ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 71 to 80

Wai me yake faruwa Nabeel? Wallahi nima ban sani ba, domin munyi waya da Abbah yace mun ya fito daga gida ya taho, bayan dana iso naga bai zo ba nakira wayarsa bata shiga na d’auka matsalar network ne shiyasa banyi wani abu ba, ga Adnan ma wayarsa gaba d’aya akashe. 

Shiru sukayi Ra’eez yace dama nasan da wuya mu kwashe da sauki a wannan shari’ar, domin da manyan mutane abun ya had’o dole sai mun hada’ da ‘Yan sanda amma amintattu. 

Rafeek yace tabbas zargin da nakeyi ya tabbata, Ra’eez kaje ka samu Alkali ni nasan suna buk’atar ka, ina so kayi amfani da wannan damar ka k’ara samun wani abu, nasan dole Alhaji M. Sanda yayi wani abu, kuma k’arya ne ace Fawwaz baya k’asar. 

Ra’eez yace wallahi na ganshi. Jabeer yace yanzu ya zamuyi? Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in zanyi magana da abokina inspector Hamza nasan zai taimaka mana, kome ake ciki bazamu bari Fawwaz ya bar k’asar nan ba, dan nasan ayanzu suna gab da fitar dashi, dole muyi wani abu matukar muna son a kammala shari’ar cikin sauki. 

Ra’eez yace haka za’ayi, yanzu bara naje wajen Alkali, Jabeer kai da Nabeel kuje abi maku diddikin layin Abbah da Adnan, kafin nan Yaya yaje wajen Inspector Hamza sai kuyi magana dashi dole muna buk’atar ‘yan sanda saboda kada a cutar dasu Abbah. Kai suka jinjina gaba d’ayansu. 

Wucewa yayi ofis d’in Alkali yayinda Alhaji Mansur suke zaune a mota shida Kawun Jabeer suna tattaunawa. 

***

Wallahi Alhaji dole na sara maka, sai yanzu na yarda da maganar ka, tabbas kai d’in kwararre ne, amma abinda ban gane ba, gashi dai kace Adnan kawai za’a sace sai kuma gashi Alhaji Sulaiman bezo kotu ba, kuma alamu sun nuna zai zo d’in saboda sunce ya taho. 

Murmushi Alhaji M. Sanda yayi yana fad’in kana wasa dani Alhaji Barau, na fad’a maka duk wani wanda naga zai kawo mana tasgaru a wannan tafiyar zanyi komai dan na kaudashi. 

Bayan tafiyarka jiya na zauna ina wani tunani, nasan dole sai an buk’aci ganin shugaban makarantar su Fawwaz, gashi kuma bamuyi wata magana dashi ba hakan yasa zuciyata bata amince abarshi ba, hakan yasa na turama Lucky kwatancen gidanshi nace shima a d’aukemunshi idan ya fito zai taho kotu, yanzu haka suna wajen su Lucky nace sujirani a kammala shari’ar kafin a aiwatar masu, dan yanzu idan aka kashe su wata sabuwar shari’ar ce, kaji yanda nayi dashi. 

Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad’in yanzu kam hankali na ya kwanta, abinda ya rage na kira Ra’eez na siyeshi domin yayi watsi da shari’ar. 

A’a kada kayi haka Alhaji Barau, na fad’a maka zuciyata bata kwanta da wannan yaron ba, k’wazonshi yayi yawa, basirarsa baiwace daga Allah, kuma nasan bazai tab’a amincewa da cin hancinka ba, dan haka ka barshi kada kayi abinda zaisa ya gane ko kai waye, dole sai yana da shedu sannan zai gabatar da shari’ar, kuma jibi ne za’a kammala komai, dan haka ka barshi, idan yazo ma ka k’arfafa masa guiwa. Alhaji Barau yace shikenan nagode. 

Kwankwasa k’ofar da akayi tasa yayi saurin kashe wayar, izinin shigowa ya bada hakan yasa Ra’eez ya shiga. Bayan ya zauna Alhaji Barau yace sannu da kok’ari Ra’eez, gaskiya kana kokari akan wannan shari’ar, shiyasa ma na kaita zuwa alhamis saboda ka samu damar kammala sauran shedun ka, maganar Fawwaz kuma idan har yana da laifi dole a maidoshi. 

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in nagode Alhaji, nasan ai saboda nine kayi haka kuma naji dad’i. Alhaji Barau yace haba ai bakomai, abinda nakeso da kai ka tsaida hankalin ka ka samo cikakkar hujja dan bana so mutane suga gazawarka musamman da shari’ar take tsohuwa, gara ace kayi nasara zaifi. 

