
.
Mun shafe kusan rabin minti muna tsaye muna duban juna haushi da fargaba da mamaki sun hanani magana.
Shin ko na iya shigowa sanyi nakeji gaskiya kuma duk kayana ajike suke. Idanuna suka kai ga katuwar akwatin mai taya dake hannunta sai hakan ya tuno min da farkon haduwarmu da LAURIYYA.
Malama ina fatan dai lafiya?…. Ma’ana daga ina kike cikin wannan uban daren? Kuma da wacce kika zo? Yar budurwar ta dubeni sa’annan t jefeni da lallausan murmushin Allah kasheni don dadi.
Lafiya kalau Hilal tun daga wata nisan duniya nataho gareka domin kawai na ganka na dade ina ganin fina finanka ina kaunar araina da begen ganinka shne naga bazan iya jurewa ba sainazo na ganka da idanuna. Ta danyi shiru tana kokarin share ruwan dake sartu daga cikin gashinta zuwa fuskarta. Gashi dai cikin duhu muke tsaye dakin babu wuta amma duk dahaka fuskarta har sheki takeyi idan akayi Walkiya. Ko makaho ya lalubeta yasan Allah yayi halitta agurin.
Tsarki ya tabbata ga mahaliccin kyawawa.
Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba…
.
KUCI GABA DA HAKURI DAI SAURA KIRIS HARHARDEWAR DA LABARIN YAYI WAJEN TYPING DINA YA WARWARE
[20:29, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-10
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar idanunta sama cikin rashin fahimta can kuma saita girgiza kai gamida wani alakaron murmushin.
Oh kana nufin daga inda nake? Daga maiduguri nake motar mu ce ta baci ahanya shiyasa mukayi dare yanzun ma direban motar na roka Allah da Annabi shine yakawo ni har nan tayi shiru tana dubana.
Jarumi Hilal ina fatan dai yanzu ka gamsu…..shin na iya shigowa?
Sanyi nakeji Wallahi hilal akwai wani abu a tattare da ita dake damuna fiyeda yawan murmushinta gashi kuma ko ganina azahiri bata taba yi ba sai yanzu yanzu ma kuma acikin Duhu.
.
Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane. Ta ajiye akwatin sannan ta juyo ta dubeni.
In baka damu ba don Allah nuna min bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf.
Gabana yafadi ras na bude baki cikin kaduwa nace Ki shanya kayanki? Na tambayeta adolance. Ta gyada kai. To ke kuma ki zauna dame? Tayi murmushi lokaci guda tasa hannu ta yane jikakkken lullubin dake kanta nan da nan siraran gashin kanta baki sidik suka zubo kan kafadarta koda walkiya ta hasko cikin dakin sainaji zuciyata na harbawa da sauri na dade banga gashi da kyawun nata ba.
Saina zauna aciki idan sun sha iska na maida kayana nafito. Na sunkuyar dakaina kasa a rude kai yau na gamu da gamona. Nace cikin zuciyata koda na daga kaina sainaga ta kura min idanu kamar zata hadiye ni.
Oh hilal yau dai Allah ya nuna min kai. Wallahi kada kaga irin son danakeyi maka duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nace ma acan maiduguri akwai kawayena da yawa da suke kirana da suna HILAL.
Tayi shiru tana dubana me yiwuwa ko don ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata bane.
Hilal yaya kakeyi min irin wannan kallon ne haryanzu baka amince dani ba. Akaro na farko sainaga ta dan hade fuska amma duk da hakan saida idanunta suka nuna alamun murmushi.
Bahaka bane malama abin da haryanzu ke rudani shine zuwanki cikin wannan talatainin dare kuma….. Ta katseni.
Nace dakai motar muce ta lalace haba hilal nifa bakuwarka ce in kuma korata kakeyi shikenan bari natafi nagode. Ta yi nan tsaye bata dai motsa ba akaro na farko saina sassauta murya nace da ita a tausashe.
Toh naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana?
Yar budurwar ta dubi akwatin dake kwance atsakar dakin sannan ta dawo da dara daran idanunta kan fuskata.
Hilal kaga in bakaji dadin zuwana ba simple ce kawai na fita saina fice ma daga daki ko a tasha na kwana da safe na koma garinmu yaya zaka sani agaba da irn wadannan tambayoyi kamar wani tsohon dan sanda. Ta harareni gamida murguda min baki ta danyi shiru tana maida numfashi.
In banda abinka hilal mutane nawa ne suke zuwa ziyartarka arana daga jihohi daban daban ? Kawayena ma nawa ne suka zo gurin ka? Ai kwatancen gidan fitacce kamar ka ba wahala bane musamman agidaje irin wadannan na gwamnati kasan fa kowane gida yanada lamba…kodayake dai zuwana ne kawai baka so. Ta juya min baya tana kallon kofar dakin.
