Labarai

Kullum garin kwaki nake ci, don haka zan fi fahimtar matsalolin talakawa, Amaechi

Rotimi Amaechi, mai neman kujerar shugaban karkashin jami’iyyar APC sannan tsohon ministan sufurin ya ce yafi kowanne ‘dan takara cancanta, duba da asalinsa talaka ne tilis, The Punch ta ruwaito.

Ya fadi hakanne yayin tattaunawa da wakilan jam’iyyar APC a jihar Neja, saboda yadda zaben fidda gwani na karatowa.

A cewarsa sai ya fi saukin cudanya da talakawa saboda tuntuni a kowacce rana yana shan garin kwaki sau uku, kuma har yanzu bai dena ba.

Tsohon ministan ya bayyana yadda duk da irin gogewar da ya yi a baya wacce ya rike mukamai kamar; kakakin majalisa, gwamna, minista da kuma darakta-janar na kamfen din shugaban kasa har sau biyu, amma ya matukar bambanta da sauran ‘yan takarkari saboda shi mutumin mutane ne.

Ya bayyana yadda iyayensa suka kasance marasa hannu da shuni

“Babban abun da ya bambantani da su shi ne, su kuma ba haka ba. Zan iya zuwa gare ku baki-da-baki in yi muku magana,” a cewarsa Kamar yadda The Punch ta bayyana.

A cewarsa, kasancewar iyayensa marasa hannu da shuni ne ya sa ya samu damar gane halin da mutane ke ciki.

Ya cigaba da cewa:

“Ina da saurin kulla alaka da mutane. Iyaye na ba masu hannu da shuni ba ne. Mahaifina talaka ne kuma mahaifiyata ko turanci mai kyau ba ta ji. A baya na ci garin kwaki sau uku a ko wacce rana, don haka na san meye talauci.”

Ba bayyanawa mutanen Neja yadda ya fahimci matsalar rashin tsaro da ke addabarsu kuma ya san hanyar da zai iya kawo karshenta a jihar.

Ya yi tuni da yadda ya marawa Buhari baya duk da kasancewarsa dan arewa

A cewarsa:

“Na san wahalar da kuke, na taba rike kujerar gwamnan jihar Ribas lokacin ana garkuwa da jinjiraye ‘yan watanni biyu, ban taba bacci ba har sai na tabbatar kowa ya yi.

“Kuma a cikin watanni biyu na kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar Ribas.”

Ya yi kira ga mutanen are da sauran ‘yan Najeriya da su mara masa baya saboda kokarin da ya yiwa kasa a lokacin da ya goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da dubi da dan arewa ne ki kudu ba.

Ya bada labarin kalubalen da ya fuskanta inda ake ta cewa yana goyon bayan Hausa/ Fulani amma duk da haka ya yi kunnen uwar shegu.

Madogara LabarunHausa

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button