ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA QAQAI COMPLETE HAUSA NOVEL


.
ALAKAKAI-12 Loading……
[20:33, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-12
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Hakika kam da nayi dace da kyautar kyakkyawan JARIRI in da ba don MATACCE BANE.
.


.
Idanuna suka fara zafi banyi mamaki domin gumin dake sartu akan fuskata kamar ruwa tuni yafara shigar min idanu.
Nasake duban kyakkyawan jaririn dake kwance acikin akwatin na tsahon lokaci sannan sannu ahankali saina janyo farin kyallen na lullubeshi gami da rufe murfin akwatin ahankali kaikace tsoro nake kada na tashe shi daga barcin dayake. To saidaikuma nasan shi da farkawa sai ranar da aka busa kaho.
Kafin na rufe akwatin saida na dauke wasikar da budurwar tasa aciki na tura ta cikin aljihuna sannan na mike tsaye ina muzurai ni kadai kamar tsararraren kwarto.
Shin wace mata ce wannan? Shin danta ne? In kuma bana ta bane menene alakata da jaririn menene kuma dalilin dayasa ta rasa wanda zata kaiwa gawar jaririnin sai Ni? Kai wannan rashin imani na mutanen duniya da yawa yake.
Haryanzu ba’adaina tsugu uban ruwan saman ba haka nan lokaci lokaci saikaji an ruguza aradu kamar ta tsaga dakin. Ama ni duk wannan ba ita bace agabana babban abinda yafi tayar min da hankali shine yaya zanyi da jaririn?
Ka kirawo yan sanda wata zuciya ta shawarce ni. Acan kuma wani bangaren na zuciyata akace dani.
Kai shashashan banza idan ka sake ka kirawo yan sanda ka kashe kanka daman tsammani zasuyi sato shi kayi ka rude shine ka kirasu.
Basai kayi musu bayanin yadda budurwar ta kawo maka shi ba? Wata zuciyar ta sake kwabata in ka sake ka kira yan sanda ka karasa rusa kanka a harkar fim domin dole ne labari ya watsu abokan hamayyarka kuwa sun sami makamin da zasuyi ta yakarka har sai sun kai ka kasa.
Can kuma sai wata zuciyar tace dani
kai dan samari rufawa kanka asiri tun wuri ka dauki jaririn nan yadda ta baka shi kaima kaje ka jefar dashi ka hutawa kanka tonon silili.
Kokuwa na tashi yayana na sanar dashi? To sai dai kuma haryanzu zuciyat nan nata kururuwa cikin kwakwalwata kai fa baka rabuwa da sakarci Wallahi mutumin da tuni mutanen unguwa sun gama zuzzuge kawun naka ana cewa yan iska ne ku yan shirin fim bakajin cewa idan yaganka da jariri zai iya tunanin ko naka ne aka kawo maka shi har gida dan bariki?
Ai kawai ka dauki jaririn nan bakinka alaikum ka jefar dashi.
Abinda yakama nayi kenan nace da kaina. Nasan dai yanzu babu jami’an tsaro akan tituna ballantana kuma mutane na mike tsaye cikin sauri ina mai fargabar kada gari ya waye min akamani da jariri dumu dumu ahannu.
Wani zazzafan gumi yayi zarya tun daga kan doro wuyana har zuwa bayana. Kagafa hakane. Nace da kaina. Lallai kam mafita ta daya ce kawai na hanzarta na dauki jaririn nan na jefar dashi na huta in yaso daga baya na nemi uwarsa. Amma tabbas in har maganar ta fito fili to ko kawuna bai zargeni da komai ba sai mutanen sunyi ta yawo da zancen me yiwuwa ma wata rana yazama abin gori ga ‘ya’yana.
Akaro na farko tun bayan da akayi min kyautar jaririn sai naji sanyi sanyi araina. Kwakwalwata kuma tafara tunani sosai da sosai.
Na nufi kofar dakin ahankali sannan na shiga falon. Na duba hanyar da zata kaika har bandaki saina girgiza kaina. Lallai budurwar tayi kyan dan maciji na wuce kai tsaye na nufi kofar da zata kaini har waje na budeta kadan. Sassanyar iskar dake ta faman watangarariya da kwayoyin ruwan dake zubowa adoron kasa daga sararin Subhanahu Wata’ala ta bugi fuskata yan sa’o’i kadan da suka wuce bazan iyayin maraba da iskar ba amma ayanzu saita zame min tamkar na’urar sanyaya daki alokacin zafi.
Na juyo dakin cikin sauri na sunkuya abakin gadon sannan na tura hannuna na dauko katuwar rigar leda ta ruwa wacce azamanin danake tashe aharkar fim idan zamu tafi daukar shirin fim lokacin damina da ita nake fita.
Koda na dauko rigar na karkadeta saina dorata akan rigar dake jikina sa’annan na fara balla maballin rigar bugun zuciyata yafara dawowa daidai ayanzu na sake sunkuya karkashin gadon akaro na biyu na dauko takalman ruwana nasa sannan na duba akwatin da mataccen jaririn ke ciki na tambayi kaina da cewa…
To yanzu kuma ina zaka jefar da akwatin waje na farko daya fara zuwa zuciyata shine wani katon kango dake bayan gidan wani attajiri wanda ya saye ginin kwamnatin gidaje uku ya hadesu ya kera katon gida.
