida Hilal domin komawarka ofis ayanzu ganganci ne… Na dubeshi gamida murmushin yake
kada ka damu isyaku leka waje ka gani hadari ne bakikirin ga iska.. Nasan dai mutum yanzu in ba maye bane dole ne ai yabar ofishin….. Kuma bugu da karawa ma dole ne na koma ofishin domin na sallami sakatariyata LAURIYYA dan nasan ko kudin mota bata dashi…… Abincin rana ma bansan yadda zatayi ba.. Isyaku ya dubeni cikin mamaki.
Kana nufin haryanzu Lauriyya tana tare dakai? Na gyada masa kai kwarai kuwa ai tattaraba ce uwar alkawari ita kadai ta rage a yarana duk sun barni sai ita kadai… Isyaku ya dan yi murmushi yana dubana.
Itama akwai dalili.. Na dube shi cikin mamaki
dalili… Kamar yaya ban fahimce ka ba isyaku yayi atishawa sannan yace
Haba Hilal har sau nawa kake so in maimaita ma cewa Lauriyya sonka take.
Nayi saurin girgiza kai
A’a bari bari isyaku kada kayi min mummunan fahimta na yarda ni dan fim ne amma zakayi mamaki idan nace dakai tunda nake ban taba soyayya ba da wata yar fim.
.
Kakkarfar iskar hadarin dake ta hankoron dauke rufin dakunan masu rangwamen gata ta bugo kofar shagon telan da karfin gaske
Isyaku yasa kafa ya tokareta.
Baka fahimce ni ba Hilal ko kuma ince kasan gaskiya ka ke takewa ai ko makaho ya laluba yasan lauriyya tana mutuwar sonka.
.


.
Lokacin dana baro shagon telolin saina tsallaka titi na nufi ofishina cikin sauri da kyar nake ganin gabana saboda kakkafar iskar ma’abociyar kara dake ta bulbule min idanu.
Kura ta turnuke ko ina haka nan garin yayi jajur duhu ya lullube ko ina kai kace karfe shida da rabi na yamma tayi duk kuwa da cewa karfe daya ne na rana.
Cikin sauri na nufi ofishin inata waige waige domin haryanzu jikina na bani cewa akwai sauran masu bina bashi cikin ofishin suna jirana.
Tun kafin na karasa ofishin na fara hange hange da rabe rabe sannu ahankali har na isa kofar ofishin wacce ke rufe tana duban bakin titi.
Nayi tsaye a kofar ofishin kusan minti guda nayi kasake kamar barawo ina saurare ko zan ji surutai ko hayaniya shiru banji komai ba na dan dada matsawa kadan na kara kunnuwana ajikin katuwar kofar nayi ajiyar zuciya sannan sainayi shahada na daga hannuna zan tura kofar kenan sai kawai naga an bude daga ciki.
Sannu da zuwa hilal yi maka ka shigo daga ciki yanzu yanzun nan EMEKA yatafi tun sha daya yaketa jiranka nace dashi katafi kaduna… Amma yaki yadda
Kirjina na dakan uku uku cikin sauri na shige ofishin.
Lauriyya ta mayar da kofar ofishin cikin gaggawa ta rufe sannan saita jingina bayanta ajikin kofar ta kura min idanu bata ko kiftawa.
Na nufi cikin ofishin ahankali hannayena cikin aljihunan wandona zuciyata na kuna nayi kokarin nazarin ofishin amma saboda duhun hadarin bana iya ganin komai cikin ofishin.
Lauriyya ta fahimci haka cikin sauri ta nufi makunnar lantarki ta kunna nan da nan dakin ya gauraye da haske.
Lauriyya tayi tsaye jikin makunnar lantarkin tana kallona ina kallonta.
Akwai alamar tausayi karara a fuskarta banda wannan kuma naso na hangi kwalla acikin kwayar idanunta. Cikin sauri na dauke kaina gefe guda sannan nafara nazarin ofishin….. Da a da dan wani lokaci can daya shude babu wani ofishin darakta na fim daya kai koda rabinsa a tsaruwa amma koda na tsaya ayanzu ina nazarin ofishin sainaji kamar na fashe masa da kuka lallai ruwa ya daki babban zakara.
Saidai hakuri Hilal haka duniya take rawar yan mata lauriyya ce ke magana abayana cikin wata rarraunar murya. Naji abinda ta fada to saidai kuma ban iya juyowa na kalleta ba ballantana ma na tanka mata.. Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan shudadden zamani sa’ar da………..
.
[20:26, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAƘAƘAI-02
.
(m) Nazir Adam Salih
.
Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan shudaddan zamani…. Sa’ar danake tauraron jarumai na wasan fina finan hausa.
Na rufe fuskata da tafukan hannuna sannan nafara tunanin sa’ar dana shigo harkar fim da kafar dama cikin watanni ukun farko da shigata harkar na fito cikin fina finai sama da shirin wadanda duk nine jarumi acikinsu sannu ahankali sai sunana yayi tambari duk inda ka zagaya babu sunan wanda ake fade sai HILAL.
Duk inda na zagaya yara da manya basa barina na huta sun yita bina kenan abaya kungiya-kungiya kamar uban garke idan naje sayayya kasuwa ba’a karbar kudina haka nan da zarar an kyalla ido na ganni saikaga anata rububin ganina kowa na gayyata dana zo nayi siyayya ta a rumfarsa duk kuwa da cewa ba kudina zasu karba ba.
