ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA KAKAI COMPLETE HAUSA NOVEL

ALA QAQAI COMPLETE HAUSA NOVEL


.
Ban isa ofishina ba sai kusan karfe goma sha biyu na rana wannan ya samo asali ne sakamakon nannuyan barcin daya daukeni.
Ahanya sa’ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suka faru a gareni tun daren jiya. A lokacin ne toh………
.
ME KUMA YAKE SHIRIN FARUWA DA KAI HILAL ?
KA RASA MILIYAN BIYAR
KA RASA TSALELIYAR BUDURWA KAMAR FADILA
.
YANZU KUMA ME KAKE SHIRIN SAKE RASAWA?
[06:35, 1/31/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-26
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Ahanya sa’ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suke ta faruwa a gareni tun a daren jiya. Alokacin ne na yanke shawarar zuwa a ranar nasami mahaifin fadila mu gama kashe magana yanzu kam nagama saduda dacewa nayi sallama da zama miloniya tun da dai na tabbata fadila bazata aure ni ba.
Haka ma yafi kwanciyar hankali akalla ka tsira da mota dan samari.
Toh amma sa’ar da tunanin lauriyya ya Fado min duk sai Naji hankalina ya tashi bansan inane alkiblata ba. Abu daya dai dana dada tabbatarwa da zuciyata tun adaren jiya shine na share su baki daya daga cikin zuciyata domin ita kanta lauriyya na lura akwai wani abu na rashin gaskiya dake tattare da ita.
Ina kokarin fahimtar ko wanne abu ne har har na isa ofishin.
Nayi mamakin da ban ga lauriyya a kofar tana hange hangen ta inda zan bullo ba.
Nasan ga al’ada ko goma na safe nakai banzo ofis ba zan Harare ta tana ta leke leke to ballantana kuma karfe goma sha biyu cikin gaggawa nayi fakin da motar na nufi ofishin cikin sauri gabana ya fadi sa’ar dana shiga gurin karbar bakin banga lauriyya ba nayi tsaye cak a tsakiyar dakin jikina Yabani cewa lallai ba lafiya ba.
LAURIYYA. Nakira sunanta murya a sarkake shiru ta gaida kunnuwana to amma naji kamar motsin mutane acikin ofishina. Nayi taku biyu gaba da niyyar nashiga sai Naji motsin tafiya an nufo dakin saukar bakin.
Sannu ahankali naji takun sawu taf taf taf har ta bayyana idonta sharkaf da hawaye tana ganina saita taho gareni ta fashe da kuka.
Dan Allah Hilal ka yafe ni…. Ka yafe ni Hilal.
Ta sake fashewa da kuka.
Yi Shiru lauriyya menene kum? Kuma meke faruwa? Banyi mamakin jin muryata ko rawa batayi domin Daman tuni jikina Yabani cewa ba lafiya ba lauriyya taci gaba da kuka.
KA yafe ni Hilal yau zamu rabu dakai……
Bazan taba mantawa da abun dakayi min…. Ta sake fashewa da kuka iko sai Allah nace cikin zuciyata.
Wai me ke faruwa ne lauriyya kin ki ki fada min komai sai…….. Maganar ta makale a fatar bakina sakamakon wani kwakkwauran motsi danaji acan cikin ofishina.
Na juyo na dubi lauriyya nace.
SU wanene aciki? Ta dubeni a tsorace ta kasa cewa komai adaidai lokacin ne to sauran mutanen dake ofishin suka fito nayi tsaye ina duban su cikin kaduwa.
Mutanen su biyu ne daya namiji ne Kato mai doguwar kasumba yana sanye da shakwara da jamfa da wando na shudiyar shadda kai da ka ganshi kasan akwai kudi zai kai kimanin shekaru hamsin da biyu a duniya dayar kuma mace ce dattijuwa zatayi kimanin shekaru kusan hamsin. Kallo daya nayi nata na gane ta na fahimci ko wacece ita da lauriyya kamar an tsaga kara.
Sannunka da kokari bawan Allah.
Munji duk taimakon dakayi mata. Nayi saroro ina kallon su banida bakin magana matar taci gaba da cewa.
Yau shekara uku kenan muna neman yar banzar yarinyar nan…. Kwana uku ka da daura mata aure ta gudo.
Naji zuciyata ta harba akaro na farko saina kalli lauriyya nace…. KINA NUFIN KICE KINA DA AURE?
Lauriyya ta fashe da kuka sannan ta nuna katon mutumin da dan yatsa tace cikin kuka… Ka ga mijina nan……. Wai wannan katon za’a aura min katon mutumin ya kamo kafadarta ya hankadata waje tsohuwar da nake tsammani mahaifiyata ce tabi su Abaya.
.
Jikina na rawa na rufa musu baya tun kafin na karasa waje na hango wata mota daga can baya Kirar Toyota Coralla mutumin ya tura lauriyya aciki tana ta kuka tuni har yara sun fara taruwa suna kallon fim din. Cikin sauri na karasa gindin motar nace.