Katon kango ne yadade ahaka an zagaye shi ba’a gina ko daki daya acikinsu ba. Lokacin damina kamar yanzu kangon cike yake da dogayen ciyayin tafasa da rai dore awani lokacin dan daya wuce zamanin muna yara acikin kangon muke bata lokaci muna wasan boyayyeniya idan mun taso daga makaranta. Bazan manta ba maciji ya taba cizon abokina Sani Ayuba acikin kangon. Nayi sauri na kawar da tunanin hakan daga zuciyata tabbas nan ya dace nakai akwatin.
Na sunkiya ahankali na dauki akwatin mai tsaya wacce jaririn ke ciki na nufi kofar dakin cikin sauri.
Koda na bude kofar dakin sainayi murmushin yake cikin duhun daren kamar awani fim din Daren mutuwa.
Allah sarki jiya ba yau ba nace da kaina.
Na dade akofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi. Daga karshe dai sai……
[07:09, 1/20/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-13
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Na dade a kofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi daga karshe dai sai na saduda naga tsoro da fargaba basu amfana ta awannan lokacin sai kawai na jefa kafata waje na shige cikin ruwan ina mai Addu’ar Allah yasa duk wanda muka hadu dashi yayi kuskurena a matsayin jami’in tsaro.
Naci gaba da tafiya ruwan saman dake zuba kamar da bakin indararo sai dukan bayan rigata yake fas fas. Duk dayake dai nayi sa’a duk kusan bangaren gidajen an dauke wutar lantarki amma Hakan bai bani kwarin gwiwar fitowa nayi tafiya kai tsaye cikin takama ba
Ina tafiya ina bin inuwar bango kamar Kadangare wata sa’ar ko Walkiya akayi sai na rabe kadan kafin naci gaba da tafiya.
Ina nan tafe lokaci guda kuma duk Addu’ar da Tazo bakina sai in karanta… Kwatsam sai nafara hango gidan attijirin tsakanina da gidan akwai yar tazara kafin ka kai ga kangon dake jikin gidan saikayi tafiya cikin wata yar farfajiya wacce babu gine gine a cikin ta sai ciyayi haka nan kuma anan filin wasan kwallon kafa na samarin Unguwar yake.
Gabana ya fadi sa’ar dana hango fitilun lantarki naci a kofar gidan dakuma kan katangar reras dasu kamar taurari tabbas injin wutar lantarki ya kunna.
Ganin hasken ne ya sani sauya shawara na kauce nabi wata yar siririyar hanya wacce ta ratsa ta cikin filin wasan kwallon kafar takuma bi ta bayan gidan attijirin zuwa cikin kangon da nake hari.
A daidai lokacin ne to najiyo sautin abin da ya kusa sa akwatin dake hannuna ta subuce….
Ko shakka babu mutum ne abayana. Nayi mutuwar tsohuwa a tsaye tsoro da fargaba suka hanani juyawa. Wani abu ya dunguri dunduniyar takalmina na dauke numfashi cak ina kokarin zama gunki har yanzu wanda ke bayan nawa bai ce Dani uffan ba sannan ne to naji wani gurnani abayana marar dadin ji
Gashin jikina ya mimmike tsaye kamar gashin bushiya tuni wani zazzabi zazzabi yafara kokarin rufeni nayi ta yan maza na juya a hankali na dubi bayana sai mukayi ido hudu da bawan Allah mai bakaken idanu kamar ifritu yana gurnani wani dankareren kare ne mai jajayen idanu da zako zakon hakora kamar tarko babu alamar farin gashi a jikinsa.
Wani katon kare ne ya kwada min uban haushi WAW-WAN Nayi tsallen gefe guda sai yakawo min sura santsi ya kwashe ni nafada cikin cabin ruwan nagama gigicewa maimakon na Jefar da jakar saima na sake mikewa tsaye da ita kankame a kirjina kai kace wasu makudan kudade ne aciki.
Mukayi tsaye cirko cirko nida karen ya dube ni na dube shi saina juya da gudu karen kuwa yace da wa Allah ya hadashi bada ni ba.
Tun kafin tafiya tayi nisa karen ya fara kawowa dunduniyata sura. Allah ya taimake ni da takalman ruwa a kafata akaro na biyu ne ya sami Nasarar farka rabin rigar ruwan dake jikina.
.
Wayyo Allah.
Na kwalla ihu na manta da abun da ke dauke a hannuna na sake juyowa a firgice na kaiwa karen duka da jakar dake hannuna Saidai kuma dukan na matsoraci ne domin bai iya kwantar da ko da yar budurwa ba ballantana mahaukacin kare alokacin ne to
TAFARU TA KARE. Wani abu mai kamar guduma ya sulalo ta cikin duhun daren ya daki tsakiyar kaina kafin na gama warwarewa sai wani abu kuma mai kamar katakon duka ya daki bayana naji kamar an soke ni da mashi.
Wayyo Allah na kwalla ihu.
Zakayi ihu ma sai agaba shege BARAWO Meka sato acikin akwatin?
Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren………..
.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button