
.
Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo da kanta tace dani.
Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba haryanzu sai don…… Ta kasa karasawa tausayinta yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso.
Cigaba lauriyya…. Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin karyayyyiyar murya.
Kau…..narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare dakai…. Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka mutuntani ka maida ni mutum.
Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina sauraron abinda zataci gaba da cewa.
Hilal…..abinda nake kokarin baka shawara akai shine me zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me yiwuwa…… Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin data gani karara a fuskarta.
Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar zata kankameni.
Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so ba. Ta dan saurara.
Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin ciki dakai…. Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana. Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin zuciyata.
Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan fa babu irin nacin da baiyi min ba sa’ar da nake kan ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a finafinansa amma naki… Ke din nan da kanki sau nawa yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan….?
Duk da haka dai hilal….. Haka nan zaka daure muje ai durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na girgiza kai sa’ar danaji tayi shiru.
Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a fim domin ana ganin nazama asara.
To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in janyo masa asara sa’ar danayi shiru saina lura tuni hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya.
.
Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal….abin da nake so ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan HILAL dinka jarumin jarumai.
Kukanta yafara bayyana a fili.
Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye.
Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma kuma wani hanzari ba gudu ba.
Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin fahimta.
Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin jarumai yafara tallan kansa….. Wacce illa kike tsammanin hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu? Lauriyya ta bata fuska tace.
Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida murmushin yake tace.
Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi. Tana gama fadin haka ta kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro……….
.
SOYAYYAR GASKIYA AKWAI DADI BA IRIN SOYAYYAR SU O’O BA
[20:27, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-04
.
(m) Nazir Adam Salih
.
Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro.
.
Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina.
Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki daddadan murmushi. Lauriyya ta lura
Murmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu komai…. Kece kawai kika burgeni,
.
.
Sa’ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da lauriyya
Jeki kuyi magana dashi ni bazan karasa ba… Lauriyya ta dubeni zatace wani abu saikuma ta fasa me yiwuwa itama ta lura da taron yan alabaku mu samun fim dake tare birjik akofar kamfanin duk kuwa da uwar iskar da ake ketawa. Lauriyya ta rike hannuna tace.
Toh shikenan hilal jirani anan naje na dawo ta lura da fuskata haryanzu a murtuke take cikin damuwa.
Kada ka damu hilal komai zai zama daidai in Allah ya yarda.
Kaidai ka jirani. Tana gama fadin hakan saita matsa hannuna sannan ta jefeni da wani boyayyen murmushi mai kunshe da dubban manufofi ta juya tana rausaya ta nufi cikin kamfanin.
.
Na duba agogona bayana na jingine da itacen wayar lantarki dake daf da kantin na cika da mamaki sa’ar danaga tuni har mintuna goma sha uku sun shude da shigar lauriyya cikin kamfanin. Adaidai lokacin da damuwata ta fara tsananta saina hangi lauriyya ta fito alhajiji kuma yana biye da ita cikin fara’a akwai alamun farin ciki karara a fuskarsa me ywuwa na murnar zanyiwa kamfaninsa fim ne. Sa’ar da kuma na tuna da cewa nifa ayanzu ta kare min sai nafara tunanin to me yiwuwa ganin lauriyya ta nemi alfarma agurinsa ne yasashi murna.
Ina nan tsaye har suka iso gareni.
Yallabai! Yallabai!! Alhajiji yace dani cikin wata murya mai sautin amon alburushi sannan ya cafki hannuna kamar zai tsaga minsu saboda riko. Alhajiji kato ne baki mai katon ciki da dogon gemu babu gashin baki fuskarsa cikakkiya ce a mulmule kamar kwallon kafa duk sa’ar da yayi dariya saikaga ya zama tamkar mutum mutumi wannan ce tasa dayawa daga cikin shakiyan jaruman fina finan hausa suke so suga yayi dariya dan kawai su sha dariya. Wata shekara an taba fitowa dashi cikin wani shirin fim na abin dariya amatsayin dan daudu.
.
Saika rabe kuma daga nan Hilal ai
SINAD PRODUCTION kamar gidan kace. Ya dubi lauriyya cikin murmushi itama kuma ta dubeni da murmushin yaudara ta kifta min idanu.
Mu shiga daga ciki Hilal…. Wallahi nayi farin ciki da ganinka domin kaya ya tsinke agindin kaba daman yanzun nan nake kokarin buga ma waya saiga Lauriyya domin akwai wani babban fim dinmu na shekara da za’a fita gobe kai nake so ka fito a jarumi sunansa.
