ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA QAQAI COMPLETE HAUSA NOVEL


.
Har sa’ar dana dawo dakin karbar bakin lauriyya tana nan kamar yadda nabarta kanta kife akan teburina na tsaya akanta.
Lauriyya na kira sunanta akwai alamar rawa a muryata. Ta dago kai ta kalleni da wani fatalwan murmushi. Ba sai an fada ba duk wanda ya kalli idanunta yasan taci uban kuka duk kuwa da matukar kokarin datayi wajen share hawaye.
Har ta tafi? Ta tambayeni hannunta rungume a kirjinta.
Ta…. Tafi na fadi muryata na sarkewa.
Mukayi shiru babu wanda ya sake cewa kala har aka kira sallar isha. Sai lauriyya ta mike ta sakala jakarta akafada.
Hilal zan tafi gida… Na danyi shiru na farko saikuma nace Gida? Haka da wurwuri… Ta danyi tsaki sai gabana yafadi tunda nake da ita bata tabayin tsaki a gabana ba.
Banajin dadi ne… Shiyasa nake son tafiya yau da wuri muka dan sake shiru na tsawon lokaci.
Dan dakata to ina da sauran magana dake.. Ta hade fuska.
Maganar me kuma zakayi min na dauka mun gama komai tun dazu? Ga kayan ai acikin jakata. Ta nuna jakar da hannunta.
Duk lokacin daka shirya saika karba in kuma kana so ma yanzu sainaba ajiye ce agurina.
Akwai sauran magana lauriyya… A ina kika samosu? Naji ta rike numfashi cikin kaduwa.
Hilal me kake nufi da a ina na samo su kana nufin kace ni barauniya ce?
Dan girman Allah kada ki bata zancen nan lauriyya ni bahaka nake nufi ba. Ki tuna fa kyauta zakiyimin da kararki ta makudan kudi a iya sanina kuma ban taba ganinki dasu ba kinga kuwa ashe banida laifi danna tambaya.
Ta sunkuyar dakai cikin takaici. Tambayar ta kona mata rai ta daga kai.
Tunda ka dage saika san inda na samesu bari yo na fada ma MIJINA NE ya saya min su.
Mijinki? Ta gyada kai.
Kwarai kuwa baka san na taba aure ba kafin nazo nan garin ba? Nayi ajiyar zuciya.
Ina fatan yanzu ka gamsu. Lauriyya tace sannan ta matso daf dani kusa dani har takai ina iya jinhucinta akan fuskata.
ITACE TA BATA MAKA RAI ?
Na kalleta a rude.
Wa..wa kenan kike nufi? Lauriyya ta dafa kafadata tace.
Nasan daman kafi karfina Hilal na dade ina kwana ina tashi da fargabar cewa watarana sai anzo har ofishin nan an kwace min kai!
Gabana yafadi nayi sauri na dauke hannunta daga kan kafadata.
Lauriyya nataba fada miki kuwa wata kalma kwaya daya?
Wacce kalma ce wannan? Ga mamakina sai naji ina mai kunyar hada idanu da ita.
Adacan Lauriyya ban dauki amatsayin komai ba fiyeda kawai sakatariya na. Nayi sa’a danaga ta kura min idanu kamar zata hadiyeni.
Yau lauriyya na wayi gari duk fadin duniya babu wata ‘ya mace datafiki agurina. Lauriyya ta dada matsowa daf dani.
Na Gode Allah Hilal tun ranar dana dora idanuna akanka nake kaunarka.
Zan baki wani labari lauriyya ki saurareni da kunnen basira lauriyya ta dubeni dakyau. Labarin me kuma? Nakama hannunta muka wuce cikin ofishina. Wannan shine karo na farko dana taaba yi mata haka. Na zaunar da lauriyya akusa dani.
Lauriyya jiya da daddare wasu al’amura masu kama da shirin fim sun faru akaina. Abubuwan na da matukar rikirtarwa to ahaka dai ni gama yanke shawara azcuiayata cewa ni dai KE NA ZABA LAURIYYA.
Dan Amina Muhammadu.
Lauriyya tace tana tafa hannu. Ban fahimce ka ba hilal….. Me kake fadi ne kace ni ka zaba ban gane ba.
Me yiwuwa idan nabaki labarin ki fahimce ni ke dai saurara da kyau.
.
Nafara zubo mata labarin al’amarun kyautar jaririn da akayi min tun daga farko har zuwa kan zuwan fadila ofis.
