ALKALI NE Page 1 to 10

Tunda ya samu gidan nine na tsaya aka gyara komai. Bayan da aka gama sai yake tambayata aikin da nakeyi, shine nake fad’a masa ina ‘yar buga-buga ne dan bani da iyali, tunda nayi aure mata ta rasu wajen haihuwa acan garin mu shikenan na taho Lagos da zama saboda ban aje kowa ba.
Jin haka yace kawai hankalinsa ya kwanta dani, idan na amince zanyi masa gadi zai rik’a biya na, amma da sharad’in duk ranar daya kamani da cin amanarsa saiyasa an kulle ni. Jin abinda yace jiki na rawa na amince, domin na samu wajen zama mai kyau, da zakaga inda nake rayuwa ada zaka tausaya mani, bacci kawai yake kaini wajen, da nayi asuba zan fice, sai gashi Allah ya kawo mani Alhaji ya taimakeni, shiyasa nake zaune dashi da gaskiya, yana da dad’in zama sosai, sam beda mugunta, yana kyautata mani, kullum sai ya bani kud’in siyen abinci kuma k’arshen wata ya bani albashi, hatta da mukullin cikin gidan ina dashi, domin duk bayan kwana biyu ina shiga ina gyarawa, d’akinshi ne kawai banda mukullinshi, kalli d’akin da nake zaune yanzu.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in gaskiya ka godema Allah, kuma kacigaba da rik’e gaskiya arayuwar ka, domin itace tasa ka kawo matsayin da kake ayanzu, shiyasa ake so duk inda mutum yake ya kasance mai gaskiya. Sai dai baka fad’a mani sunanka ba.
Maigadi yace sunana *AMADU* amma anfi kirana da *MADU*. Malan Sani yace sannu Amadu suna mai dad’i. Fitowar Alhaji Mai Wada yasa sukayi saurin tashi.
K’arasowa yayi da sauri yana murmushi. Bayan sun gama gaisawa yace lallai Malan Sani kana da cika alk’awari, shiyasa nace bara na leko naga ko kazo nasan Madu bazai kirani ba zaiyi tunanin ko ban tashi ba. Malan Sani yace ai tunda nace zan zo bazan sab’a alk’awari ba, gashi nazo muna ta fira da Madu ma.
Alhaji yace bismilla kashigo. Kallon Madu yayi yana fad’in ina fatan dai ka karya? Madu yace ai tun d’azu naci k’osai da koko. Alhaji yace haka ake so, Malan Sani kashigo.
Bayan sun sake gaisawa Alhaji ya kawo masa shayi da kyar Malam Sani yasha. Kallonshi Alhaji Mai Wada yayi yana fad’in Malan Sani nasan zakayi mamakin kiran da nake maka, ba wani abu bane yasa nace kazo illa abinda na gani jiya, tunda na ganka kawai naji ka kwanta mani, hakan yasa naji ina so nasan kad’an daga cikin labarin ka, domin ajiya naga wasu mutane sun biyo ka da kyar kasha.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in Alhaji wannan labarin ko Mata ta ban fad’amawa ba, domin tana da tsohon ciki, hakika ina cikin damuwa, kuma naji na yarda da kai zan iya fad’a maka koni waye……
Bayan ya gama bashi labarin asalinsa ya d’ora da fad’in, nayi kusan shekara ina aiki da kamfanin yin Fanta, kuma har lokacin nine nake tuk’a motarsu, da farko ban fahimci komai ba, a hankali na fara gano wani abu da suke aikatawa a kamfanin, kuma manajen wajen shine yake da alhakin yin komai, wata rana bayan na tashi daga aiki har nayi masu sallama na tafi sai na manta na sayi biredi na had’a da lemun da ake bamu na aje a mota ban d’auko ba, hakan yasa nayi saurin komawa domin na d’auko.
Kasancewar kullum acan nake barin su Manaja da wasu daga cikin manyan yaranshi, sai su kai sha biyun dare basu tafi ba, ban tsaya bin ta wajen su ba kawai na wuce wajen mota domin na d’auki abinda na manta.
Muryar d’aya daga cikinsu naji yana fad’in akwai kayan da aka kawo masu daga wajen John d’azu, wai daga waje ya shigo dasu kuma lafiya lau aka dubasu a bakin ruwa kuma aka wuto dasu, domin ya saki kud’i sosai shiyasa Kwastam d’in wajen basu binciki kayan ba, yanda naji yana fad’i wasu maganin shaye-shaye ne irin na kwalba kamar dai maganin tari, to irinsu ne ya shigo dasu sai dai kwalinsu na lemu ne irin na waje, idan ba an bud’e ba baza’a tab’a sanin ba lemun bane aciki, yana fad’in zasu samu kud’i sosai da kayan.