MUTUWA DA FARINTA TAKE TAKE!
Sa’ar da na dubeshi na dubi Lauriyya sainaji kamar na fashe da dariya domin ko shakka banayi nasan karya yakeyi dayace wai ni yayi niyyar sawa amatsayin jarumin tun farko kamata yayi a sanar dani tun satin daya gaba tabbas Lauriyya ce ta yaudaro shi.
.
Loading………. KASHI NA BIYU 2
[20:27, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI 05
.
(m) Nazir Adam Salih
.
BIYU
.
Daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin zubar ruwan saman akan kwanukan gidajen jama’a.
.
Na muskuta ahankali sannan na mike tsaye na nufi tagar dakin na dan janye gilashin tagar feshin ruwan saman gami da sansanyar iskar ruwan suka bugi fuskata. Nayi sauri na rufe tagar sannan nakoma na zauna akan kujerar ina nazarin dakin. shin wai yaushe za’a dauke ruwan nan ne. iskar dake cikin dakin ta fara karanci, hakan shiyasa fankar dake juyawa ta kasa yin maganin zafin dake addabata, gashi kuma idan nabude tagar dakin ruwa yajikani.
Nasake mikewa tsaye naci gaba da safa da marwa hakika indai har ba dauke ruwan nan akayiba to da kyar zan iya barci. Gashi kuma tuni karfe dayan dare ta gota.
Dakin danake ciki matsakaicine kamar dai sauran gidajen gwamnatin dake gurin. kujeru ukune kacal adakin kamar aya gami da tsohon gadon katakon dake dakon katuwar sabuwar katifar dana saya kwanaki biyu da suka wuce. daga bangaren arewa na dakin akwai
talabijin mai kala da bidiyo asamanta. sannan kuma asaman bidiyon fulawace ta roba acikin kofin tangaran Amatsayina na
TAURARON JARUMAN WASANNIN FINA-FINAN HAUSA
dole ne naga nayi kokarin kawata dakin danake kwana koh don taren bakin dake tafaman sintirin
kawomin ziyarce-ziyarce dare da rana. Yawan bakin da suke kawomin ziyara ne yasa kawuna ya waremin bangare guda agidan ya sanya
katanga tsakanina dashi domin nasamu damar ganawa da bakina, tunda dai haryanzu banyi aure ba
.
MAFARIN RIKICIN KENAN WANNAN RUWAN SAMAN.
[20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAƘAƘAI-06
.
(m) Nazir Adam Salih
.
Na koma bakin gadon na zauna sannan na cire rigata na kwanta, inajin zazzafar iskar da fankar dakin ke busawa akan fuskata sannan kuma lokaci guda ina mai adu’ar Allah yasa a dauke ruwan saman koh na bude kofar dakin nasha iska. Na rufe idanuna amma barci ya kasa daukata gashi kuma gobe tashin asuba zanyi domin awashegarin ne zamu fara sabon fim din kamfanin
SINAD PRODUCTION
mai suna MUTUWA DA MAFARINTA TAKE TAFE, amatsayina na
jarumin fim din dole ne nasamu isashen bacci domin na sami nutsuwar yin abin da daraktana yace nayi, toh sai gashi kuma zafi na neman hanani barci. toh ashe abun daban saniba shine bayan zafin dake addabata akwai wani al’amari daban dazasu kawo wa shirin fim din nawa matsala.
.
Ban san sa’ar da barci ya daukeniba acikin barcin ne nayi mafarki wai ana ta bubbuga kofar dakin danake ciki nayi firgigit na farka ina mutsutstsuka idanuna sannan ne to naji ana buga kofar dakin danake kwance nayi shiru cikin mamaki ganin mafarkin nawa ya zama gaskiya sannan kuma nayi mamakin shin wanene ke buga min kofata cikin wannan talatainin dare.
Nadubi agogon dake makale ajikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da muka shirya wasan fim din
DAREN MUTUWA dasu karfe biyu da rabi na dare Tsoro ya kamani domin kuwa banga wanda zai bugamin daki ba cikin wannan daren sai koh BARAWO
Aka sake bubbuga kofar dakin Das Das kamar ana bugun kwarya da sillan kara Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin kowane ne ke buga kofar dakin hakika yana tausayamata aka sake bugawa raf raf raf har sau uku. Gumi yafara kwararowa kan fuskata
hakika acikin mafiya yawan finafinan danake fitowa ni jarumine mai zafi marar tsoro to amma fa azahiri tsoro ne dani kamar farar kura dan karamin yaro ma yana iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona.