Allah baki hakuri nace da ita a tausashe juyo mu fuskanci juna basai kin juya min baya ba yar budurwar ta juyo da faffadan murmushi.
Lah hilal menene kuma na bata rai nifa ba fushi nayi ba ai ko ina fushi da mutane hilal kai ka wuce nayi fushi dakai idanunta suka kai ga agogon dake makale abangon dakin. Na dubeta nima karfe biyu da rabi na dare 2:30am
.
Lah wannan ai hotonku ne na fim din Daren Mutuwa. Budurwar tace cikin karaji sannan cikin hanzari ta matsa kusa da agogon ta kura masa idanu.
Nikuwa hilal daman inason na tambayeka na dubeta cikin mamaki.
Me zaki tambayeni? Yar budurwar ta dora dan yatsanta na hagu akan hoton ta nuna fuskar Lauriyya tace. Amma wannan yarinyar ko agaske ba’a fim ba budurwar kace ko? Naji gabana yafadi ras na girgiza kai.
Kokusa kada kiyi tunanin haka fim ne kawai kinsan ku yan kallo kusan ko yaushe kuna da wannan kuskuren fahimtar.
Irin kallon datakeyi mane a fim din na lura ya wuce na wasa….. Na dubeta akaro na farko sainayi mata murmushin yake..bakya rabuwa da kame kame baiwar Allah bakisan yan dirama bane yanzun nan sai suyi miki abu kiga kama da gaske nan kuwa karya suke. Bata juyo ta kalleni ba haryanzu kallon hoton take amma na lura da murmushinta ba zato ba tsammani saita juyo ta fuskance tace.
Ai kuwa kyakkyawa ce. Mukayi shiru na tsahon lokaci muna duban juna.
.
Nuna min bandaki hilal kada mura ta kamani da wannan jikakkun kayan dake jikina.
Zo muje nace da ita domin nagaji da jayayya.
Nashiga gaba tana bina abaya kamar bawa da balarabe bandakin acan bayan falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin ta cikin falon batareda k fita waje ba.
Ga kofar nan nace da ita ina duban yala yalan gashin kanta. Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin gamida rufo kofar gararam da karfin gaske karar rufr kofar suka cakude da rugugin aradun nayi sauri na rufe kunnena.
Akwai lokuta da dama da bana son sautin aradu domin ji nake kamar ni zata fadowa………
[20:30, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-11
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Domin ji nake kamar ni zata fadowa..
.
Na juya ahankali na nufi dakin ina shiga saina janyo kofar dakin amma ban rufe ta gaba daya ba. Na zauna abakin gado nafara jujjuya batun wannan kyakkyawar budurwa mai ziyarar tsakar dare cikin zuciyata.
Akwai wani abu atattare da ita dake bani tsoro na lura da ita ko kusa ko alama batada tsoro haka nan batada kunya kuma babu alamar bakunta ajikinta bugu da kari kuma acikin amsoshin tambayoyin danayi mata akwai amsa daya na tabbata karya takeyi.
.
Shin duka duka wata na nawa da tarewa awannan gidan da har maziryata na zasu kwatonta mata inda nake? Nidai a iya tunanina tun dana tare agidan bansamu wani maziyarci daga bakuwar jiha ba ina nan zaune ina jiran fitowarta na dubi agogo karfe uku saura kwata 2:45am nasan ni da sake samun wani isashshen barci kuma sai abinda hali yayi tunda dai nan sa sa’o’i biyu da motsi zamu fita sabon fim dinsu Alhajiji. Nayi murmushi sa’ar dana tuna yaudarar da Lauriyya tayiwa alhajiji kai wannan al’amari da daure kai yake nace da kaina saikayi mamakin yadda kudi da mata suke tsananin tasiri azuciyar Mazaje.
Naji gabana yafadi sa’ar da wani tunani ya fado min nan da nan naji gumi ya fara sartu agoshina yanzu idan garin Allah ya waye wani kokuma kawuna yazo ya sameta adakin nan me zance dashi? Kirjina yafara dakan uku uku tuni nasan mutanen unguwa sun dade suna zuzzuga kawuna akan wai dole sai ya hanani harkar wasan kwaikwayo domin wai duk yan wasan kwaikwayo yan iska ne marasa mutunci da kyar nasamu na shawo kansa. To yanzu kuma bayan duk wannan idan yasami mace ta kwana adakina fa?
Gumi yaci gaba da sartu akan goshina kaga dan samari wata zuciya tace dani abu mafi sauki shine data fito daga bandaki katafi da ita gidan kawunka ka kwankwasa masa kofa nasan in nayi masa dogon bayani yana iya fahimta sai su kwana tare da matarsa.
Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji wani abu kamar sautin mota wajen gidan na dubi agogo karfe uku harda kusan rabi 3:30am kai amma dai ta dade cikin bandakin nan kodana lissafa sainaga kusan sa’arta guda aciki na mike tsaye cikin sauri na nufi falon ina zuwa saina wuce kai tsaye zuwa kofar da zata kaini har bandakin ga mamakina sainaga kofar a bude. Gabana ya ya fadi na mtsa ahankali na kara kunnena ajikin kofar bandakin ko zanji motsi shiru sai sautin zubar ruwan sama akan kwanuka zuciyata na harbawa saina kwankwasa kofar bandakin. Malama haryanzu kina ciki? Shiru ta gaida kunnuwana.
Malama ina kike ne? Na sake kiran sunanta to saidai kuma ni kaina nafara tunanin bazanji amsar komai ba.
Na bude kofar bandakin ahankali sainaga WAYAM. Babu ita babu alamarta. Nan da nan na ruga aguje zuwa kofar gidan. Ina kike ne? Adaidai lokacin ne to naji sautin injin mota an tuka anbar gidan. Nakarasa aguje amma ni kaina nasan bazan taba samun motar ba na tsaya sororo ruwan saman na dukana ina hangen danjar motar tana daukar idona kamar gauta acikin rana.
Sannu ahankali har na daina hangota.
.
UKU 3
.
Nadawo cikin dakin jikina na rawa kamar tsohuwar data sami kwarto karkashin gado. Na zauna jagwaf atsakar dakin kamar tsohuwar saniya na kurawa akwatin data bari danu sama da tambayoyi dari suka fara turereniya cikin zuciyata.
Shin wacece ita? Daga ina take? Menene dalilin zuwanta? Yanzu kam dana tabbata TA GUDU na tabbata duk abinda ta fada abaya karya takeyi. Sannan babu zato babu tsammani saina tuno da akwatin datazo da ita.
Na mike zumbur kamar an sokeni da kibiya na nufi inda akwatin take jikina na tsuma na daukota na dora akan gado sannan na fara kokarin budeta. Atunanina acikin akwatin ina iya samunwata shaida da zata sanar dani ita wacece. Allah ma ya taimakeni data bar akwatin nace cikin zuciyata.
Na danna mabudan akwatin ina mai wasi wasin budurwar ga mamakina sainaga ta bude fayau. Na dubi cikin akwatin ina mai mamakin ganin babu komai ciki sai wani dan kyallen yadi fari lullube da wani abu. Jikina ya dauki rawa kamar mazari. Nasa hannuna kan farin kyallen sannan na janye farin kyallen.
Numfashina ya kauracewa kirjina yawun bakina ya kafe kana yar autar cikina ta manne jikin hanjin cikina. Akwance male male akasan akwatin.
DAN JARIRI NE.
Sabuwar haihuwa kyakkyawa dashi kamar dan larabawa akusa dashi kuma takarda ce ko liketa ba’ayi ba ajikinta sakone a rubuce kamar haka……..
.
HILAL.
Na dade ina ganin fina finanka kuma kana matukar burgeni hakan nema yasa begenka yafara mamaye zuciyata. Hakika tun danake arayuwata ban taba ganin jarumin danake kauna ba kamar kai ka iya shiri kwararrene kai mai burge yan kallo to saidai kuma katsam sai gashi acikin fim dinka na DAREN MUTUWA ka bani haushi kasa na tsaneka. Lokacin da ka dauki jaririn nan acikin fim din zaka jefa shi cikin rami sainaji kamar da gaske zaka jefa ciki.
Baka dade ba da gama fim din sai nima na sami nawa jaririn abin dai kamar acikin dinka na daren mutuwa CIKIN SHEGE NE don haka sai naga abinda ya dace shine na sako shi cikin akwati na kawo maka shi tunda dai ka saba jefa jarira acikin rami me yiwuwa kana iya rabani da nawa abin kunyar ka taimaka ka Jefar min da shi. In kuma kana so to gashi nan nabaka shi kyauta a matsayin ka na kwararren jarumin fim din
DAREN MUTUWA.
Sai anjima kada ma ka nemeni domin bazaka taba samuna ba domin GARIN MU DA NISA…..!
.
NA ajiye takardar cikin akwatin jikina na rawa sannan na dubi jaririn dake kwance cikin akwatin sainaga kamar yanayi min dariyar kuda. Na dafe kirjinsa da tafin hannuna na girgiza kai cikin Kaduwa lallai kam kyauta ta musamman. Hakika kam nayi dace da kyautar kyakkyawan jariri in da ba don MATACCE BANE.
.