Bayan ya gama fad’a masa sai naji Manaja yana fad’in ai sunyi magana da John zasu rik’a siyar da kayan ab’oye tunda kowa yasan harkar lemu sukeyi yan drugs bazasu saka idonsu akan kayan ba, yace zasu rik’a d’ora kayan had’e da katan d’in Fantar da muke d’auka muna kaiwa wajen da ake sara.
Jin wannan abun sai hankalina ya tashi, domin nasan zanyi aiki ne da haramtacciyar abu aciki, alokaci sai na kasa rik’e firgici na har suka jiyo motsi, ganin sun taho zasu duba yasa nayi saurin bud’e mota na d’auko leda ta na fito ina kok’arin b’oye damuwata na fad’a masu mantuwa nayi.
Ganin Manajan ya tsura mani ido yasa na d’an daburce, gashi dama Inyamuri ne, sai kawai ya matso kusa dani yana fad’in tun yaushe nake awajen? Ganin yanda hankalinsa ya tashi yasa nace zuwana kenan. Matsowa d’ayan yayi yana fad’in Manaja nima yanzu naji motsinshi da alama yanzu yazo.
Kallona yayi yana fad’in ka tabbata babu abinda kaji? Kai na d’aga mashi ina fad’in babu abinda naji dan hankalina yana wajen kayana. Kai ya jinjina yace zaka iya tafiya. Bayan tafiya ta bansan abinda suka tattauna ba, ni dai haka na isa gida jikina babu kwari, rayuwata ina tsoron cin dukiyar data fito da haramun acikinta, musamman ace kasan abinda ake kullawa amma kacigaba da aiki a haka, nasan kona je na fad’ama ‘yan drugs za’a iya samun masu karb’ar cin hanci a rufe maganar ni kuma na jawo ma kaina, hakan yasa na yanke shawarar barin aikin na nemi wani, duk da Matata tana da tsohon ciki amma naji aikin ya fitar mani, nasan yanda aiki yake da wahalar samu a Lagos, amma ya fiye mani na bar aikin da dai arik’a aikata b’arna dani kuma nasan komai.
A waccan shekaran jiyar ina zuwa wajen aiki na samu takarda daga wajen Manaja ta sallamar aiki wai na manyanta da yawa sunfi son Matasa, gaba d’aya kud’in da suka bani na sallamata dubu talatin ne, ganin haka yasa nayi hamdala ga Allah, ban nuna masu komai ba mukayi sallama dasu, haka naje na siyo komai na abinci, domin nafison na aje abinci da na rike kud’i ahannu na, nasan har Matata ta haihu bamu da matsalar abinci, kud’i ne dai bani dasu a hannu, domin acikin kud’in nayi biyan bashi dan nasan banda aiki bare nace sai na kwashi albashi kafin na biyasu, hakan yasa na biya duk mai bina bashi saura nayi cefanan gida.
Wallahi Alhaji ajiya da muka had’u bana maganin naira biyar a aljihu na, haka na bar gida ko kud’in cefane ban bayar ba, nasan dai akwai abinci shiyasa ban damu ba, sai gashi Allah yasa ka bani wad’an nan kud’in.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in to amma su waye suka biyoka jiya? Malan Sani yace wallahi ban san su ba, kawai ina zaune bayan na gama neman aikin yi na rasa sai na zauna bayan nayi sallar isha’i ina jiran wani Alhaji da naji ance yana neman direba, na dad’e a wajen ina jiranshi amma bai dawo ba, ganin dare yayi nace bara na tafi yau na koma kozan dace.
Kawai na taho sai had’uwa nayi da wasu Matasa suna kok’arin yin Lalata da wata yarinya sai ihu take yi, cikin azama nayi kansu ina kok’arin ceton ta, da kyar na kwaceta daga wajen su nasa ta gudu, ganin ta tafi yasa sukayo kaina d’auke da adduna, shine fa na gudo har Allah yasa muka had’u, sauki na d’aya akwai duhu babu wanda ya sheda fuskata bare naji tsoron sake had’uwa dasu. Kaji dalilin da yasa suka biyo ni.