.
ABUN TSORO SAI MA GABA JARUMI HILAL
[20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-07
.
TA’AZIYYA GA IYALAN DAN UWA ABOKIN CHART WANDA DUK POSTING DINA SAI YA KARANTA YAKUMA YI COMMENT
IBRAHIM ABUBAKAR
.
ALLAH KAYIWA IBRAHIM ABUBAKAR KADUNA GAFARA KASA ALJANNAH CE MAKOMARSA DAMU GABAKI DAYANMU AMIN
.
(m) Nazir Adam Salih
.
Me yuwuwa kawuna ne nace da kaina to amma kuma ban yadda da kalaman da zuciyata keyiba domin nasan tun da kawuna ya ware min bangarena daban bai taba koda lekowa ba idan kuwa shine to nasan tabbas ba lafiya ba to
amma kuma idan shine ai kiran sunana zaiyi gami da kwankwasa dakin, jikina ya sake daukar bari na juya a hankali na dubi ‘yan kayan dake dakin indai dan wannan ne sai nabasu su tafi.
Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na daddakesu wasu kuma kamasu nake in daure to amma wannan daban wasane, yanzu kuma shine zahiri tunda gasu akofar dakina, Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi abude,ko da yake daman kuma kullum ahaka take kwana saboda maziyarta da abokan arziki dasuke yawan zuwa gurina da daddare to amma ba karfe biyu da rabin dare
irin wannan ba………..
Raf Raf Raf aka ci gaba da kwankwasa kofar Na yunkura hantar cikina na
rawa na nufi kofar dakin, ina ta salati da salalallami.
Wai…..wai wane ne? Nace muryata ashake ban iya shaida muryar amatsayin tawa ba. Maimakon abani amsar sai naji an sake kwankwasawa,
Wa……Nene? Na sake kuma tambayar shiru ba abani amsa ba haushi ya kamani sannan sai na tuno da fim din DAREN MUTUWA Muntaba wani sin
mai kamar wannan inda barayi suka zo suna kokarin balla kofata nikuma na bari sai da suka gama jingina ajikin kofar sannan na bude suka
zubo cikin dakin kamar an hankadosu nikuma nabisu na daddakesu. To yau ma zan kwatanta.
Nace cikin zuciyata Saidai kuma wannan karon inhar Allah yabani sa’a suka zubo cikin dakin to tsallakewa zanyi na gudu.
.
Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi. jin haka shiyasani tunanin komai bugun kofar kafadarsa ya jingina ajikin kofar yake kokarin balle kofar dakin. Nan da nan nayi wuf na zare sakatar dakin na janyo kofar da karfi.
Sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abin da yabiyo baya.
.
Ashe dai ko agaske jarumi ne wata zazzakar murya tace dani Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki daya sani wangame baki fayau ina dubanta
Atsaye abakin kofar sanye da bakar riga doguwa da jan lullubi jikinta na digar ruwan saman daya doke ta, wata mace ce ajin farko a jerin kyawawa.
Shin ko na iya shigowa, sanyi nakeji gaskiya, gashi kuma duk kayana sun jike
Na sake kallon katuwar akwatin mai taya dake hannunta na dama Nace
Malama Lafiya? Daga ina kike Meya kawo ki gidana cikin wannan daren?
Ta dubeni sannan ta jefeni da wani lallausan murmushin Allah
kashemu dan dadi, tace Lafiya kalau HILAL ,daga wata nisan duniya na
tawo domin kawai na ganka, na dade ina ganin finafinanka ina kaunarka raina na Begen ganinka. Shine naga bazan iya jurewa ba sai nazo naganka tun daga maiduguri Nake motar mu ce ta lalace ahanya shine mukayi dare yanzun ma direban motar ne yaga nayi dare
shine na roke shi yakawoni nan , Tayi shiru tana dubana.
Jarumi Hilal, Ina fatan yanzu dai ka gamsu Shin na iya shigowa, sanyi nakeji wallahi Hilal. Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane ta ajje akwatin atsakar
dakin sannan tajuyo ta dubeni.
In bazaka damu ba dan Allah nunamin inda bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. To ke kuma ki zauna dame Ina dubanta baki bude Tayi murmushi Sai na zauna aciki idan sun
sha iska saina mai dasu jikina nafito, Sannan fa takura min idanu tana dubana ko kiftawa batayi
Oh Hilal yau dai Allah ya nunamin kai wallahi kada kaga irin son danake ma duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nacema acan maiduguri
akwai kawayena da suke kirana da suna HILAL tayi shiru tana dubana me yuyuwa koh dan ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata ba Hilal yaya kake yimin irin wannan kallo ne, koh haryanzu baka amince dani ba?
