ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

Jinjina kai Alhaji Mai Wada yayi yana fad’in lallai Malan Sani ka had’u da jarabawa,  tabbas kai mutumin kirki ne,  ba kowa ne namiji bane zaka samu wanda yake gudun tashin hankalin Iyalinsa ba,  kayi kok’ari daka iya b’oye mata halin da kake ciki,  kuma wannan abun da kayi shine akeson mutane surik’a aikatawa,  matuk’ar ka gano ana aikata haramtaccen abu a wajen da kake samun na abinci abinda zai fi maka kayi kok’arin barin wajen,  musamman idan kasan cewar ko ka fad’i gaskiya baza tayi aiki ba. 

Ina mai tabbatar maka da ace wad’annan mutanan sun gano cewar kaji su bazasu barka ba,  dole su nemi rayuwar ka domin gudun kada ka tona masu asiri,  da yawa yanzu ana aikata kasuwanci had’e da haramtacciyar harka,  tun zuwana garin nan na gano abubuwan da suke gudana,  kasan yanayin aikin mu, duk kayan da za’a shigo dasu hakkin mu ne mu tabbatar da nagartarsu kafin a wuce dasu,  kasancewar gaskiya tayi k’aranci yasa mutanan mu suke son karb’ar cin hanci,  domin mutane da yawa suna shigo da kaya ba bisa k’aida ba,  wannan dalilin ne yasa suke sakin kud’i ga masu matattar zuciya acikin mu domin su samu kayansu su fito lafiya,  tabbas k’asar mu bazata cigaba ba matuk’ar muna da irin wad’annan mutanen,  nasan ni d’aya bazan iya gyara su ba,  amma ga Allah na dogara,  kamar yanda nayi rantsuwa zanyi aikina bisa gaskiya da amana to bazan gajiya ba,  zanyi kok’ari wajen ganin na kare hakkin aikina,  naci ta hanyar halak d’ina,  kuma insha Allahu zanyi kok’ari wajen gano b’ara gurbi acikin yankina. 

Malan Sani yace hakika Alhaji kai d’in mai gaskiya ne,  tun bayan zuwanka na fara jin labarin ka,  duk da baka fara aikata komai ba amma naji wasu daga cikin manya sun fara tsoron kada ace kazo da wani abu daban ba kamar wanda ka canza ba,  domin sun riga sun saba dashi,  sam basu da  wata matsala tun alokacin tsohon shugaban kwastam,  tun lokacin da na fara jin magana akan ka nake tunanin ko dai Allah ya kawo mai gaskiya ne,  duk wanda kaji ana yawan magana akanshi to akwai wani abu na daban agareshi. 

Alhaji Mai Wada yace wannan haka yake,  hakika ina tsoron kaidin mutane,  wannan aikin da nake son tabbatarwa yana da matuk’ar had’ari,  domin duk wanda ya fito a zamanin nan yace yana son ya kauda b’arna to yasa aranshi zai iya mutuwa a kowane lokaci,  domin su dai masu aikata b’arnar bazasu so wani ya dakatar dasu ba,  domin  ayanzu mutane sunfi sha’awar aikata haramun akan aikin halak,  domin shed’an yariga ya gama da zuciyarsu,  ya nuna masu hanyar haramun tafi kawo kud’i,  shiyasa zaka iske kowa yanzu wannan hanyar yake bi sai dai fatan shiriya kawai. 

Ajiyar zuciya yayi ya kalli Malan Sani yana fad’in,  naji labarin ka Malan Sani,  kuma na yarda da kai sosai,  zuciyata ta aminta da kai har naji dad’i daka fad’a mani mutumin da yake neman direba baka sameshi ba,  ina ganin nine wanda Allah yayi ma zab’in ka shiyasa baka sameshi ba. 

Murmushi Malan Sani yayi domin yaji dad’in kalaman Alhaji Mai Wada,  saboda tunda yaji labarinsa yaji yana son kasancewa dashi. Kamar daga sama yaji Alhaji Mai Wada yana fad’in idan bazaka damu ba Malan Sani inason ka kasance direba na,  domin na yarda da kai,  na dad’e ina neman wanda zai rik’a tuk’ani amma tsoro yasa na kasa samu har yanzu,  kasan yanayin yanzu amana tayi k’aranci,  amma samun ka ayanzu yasa zuciyata ta aminta da kai. 