Lauriyya….. Allah ya kiyaye kinji Allah taimake ki katon mutumin ya Harare ni alamun tsana karara suka bayyana a fuskar sa ban zarge shi ba ban kuma ga laifinsa ba shekara ta uku tare da matar sa nasan duk duniya babu wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa.
Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa.. Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace.
Watarana zamu sake haduwa Hilal…. Nayi maka alkawari. Nagode Allah ya saka maka.
Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar lauriyya yace.
GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI YANZU BA SAYAR DA ITA NAYI BA KO?
Yana gama fadin haka sai ya sawa motar giya suka harba aguje.
Koda suka tafi sai cincirindon yaran dake kallon diramar suka rufa musu baya aguje suna shewa me yiwuwa da yake sun saba ganin jaruman shirin fim na taruwa agurin sun dauko ko wani sabon fim din aka shirya musu.
.
Kusan mintuna biyar ina nan tsaye sannan sai na juya na nufo cikin ofishina koda na shiga sai Naji shiru kamar makabarta zuciyata tayi kuna bakin ciki da takaici suka lullube Ni hakika rashin lauriyya kusa dani ba karamin rashi bane.
Ba’a dade ba sai Naji kafafuna duk sunyi rauni kamar bazasu iya daukata ba dan haka sai na nufi kujerar da lauriyya take zama a tunani wai ko zata dauke min kewa na zauna a kai ina zama sai Naji duk kasala ta lullube ni dan haka saina dauki kafafuna na dora su akan teburin sannan na lumshe idanuna na fara tunanin matsayina a yanzu.
TA LEKO TA KOMA. Nace da kaina babu Fadila na rasa lauriyya ga shi kuma nayi sallama da zama Miloniya.
Ina Nan zauna sai nafara kiyashin kudaden da ake Bina bashi. Cikin zuciyata a iya sanina ana Bina kudi kusan dubu dari shida da hamsin wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina.
Dole ne nasan duk yanda zanyi na biya su kudin su tun da dai wacce ke tarairayata da kwantar min da hankalin ma an dauke ta.
.
Daga inda nake zaune ina iya hangen sabuwar motar da mahaifin fadila Yabani tana sheki acikin rana nasan banida wani zabi daya wuce na sayar da motar na biya mutane basussukan su zuciyata tayi kuna tuni labari ya ya fara yada duniyar fim cewa na sake shigowa gari domin duk cikin JARUMAI maza babu mai shiga motar da takai tawa a yanzu dan haka sayar da ita ba karamar faduwa bace.
To amma banida zabi. Na lumshe idanuna sannan nace da kaina dan samari Hilal sayar da motar ka biya mutane bashin su ai zama lafiya yafi zama dan sarki ina yanke shawarar sai Naji nafara samun saukin rayuwa cikin zuciyata.
Naji wani dadi ya lullube ni sa’ar dana tuna da cewa motar zatayi tsada idan na sayar da ita dole ne na samu rarar kudin da zanci gaba da juyawa acikin harkar fim.
.
Can kuma sai wani tunani ya Fado min nan da nan na zabura ai kuwa da zan maida duk abubuwan da suka faru akaina tun daga daren shekaran jiya zuwa yau fim. Ba karamar karbuwa zanyi ba murna ta cika ni sai nafara tunanin sunan da ya kamata na sa masa. Sai kuma tunanin wahalar dana sha kafin na jefar da JARIRIN nan tafado min tabbas ALAKAKAI zan Sawa fim din
.
Kwarai kuwa cikin zumudi saina tuma kafata da karfi akan teburin sannan ne to naji wani abu ya Fado daga karkashin teburin. Cikin sauri saina sunkuya na dauka.
JAKA ne ya Fado.
Yawun bakina ya kafe zuciyata tafara harbawa cikin sauri a kwance a tsakar dakin jakar lauriyya ce data kawo min adaren jiya dauke da sarkokin nan masu tsada jikina na rawa na bude jakar.
Suna nan kamar yadda suke suna daukar idanu.
.
Lauriyya!! Nakira sunan ta cikin murna da farin ciki yanzu kam nasan bana bukatar saina sayar da motata dan biyan bashi.
.
Jikina na rawa na Mike tsaye ni kadai kamar mahaukaci nafara juya jakar dake kyalkyali a hannuna kawai sai Naji na fashe da dariya sannan Nace da kaina…
HILAL DAN DUNIYA ALLAH KE SON KA BA MUTANEN DUNIYAR FIM BA..
.
KARSHE…..
.
Nazir Adam Salih (NAS)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Leave a Reply

Back to top button