Bahaka bane malama amma abin dake bani mamaki shine zuwanki cikin wannan tala-tainin daren kuma…… Ta katseni.
Nace dakai motar muce ta lalace, Haba Hilal nifa bakuwar kace.
To naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana. Haba hilal Mutane nawane suke ziyartarka arana daga jihohi daban daban kawayena nawa ne suka zo gurinka ai kwatancen gidanku ba wuya tunda agidajen gwamnati kake ga kuma lamba daman kuma ance kai kadaine abangarenka daban amma kada ka zargeni agurin maziyartanka naji.
Mukayi shuru muna duban juna sannan sai tasake cewa
Nunamin bandakin Hilal kada mura ta kamani da wannan jikakken kayan jikin nawa. zo muje nace da ita na shiga gaba tana bina abaya Bandakin gidan acan baya babban falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin tacikin
falon akwai kofar dazata kaika ciki
Ga kofar nan Nace da ita ina duban yala-yalan gashin kanta Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta
shige bandakin ta rufo kofar gararamm a daidai lokacin ne toh aka saki wata aradu Rugugugu………
.
INA MAI AMFANI DA WANNAN DAMAR A YAU GURIN MIKA TA’AZIYA TA GA MEMBERS DIN SOYAYYA RAYUWA GROUP FACEBOOK & WHATSAPP DAKUMA IYALAN IBRAHIM ABUBAKAR KD BISA RASUWAR SA
INA ROKON ALLAH YA GAFARTA MASA YASA ALJANNAH CE MAKOMARSA YA BAIWA YAN UWA DA IYAYEN SA DA MATAR SA HAKURIN JURE WANNAN GAGARUMIN RASHI DA SUKA YI ALLAH YA YI RIKO DA TAIMAKON YARAN DAYA BARI
TABBAS IBRAHIM BAZAMU TABA MANCEWA DA KAI BA ADUK LOKACIN DA MUKA TASHI YIWA KAWUNAN MU ADDU’A
.
Hadiza Sirajo
INA TAYAKI ALHININ RASHIN ABOKI NAGARI
[20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-08
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
MASU KARATU KUYI HAKURI DA WASU YAN KURA KURAI DA ZAKU CI KARO DASU TUN DAGA NA DAYA ZUWA NA 10 TAYANDA WASU SHAFUKAN ZAKU GA NA MAIMAITA SU KUMA HAKAN YAFARU NE SABODA WASU DALILAI NA KUSKUREN RUBUTU DANAYI TUN A FARKON LABARIN KUMA ZAIYI WAHALAR WARWAREWA SAI AKASHI NA 10 ZAREN LABARIN ZAI DAWO DAIDAI NAGODE. AMMA INA NEMAN AFUWAR KU
.
Na sake mikewa tsaye akaro na biyu naci gaba da safa da marwa cikin dakin. In har ba dauke ruwan akayi na bude tagar dakin ba zaiyi wuya in zan iya barci.
Banda wannan kuma al’amuran da suka faru ma a yammacin ranar sun isa su hanani barci na daga kaina na dubi agogo karfe daya na dare daidai.
.
Sa’ar da muka baro kamfaninsu alhajiji (Sinad Production) sai Lauriyya tace saita rako ni har gida.
Kiyi hakuri lauriyya kinsan yanzu ba kamar da bane sa’ar danake agidana yanzu kinga agidan yayana nake kare. Duk da yake dai bangarena daban ne to amma fa mutanen unguwa sun gama sa min ido dan sanin kanki ne duk yan fim yan isa aka daukesu ana son mune ana kuma kyamar mu. Lauriyya ta fahimci abinda nake nufi.
Toh hilal sai gobe din kenan ma hadu. Kada ka manta fa da asussuba alhajiji yace zaku fita…. Na dubeta cikin murmushi ban taba sonta har cikin zuciyata ba kamar wannan ranar.
Dan haka sa’ar dana fara zirga zirga acikin dakin inata lissafin dimbin basussukan da suke kaina sainayi mamakin irin tsabar son da lauriyya takeyimin.
Kafin naci gaba da labarin nan danake baka bari in baka hoton lauriyya. Dakuma ranar da muka fara haduwa da ita domin lauriyya tana da matukar muhimmanci acikin labarin.