Hamdala Malan Sani yayi yana fad’in ina matuk’ar godiya Alhaji,  Allah maji rok’on bawansa,  cikin rufin asirinsa ya kawo mani mafita tun kafin mai d’akina tasan halin da nake ciki,  hakika naji dad’in samun wannan aikin,  domin Mai d’akina zata iya haihuwa a kowa ne hali,  ko yanzu akace ta haihu baza ayi gardama ba. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in babu komai Malan Sani,  abinda nake so kawai shine amana,  Allah ya had’ani da maigadi nagari,  na roki direba nagari gashi Allah ya bani,  babu abinda zanyima Allah sai godiya. Dan haka inaso ranar litinin kazo ka fara aiki,  kud’in albashinka ayanzu naira dubu talatin ne awata kafin zuwa gaba muga abinda za’a k’ara maka. 

Zaro ido Malan Sani yayi cike da farin ciki yake godiya,  kallon Alhaji yayi yana fad’in na rasa bakin magana,  ina d’aukar dubu sha biyar ada sai gashi yanzu Allah ya juya mani,  ina dab da samun zuri’a sai gashi Allah ya kawo mani cigaba,  nagode sosai Allah ya k’ara bud’i ya kuma bamu zaman lafiya. 

Alhaji zaiyi magana wayar Malan Sani tayi k’ara. Saurin d’auka yayi ganin sunan makwabcinsa ne. Bayan sun gaisa ya fad’a masa suna asibiti da matarsa tana nakuda shine matarsa tashiga ta fito da ita ya kaisu a motarsa. 

Saurin tashi yayi yana fad’in ganinan zuwa. Kallonshi Alhaji yayi yana fad’in ko haihuwar ce?  Kai Malan Sani ya d’aga jiki asanyaye. Tashi Alhaji yayi yana fad’in bara na d’auko mukullin mota mu tafi tare. Sakin baki Malan Sani yayi yana kallonshi jin irin karamcin da yayi masa. 

Yana tsaye har ya fito suka nufi waje. Hannu Malan Sani ya mik’a yana fad’in Alhaji kawo na tuk’a mu. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in haba yanzu ai baka cikin natsuwar ka,  ka bari na tuk’a mu. Madu ne ya k’araso yana tambayarsu lafiya?  Alhaji ne yayi masa bayani. Murmushi yayi yana masu fatan alkhairi. Haka suka fice Malan Sani sai addu’a yake Allah ya sauketa lafiya shima yaga kwanshi a duniya. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne,  naira 200  kacal, MTN Card a wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa,  idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.*

0⃣5⃣

 Tsaye suke a cikin asibitin, Malan Sani ya kasa zama duk yashiga damuwa,  tsoronshi d’aya kada ya rasa Matarsa,  gashi tun kafin suzo aka kawota tana nakuda har sunzo da kusan mintuna ashirin amma shiru. 

Alhaji Mai Wada ne ya dafashi yana fad’in addu’a zakayi mata Malan Sani,  wannan damuwar bazata amfanar da komai ba,  kai namiji ne ya kamata kasa dauriya aranka. 

Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in nagode Alhaji. Fitowar wata ma’akaciyar asibitin ne yasa sukayi saurin matsawa wajenta. Bakinta a washe take tambayarsu sune suka kawo Halima?  Da sauri Malan Sani ya amsa mata. 

Murmushi tayi tana fad’in Halima ta sauka lafiya Allah ya azurta ta da ‘Diya mace,  tasha wahala sakamakon dad’ewar da tayi bata haihu ba kuma gashi haihuwar faari,  wannan shine ya jawo mata doguwar nakuda amma yanzu suna lafiya. 

Hamdala Malan Sani yayi yana mata godiya. Murmushi tayi tace ai bakomai, yanzu ana gyara ta idan aka kaita d’akin hutu zaku iya ganin ta. Hannu Alhaji Mai Wada yasa a aljihu ya ciro kud’i masu yawa ya bata yana fad’in ga tukuicin ki. Amsa tayi tana masa godiya ta wuce tana fad’in idan kun gama kuje wajen likita akwai maganar da zakuyi. 

Bayan da aka maida Halima d’akin hutu Malan Sani yaja Alhaji Mai Wada suka nufi d’akin. Sai murmushi yake yana kallon matarsa. Alhaji kuwa yarinyar ya d’auka ya tsura mata ido domin Allah yayi mata kyau tun tana jaririyarta,  yana matuk’ar son mace amma Allah be bashi ba. 

Mika ma Malan Sani ita yayi yana fad’i kayi mata hud’u ba. Murmushi yayi yana fad’in Alhaji wannan yarinyar da namiji ne sunanka zan saka,  domin had’uwata da kai akwai alkhairi acikinta. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button