Karfe tara saura kwata nagama bata labarin.
Lauriyya tayi shiru bata ko motsi kamar ruwa ya cinyeta ga mamakina akaro na farko sainaji da gama fada mata labarin damuwa zuciyata ta ragu.
Lauriyya ta mike tsaye tabar kusa dani sannan tafara safa da marwa….
[06:34, 1/31/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-24
.
(m)Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Lauriyya ta Mike tsaye tabar kusa dani sannan saita fara safa da marwa acikin ofishin akwai wani yanayi dake fuskanta daya hanani na katse mata hanzari don haka sainayi zamana ina jiran naji ta inda zata bullo inada kwarin gwiwar cewa indai har akwai mafita to lauriyya ce zata kawota na yarda da kwakwalwarta akan hakan.
.
Hilal! Nayi firgigit sa’ar danaji ta kira sunana.
Mecece shawarar Ki akai. Lauriyya ta dawo kusa dani ta zauna sannan tace
Zancen gaskiya Hilal indai kabar miliyan biyar ta wuce ka kayi shashanci. Na zabura cikin kaduwa.
Me kike nufi? Lauriyya tayi dariya miliyan biyar tafi karfin wasa Hilal Amatsayina na mai kaunarka bazan so ka rasa naira miliyan biyar saboda ni ba.
Tunanina ya kure na rasa abin da zance da ita.
Ni shawara ta ta Hilal kaje ka aure ta.
Lauriyya meke damunki ne ta girgiza kai.
Lafiya ta Kalau babu abin da ke damuna ni har kullum babu abin da ke faranta min rai irin cigaban ka
Da miliyan biyar kana iya wa duk Abokan hamayyar nisa.
Lauriyya kibar zancen nan tuni nagama fada miki in har akwai wacce zan aura yanzu a duniya to kece. Idan kuwa na Auri fadila bansan da idon zan Kalle ki ba ta daga kai muka hada idanu tace.
Ko?
Kwarai kuwa na Mike tsaye.
Ko sallah banyi ba yakamata naje nayi sallah lauriyya ta biyo ni Abaya.
Kayi tunani Hilal tunda dai sati daya suka baka amma ni ina ganin gara ka aure ta Hilal.
Ban juyo na kalleta ba sa’ar da take maganar domin na lura ita kanta akwai wani sirri datake kokarin boyewa daga gareni. Wata zuciyar ta ci gaba da yi min kururuwa. Duk kabi ka zama wawa Hilal haka kawai kabari matan zamani suna neman su zauta ka.
Daya kasan yadda take dayar kuwa baka ma san koda tarihin taba.
Zan tafi gida Hilal sai goben lauriyya tace.
Mamakin abin da yasa ta firgicewa haka take sauri sauri ta tafi gida.
Toh shikenan sai goben kenan. Ahaka muka rabu da lauriyya ta tsallake bakin titi tana sauri sauri na bita da kallo cikin mamaki meke faruwa ne? Yanzun nan fa take nuna tsananin kishin ta a gareni take nuna cewa duk duniya ni take kauna lokaci guda kuma tana cewa naje na Auri fadila… Tabbas akwai wani abu murdadde acikin al’amarin.. Bi a hankali dan samari kada ka bari matan zamani su haukata ka a banza nace da kaina….
.


.
Karfe tara da rabi agogon mota ta ya nuna nayi kokari tun sa’ar dana baro ofis na fitar da komai daga cikin zuciyata abunda nafi kauna yanzu a duniya shine isashshen barci domin rabona da barci sa’o’i kusan ashirin da hudu kenan.
Nayi fakin da motar a kofar gidana na rufe gilasan sannan na fito zan kulle kofar kenan sai Naji kamar motsi abayana na juya cikin sauri sainaga wata sura ta fito daga cikin duhu ta nufo inda nake.
Tun dazun nake jiran zuwan ka JARUMIN JARUMAI.
.
BAKWAI 7
.
Da wacce kuma kika zo? Na tambayi fadila lokaci guda kuma na jingina ajikin motar barcin dake idanuna ya zama tarihi a halin yanzu domin tuni nagama fahimtar fadila ta zama kamar tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba.
Nazo maka ne da wani babban labari domin dazun na fahimci wani gani gani kake yi min ka daukeni kamar wata yar iska fadila tace tana tabe baki.
Fadila abin har Yakai da bakaken maganganu.