.
LAURIYYA doguwa ce launin kofi mararta ashafe siraran yan yatsun kafarta da na hannu gami da dan madaidaicin bakinta ma’abocin tattausan murmushi tare da taimakon dara daran fararen idanunta gamida dogon hancinta mai kamar kan biro su suka fallasa kyawun da ta gado daga kakanninta fulani mazauna Gongola.
Haduwar mu da ita tsautsayi ce domin adaren wata juma’a ne nafito daga ofishina mukayi kicibis da ita dauke da jaka kallo daya nayi mata ta burgeni.
Sannan naga zatayi daidai da budurwar da muke bukata acikin fim dina na DAREN MUTUWA.
Kaine Hilal?
Kwarai kuwa nine
Wallahi daga gongola nake masauki nake nema. Hakanan a saukake don tsabar taren aradu da ka dakuma neman tsautsayi da rashin tunani sai kyawunta ya rufe min idanu na samar mata masauki batare da na binciki abinda ya rabo ta daga gida ba. Yan kwanaki kadan na fahimci ashe tanada ilmin boko mai dan tsayi domin har diploma ce da ita abangaren tsimi da tanadi. Haka nan tanada wayo da hikima hakan ce tasa na maida ita amatsayin sakatariya lokaci lokaci kuma nakan jefata a fina finai naso ace duk fim din da zan fito tare zamu fito to amma saboda acewarta.
Bana son fuskata tayi yawa acikin fina finai sai kawai na kyaleta ban kuma tambayarta dalili ba.
Har yanzun nan da nake safa da marwa cikin dakin bayan shekaru biyu cif cif da faruwar al’amarin ina tambayar kaina shin me ya raba lauriyya daga gaban iyayenta? Hakika lauriyya ta fara shiga raina sosai.
Adacan sa’ar dana fara ganinta kyawunta ne kawai ke burgeni babu dadi ba ragi. To amma ayanzu abin ya wuce haka lauriyya ta zama jinin jikina abin tunaninaba dan komai ba kuwa sai don na fahimci ita kadai ke damuwa da fushina ita kadai ke farin ciki da karuwata ita kadaice komai ke sani dariya ta dauke min kewa aduk lokacin dana shiga damuwa.
Gobe in Allah yaso saina tambayeta labarinta baki daya. Nayiwa kaina alkawarin hakan.
.
Haryanzu ruwan saman ake tafkawa kamar da bakin kwarya na sake nazarin sabon dakin dana dawo cikin takaici domin baikai ko rabin bandakin da nake wanka ba atsohon gidana dana sayar na biya bashi.
Dakin danake ciki dan kankani ne kamar dai sauran dakunan da ake yiwa boyi boyi agidajen gwamnati kujeru uku ne kacal dakin ya iya dauka. Koda yake dai in ma zaici fiye da hakan ba samu zaiyi ba domin duk na sayar da kujeruna sama da talatin na biya bashi ayanzu kam in kadauke tsohon gadon katakon dake dakin katifar daya dana tsira da ita gamida talabijin daya mai kala da bidiyo da rediyon jin labarai mai gidan kaset daya dakin babu komai sai shegen zafi gamida manya manyan saurayen dake fizgar rigata ta baya ina kwacewa dakyar.
Dakin danake zaune ayanzu an tanadae shi ne dan yaron gida dayake kawuna ma’aikacin gwamnati ne ya kuma san irin yadda mutane ke ta kawo min ziyara sai ya shawarce ni dana dawo nan na tare tunda da dai karayar arziki tazo min.
.
Nakoma bakin gadon na zauna sannan na cire rigar dake jikina na kwanta akan tsohon gadon inajin zazzafar iskar fankar dake busowa akan fuskata.
Sannan kuma lokaci guda ina mai addu’ar allah sa adauke ruwan kona sami damar bude kofar nasha tsabtatacciyar iska.
Ina nan kwance idanuna rufe zuciyata cike da zullumin basussukan da ake bina gamida tunanin Lauriyya ga kuma shegen zafi wannan shi ya hana barci ya daukeni. Nashiga cikin damuwa domin nasan gobe da asusussuba zan tashi domin tafiya sabon fim din da aka daukeni na Sinad production. Gashi kuma yanzu ba da ba. Domin banida ko jaki ballantana mota.
Bansan sa’ar da barci ya daukeni ba adaren.