Kai Ra’eez ya jinjina yana fad’in insha Allah. Tashi yayi yana fad’in nagode zan tafi. Alhaji Barau yace ka kula da kanka. 

**** ****

Kada ka damu Rafeek, wannan abu ne mai sauki, ina tabbatar maka ayau zan kama Fawwaz, nasan Iyayen shi sun killace shi agida suna jira lokacin tafiyarsa yayi sannan su fiddoshi ya tafi, nasan dan wasa yanzu bazamu ganshi ba, amma nasan wanda zansa ya fiddo manishi cikin sauki. 

Rafeek yace nagode Hamza, sai maganar su Adnan, tabbas nasan sune sukasa aka kamasu, amma na tura su Brr. Jabeer suje abi mana diddikin layinsu. 

Hamza yace bara nakira amintattun ma’aikata na dole wannan aikin yana buk’atar sirri saboda kasan yanzu duniyar babu gaskiya zasu iya siye masu matattar zuciya acikin mu, shiyasa sai amintattuna kad’ai zan d’auka domin na saba fita dasu irin wannan aikin sirrin. 

Rafeek yace yanzu waye kake tunanin zai iya fito da Fawwaz? Murmushi Hamza yayi yana fad’in akwai babban abokinsa d’an uwan su Maid’akina ne, nasan yanda zanyi ya fito mana dashi. 

Hamdala Rafeek yayi yana fad’in nagode abokina. Hamza yace haba bakomai, insha Allahu komai zai tafi lafiya lau, kuma zan tsaya har sai an tabbatar da gaskiya. 

Wayar Rafeek ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Jabeer, saurin d’auka yayi. Jabeer yace Yaya gaba d’aya layinsu a waje d’aya ya dena aiki, sai dai kuma alamu sun nuna wajen da yabar aikin waje ne da yayi nuni da b’oyayyan waje dan ba cikin gari bane. 

Rafeek yace shikenan ku taho zamu san yanda za’ayi. Hamza yace ya dai? Fad’a masa abinda ya faru yayi. Murmushi Hamza yayi yana fad’in sace su akayi, idan kuma har abinda aka duba gaskiya ne to zamu duba daga inda layin ya tsaya dole suna ata wajen. Rafeek yace nagode. Sallama yayi mashi ya tafi. 

**** ****

Dan Allah Sweetheart ki nutsu, idan akabi komai a sannu babu abinda zai faru. Zama Momin su Marwan tayi tana goge idonta, kallon Yaronta tayi tana fad’in wallahi kashe shi zasuyi, kasan kuwa dokar k’asar saudiya? Ni na rasa wannan abu na Marwan, shida yake india bansan ya akayi yaje saudiya ba, duk da nasan yana fad’a mun yana kasuwanci a Madina amma be fad’a mun zeje can ba. 

Gyara zama saurayin yayi yana fad’in to dama baki san Marwan yana dillacin kwayoyi ba? Momy tace wallahi ban tab’a sani ba, idan nasani taya zan barshi, dan Allah *Nuress* idan kana da mafita ka fad’a mani. 

Murmushi Nuress yayi yana fad’in gashi kuma gobe zan koma, kuma gaskiya ni bani da wanda na sani a Madina, tunda Alhaji zai dawo gobe ki barshi yazo nasan abun zaizo da sauki tunda sune masu k’asar. 

Ajiyar zuciya tayi tana jawo wayarta tace bari na turama Khalil kud’i yace mun kud’inshi sunyi k’asa, nima ba kud’in gareni ba tunda duk na kwashe su nayi wannan siyayyar gashi kuma asara ta sameni, jira nake Alhaji ya dawo ya k’ara mani jari dan duka kud’in account d’ina bazasu wuce million goma ba. 

Matsowa Nuress yayi yana shafa mata baya yace kada ki damu Baby komai zaizo da sauki, tunda Alhaji ya warke daya dawo kud’inshi zasu dawo. 

Murmushi tayi tana kok’arin tura kud’i, tsaf Nuress ya haddace code d’inta. Bayan ta gama ta mik’e tana cire sark’ar zinarinta dan tunda suka dawo daga unguwa bata samu cire kaya ba ta samu wayar an akama Marwan hakan yasa hankalinta ya tashi. 

Durowa ta bud’e ta d’auko wani akwati, bud’eshi tayi saiga wasu sarkokin da abun hannu hada zobuna duk na gwal, maida wadda ta cire tayi ta rufe akwatin da mukullinshi ta maida mukullin inda yake. 

Koda ta juyo sai taga Nuress ya juya mata baya da alamu baisan abinda takeyi ba dan hankalinshi yana kan waya. Abinda bata sani ba ta cikin wayar yake kallonta. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button