Na mallaki abubuwa da dama a shekarata ta farko da shiga harkar fim wanda adacan wani lokaci ban taba mafarkin mallakarsa ba akwana kusa motoci uku na hawa kayan sawa na kwalisa sama da kala dari uku da goma sha takwas agogunan sarka ashirin na fata goma takalma sittin safa kuwa da singileti duk wacce nasa sau uku bana kara amfani da ita sai wata sabuwar.
Sannu ahankali samari suka fara kwaikwayon yadda nake direshin duk abinda nayi koda sakarci ne sai ya burgesu saikaga sun zamo masu kwaikwayona.
.
Ashekarar ne na bude katon ofishina wanda aka kawata shi da kyale kyale gami da manya manyan kujeru masu numfashi da taushi kamar ada da sau da yawa idan muka sauki baki indai har zasu shafe mintuna goma suna zaune sai an sami wanda ya bingire da barci saboda dadi.
Duniya ta dawo min sabuwa ina da yara dake aiki akarkashina sama da mutum ashirin suna kuma jin maganata fiye data iyayen da suka haifesu wasu suna bina sau da kafa ne wai don kawai suna so na sa su kokuma nayi musu hanya su shiga shirin fim yayinda wasu kuma suke yi min biyayya don kawai kaunata da sukeyi. Nazama kamar sarki acikin fadawa duk abinda nake so shi za’ayi batareda bata lokaci ba. Da ace yarana awannan lokacin suna da iko da fitsari da numfashi ma su zasuyi min.
Muna nan ahaka har shekaru biyu suka shude
Kwatsam ran nan sai duniyar data dagani sama ina shanawa tafara yin kasa kasa dani sannu ahankali ta damfara ni da kasa.
Abin yafara ne a yammacin wata ranar lahadi sa’ar danake karbar kudaden sabon fim dina RAGAS daya fito.
Shagon farko danaje sai akace dani wai fim din baya tafiya nayi mamaki domin tunda kamfanina yake fim ba’a taba samun wanda bai shiga ba.
Me ya faru da fim din? Na tambayai wani dillalin kasa kasan fim din.
Eh to kasan dai mutane yadda suke ba’a iya musu inajin dai gajiya sukayi dakai…. Kuma sunata korafi akan cewa wa fina finanka na kwanan babu labari mai kyau.
Tun daga ranar ne al’amura suka dagule min abin kamar sa hannu komai na taba sai ya lalace gashi dai nagama kashewa fim din Ragas kudi… Na ranto kudin jama’a duk na lafta saboda a tunanina zaiyi bala’in karbuwa saigashi cikin ikon Ubangiji saidata kawo ko kashi daya bisa goma na kudin fim din basu komo ba.
Rayuwata tsananta kaina ya dauki zafi rikici goma da ashirin ga tarin bashi fal akaina gashi kuma ya furodusoshin ma da suke daukana na fito musu a matsayin jarumi duk sun gujeni ba’a dade ba duk yarana suka watse suka barni daga ni sai yar amana LAURIYYA.
.
Koda na daga fuskata sa’ar danake tunanin na dubeta saina tuno da kalamanta saa’ar da gari yayi mana zafi bazan taba mantawa da ranar ba. Ranar wata laraba da yamma bayan sama da mutane goma sun zo tambayata bashin su.
Hilal.. Ina da shawara in zaka yarda. Lauriyya tace dani na dago kai na dubeta.
Fadi shawararki lauriyya…indai mai amsuwace ai na dauka.. Tunda dai ko banza dai ke kadai kika rafe atare dani.. Wallahi lauriyya ayanzu kin wuce sakatariya agurina saidai ko in Yar Uwa.
Lauriyya ta dan matso daf dani duk da yake duk ranmu abace yake to amma na lura da alamun jin dadin abinda nace karara a fuskarta na sani ba tun lokacin ba har zuwa yanzu Lauriyya sona takeyi to amma ta rasa yadda zata fito ta fada min.
Hilal… Ni ina ganin a shawara da ace kullum mutane suyita binka suna tambayarka bashi… Suna muzanta ka kamar barawo gara in kana ganin babu damuwa ka daga dan kadarorin daka mallaka kasa su akasuwa in yaso saika biya mutane bashin su… Ko banza dai ina ganin ai tsira da mutunci yafi tsira da kudi. Hakan data fada saina fahimci tabbas ta fadi gaskiya ba’afi sati daya da bada shawarar ba na sayar da motocina guda uku gidana kai da duk wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu dunkulallun kudi saida na sayar dasu.
Acikin makonne na biya jama’a da dama basussukansu ni kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan nake kafin na samu abin duniya
UNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA
.
To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba.
Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai kasuwar fim ta daina yi dani……… Wannan duk wani Abune daya shude Abaya.
.
LABARIN AKWAI DAMBARWA KU DAI KASANCE DANI
[20:27, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI 03
.
(m) Nazir Adam Salih
.
Wannan duk wani abune daya shude abaya
.
Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka.
Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale abayanta.
Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi magana alokacin fashewa zatayi da kuka.
Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba.
Ban da shima su shafi’i sunzo wai karbar kudin kayan kwastum… Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar cikon kudinsu…
Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda nake tsaye inata faman karatun wasikar jaki
ta dafa kafadata tace dani.
Juyo ka dubeni hilal… Ina da shawarar da nake tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci.
.

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button