Acikin barcin ne harna fara mafarki wai anata bubbuga min kofar dakin danake ciki kuma wai muryar lauriyyace ke kirana. Nayi firgigit na farka ina mitsitstsika idanuna sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa a gaske kofar dakin nawa ake ta bugawa…….
[20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-09
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa da gaske kofar dakin nawa ake bubbugawa.
Nayi fakare kamar zakara zuciyata na harbawa cikin mamakin ganin mafarkin nawa yazama Gaskiya.
To saidai kuma buga kofar yasani cikin damuwa domin na lura haryanzu sheka uban ruwan ake kamar da bakin kwarya tabbas nasan ba lauriyya bace.
Toh wanene ? Na tambayi kaina nadubi agogon dake jikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da mukayi shirin flm din Daren mutuwa dasu.
Karfe biyu da rabi na dare. Domin kuwa banga wanda zai buga min kofa ba cikin wannan uban daren sai ko barawo.
Aka sake bugun kofar dakin Das Das Das kamar ana kugun kwarya da sullen kara. Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin ko wanene ke bugun kofar to yana tausaya mata.
Aka sake bugawa Raf Raf Raf har sau uku gumi yafara sartu a goshina hakika amafi yawan fina finan danake fitowa ni jarumi ne mai zafi marar tsoro to amma azahiri tsorone dani amar farar kura domin dan karamin yaro ma na iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona.
Me yiwuwa lauriyya ce…. Kai ba ita bace babu mamaki dai kawuna ne nace dakaina. To amma jikina baiyi amanna da kalaman zuciyata ba domin tun ranar dana tare agidan kawuna bai taba lekowa bangaren danake ba in son ganina yake saidai ya turo ayi kirana indai shine to tabbas ba lafiya ba. Can kuma sai wata zuciyar tace dani to ai kuwa idan shine kiran sunana zaiyi kai tsaye basai ya tsaya yanata kwankwashe kwankwashen kofar ba. Wannan shiyasa cikina ya dada durar ruwa jikina ya dauki bari nan da nan naji hakorana sun fada haduwa da juna kaf kaf kaf saboda tsoro.
Najuya ahankali akan tsohon gadon na dubi yan tarkacen da suke dakin nace da kaina. In dan wannan ne sai na basu su tafi sun dauka jiya yau ce. Kawai wayannan barayi da rashin basira suke su basuda labarin na tsiyace ne ?
Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na doddoke su acikin sauki ina hura hanci wasu ma darakta yasa na kakkama su na daure.
To amma duk wannan daban domin wasa ne yanzu kam shine azahiri domin gasu akofar dakina.
Na lalubi aljihuna na dauko rubabbiyar naira goman da mai mashin yabani canji daman naira hamsin ce kadai ta rage a aljihuna sa’ar da zamu rabu da lauriyya na bata ashirin ta tafi gida nikuma na hawo acaba naira ashirin nakaraso gida da goma. Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi a bude koda yake kusan ko yaushe ma ahaka take saboda abokai da maziyartan dake yawan zuwa gurina cikin dare wasu lokutan ma sai na dawo daga daukar fim cikin dare zan sami baki suna jirana. Amman ban taba samun bakin kusan karfe biyu na dare ba. Raf Raf akaci gaba da buga kofar na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin inata salati da sallallami.
Wai wan….ne ? Nace muryata ashakre ban iya shaida ta ba amatsayin tawa, maimakon abani amsa sainaji an sake kwankwasawa.
Wai wanene? Nasake kuga tambayar shiru ba amsa ba. Haushi yakamani saina tuna da fim din DAREN MUTUWA. Mun taba yin wani guri mai kamar wannan inda wasu barayi sukazo suna kokarin balla kofata nikuma nabari saida suka jingina da kofar suka gama bada karfinsu akanta sai na bude kofar da karfi suka zubo dakin kamar an handakosu nikuma na doddoke su. Yau ma zan maimaita nace cikin zuciyata saidai kuma sabanin wancan karon yanzu idan Allah yabani sa’a suka fado cikin dakin tsallake su zanyi na Gudu.
Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi jin hakan shiyasani tunanin me yiwuwa mai bugun kofar jikinsa ya jingina akofar don haka cikin sauri saina zare sakata na janyo kofar da karfi sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abinda ya biyo baya.
Ashe dai ko a gaske Jarumi ne. Wata zazzakar murya tace dani. Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki.
Mace ce tsaye akofar dakin sanye da doguwar riga baka da jan lullubi akanta jikinta na digar ruwan saman daya daketa hakika ajin farko ce ajerin kyawawa.
.