Yama wuce da haka Hilal duk abin da nake yi ni ba mahaukaciya bace nasan abunda Nakeyi tayi shiru tana maida numfashi
Babana yayi min bayanin duk abubuwan da kuka tattauna dashi jiya banyi mamaki ba sa’ar da nazo ofishin ka naga kana neman ka wulakanta ni ashe tallata maka ni akayi.
Cool down fadila nace da ita rabi da turanci rabi hausa.
Anki ayi cool down din da asama nake ta ci gaba da huci agabana.
Ka dubi da kyau Hilal tun daga sama har kasa kaga makusa ajikina?
Maganganun ta sun fara bani haushi dan haka sainace.
Azahiri dai kam ko shakka babu baki da makusa amma a badini kuma fa…
Ta yamutse fuska.
Abar kaza cikin gashinta Hilal a kare wanne ne ba bare ba ku yanzu yan fim har kuna da bakin da zaku bude kuce wa wani dan iska? Kai yanzun nan Hilal kana tsammanin kai waliyi ne? Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim
[06:34, 1/31/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-25
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim?
Kada kice haka fadila ba duka aka taru aka zama daya ba.
Fadila ta zabura cikin fushi kamar zata hau ni da duka
Kasani Hilal na kasance daga cikin dubban yan matan da Allah ya jaraba da son karance karance da kallon Fina finan hausa wannan ne ma tasa duk inda akayi wani gangami na yan shirin fim sainaje gurin ba don komai ba sai kawai don na ganku Abin da baka sani ba shine ba dade da sanin ka abin da yasa ban taba tunkarar ka nayi ma magana ba shine girman kanka musamman ma a lokacin da kake kan ganiyar tashen ka….. Na katse ta.
Fadila duk naji kiyi hakuri don Allah kibar zancen nan mu rabu lafiya Wallahi barci ne a idanuna kamar na fadi nakeji. Tsaho lokaci tana nan tsaye tana ta kokarin dannan bakar zuciyar ta dake ingizota akan dokan danasani.
Dole ne na fada maka tarihina Hilal dole ne na fada maka.
Domin ka daukeni wata tambadaddiyar yar iska bayan kuma dan uwan ku ne dan shirin fim ya batani…… Bazan taba yafe masa ba har abada tafara kuka.
Aure Kam ko zan rasa miji a duniya bazan aure ka ba domin nasan har abada bazaka taba yarda dani ba.
Natafi Hilal ka huta lafiya…. Ta juya aguje ta nufi bayan gidan.
Na bita da gudu gudu adaidai lokacin da take kokarin shigewa mota.
Fadila….. Dan Allah tsaya ki saurare ni ta tsaya cak kafarta daya acikin motar daya kuma awaje.
Babu wani abu kuma da zakace dani Hilal…. Me kake son fada? Zancen naira miliyan biyar?
BAZAKA SAMI KO KWABO BA. tunda ka nuna min cewa kudin kafi so dani tayi tsaki agabana ta tsartar da yawu.
Dubi idanun ka kiri kiri babu tsoro babu kunya.
Kai yanzu har kana da bakin magana?
Aure ne bazan aure ka ba tuni nafadawa mahaifina dazun bayan nabaro ofishin ka….. Jeka ka tsira da mota matsiyaci.
Na yi taku biyu da niyyar kifa mata mari sai wata zuciyar tace dani..
Uhm. Uhm dan samari yi hankali da tangaran.
Fadila ta lura da niyya ta.
Au dukana zakayi? To Bismillah zo doki nayi tsaye kamar gunki duk kwakwalwata a yamutse.
.
Fadila ta shige motarta ta rufe kofar gararam sannan ta fizgi motar ta fice da gudu.
Jikina na rawa na nufi kofar dakina na lalubi dan makullin dakin dake aljihuna sannan nafara kokarin bude kofar sannan ne to wata takarda ta Fado daga jikin kwadon.
Na dubi takardar data Fado akan takalmina da farko na dauka shirme ce amma daga karshe sai zuciyata tace dani Kai duba dai…
INA shiga dakin saina lalubo makunnar lantarkin na kunna lokaci guda kuma na bude takardar dan Sako ne kamar haka…..
.
HILAL.
Me yiwuwa zaka so kasan wanda yayi min ciki zan fada Ma sunan sa domin abin yazama wa’azi a gareka ka kuma yi hankali kada abin da ya faru tsakanina dashi ya faru tsakanin ka da sakatariyar ka na lura ita tafi dacewa ka aura. Sannan wanda yayi min ciki sunan sa (ALHAJIJI)
FADILA.
.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button