ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in bakomai a hakan ma nagode. Amsarta yayi nan take yayi mata hud’uba da *RUMAISA*, suna ne da Halima take matuk’ar so,  tasha fad’in duk ranar data haifi mace wannan sunan za’asa. 

Ajeta yayi akusa da Halima yana fad’in Allah ya amsa addu’arki ya baki mace kuma ansa mata sunan da kike so wato *RUMAISA.* Murmushi tayi tana duk’ar da kai dan kunyar Alhaji take ji. 

Tare da Alhaji suka fita yace ya mik’ashi wajen aiki sai ya dawo da motar saboda d’aukar matarsa da Rumaisa. Sosai wannan abun yayi ma Malan Sani dad’i,  haka yayi ta jera masa godiya kamar zaiyi kuka. 

Bayan ya kaishi Alhaji ya miko masa dubu goma yana fad’in ga wannan kasa a aljihun ka nasan zaka buk’ace su. Har k’asa Malan Sank yazo duk’awa da sauri Alhaji ya rik’osa yana fad’in daga yau kada ka sake yunkurin aikata hakan,  ni ba kowa bane dan haka ka d’aukeni tamkar d’an uwanka. 

Jinjina kai Malan Sani yayi yana goge hawayen farin ciki yayi masa godiya yana fad’in anjima zan dawo na d’auke ka. Alhaji yace kada ka damu zan hau motar haya ka aje motar a wajenka saboda zirga-zirga,  idan ka gama zuwa dare sai ka kawo mani. 

Rasa bakin magana Malan Sani yayi sai kawai ya fashe da kuka. Murmushi Alhaji yayi ya dafashi yana girgiza masa kai kafin ya shige ofis d’insa. 

Wannan abu da Alhaji yayi ma Malan Sani ba k’aramun dad’i yayi masa ba,  yanaji aransa duk duniya baya da kamar Alhaji ayanzu,  yasa aranshi zai iya bada ranshi akan Alhaji. Haka ya nufi kasuwa domin sayen abubuwan buk’ata kafin a sallame su. 

A ranar Malan Sani ya kira gidan su ya fad’a masu haihuwar,  sosai sukaji dad’i domin abinda kowa yake fata ne. Nan aka turo wata Gwoggonta da ‘Diyar Kawunta suka taho. 

Sai k’arfe d’aya kafin Malan Sani yaje amsar sallama. Anan likita yayi masa bayanin kada ya bari Halima ta sake d’aukar ciki yanzu saboda mahaifarta ta wahala akan wannan haihuwar,  idan samu ne su bari kamar nan da shekara biyar kafin ta sake d’aukar ciki. 

Malan Sani yace to mungode likita,  sai ku aunata domin abata abinda zaiyi dai-dai da jininta wanda zai hanata d’aukar cikin. Murmushi likita yayi yana fad’in ina son mutane irin ku masu saurin fahimta,  bara na had’aka da wata ma’aikaciyar mu itace take kula da wannan b’angaren,  Allah ya bada lafiya. Sallama Malan Sani yayi masa yana masa godiya. 

Haka suka tafi gida cike da farin ciki. Lokacin da suka isa har Jamila makwabciyarsu ta sauke ruwan wanka ta kammala girki. Sosai Halima taji dad’i,  dama irin abinda take gudu kenan ace ta haihu babu kowa nata,  sai gashi Allah ya bata makwabciya tagari. 

Sai dare Malan Sani ya maida ma Alhaji motarsa yana sake masa godiya. Alhaji Mai Wada yace haba bakomai,  zuwa gobe kazo akwai abinda zaka amsa. Malan Sani yace nagode Allah ya kaimu.

Sai tsakiyar dare Gwoggon Halima suka iso saboda basu taso da wuri ba,  Malan Sani ne yaje ya d’auko su. Halima baki yaki rufuwa yau ‘yan uwanta sunzo. 

Washe gari haka ‘yan barka sukayi ta shigowa wad’an da suke mutunci dasu kasancewar unguwar ba laifi akwai hausawa,  yaren ma akwai wad’an da suke mutunci. 

Sai da akayi azahar Malan Sani yaje gidan Alhaji dan baya so yaje ya tashesa. Malan Sani ya cika da mamakin kayan abinci da Alhaji ya bashi,  sannan ya kawo kud’in rago ya bashi hada na cefanan suna wanda zasu ishe sa ya saya ma Halima kayan fitar suna. 

Yana hawayen farin ciki yashiga yimasa godiya. Tare da Madu suka d’auki kayan a mota shima yaje ganin jaririya. Bayan ya ganta sukayi sallama Malan Sani ya nufi kasuwa domin ya siyo ma Halima kaya ya k’aro ma Rumaisa kaya duk da sun sayi wasu sai da lokacin basu san abinda zasu haifa ba hakan yasa suka sayi na jinsi d’aya wanda mace da namiji duk zasu iya sawa. 

****

Ranar litinin tunda wuri Malan Sani ya isa gidan Alhaji bayan daya gama aje masu komai na buk’ata. Zama yayi wajen Madu suka shiga fira kafin Alhaji ya fito. 

Alhaji yana fitowa ya cika da mamakin ganin Malan Sani ganin har yazo shida yake da hidima. Tasowa sukayi gaba d’aya suna gaishe shi. Alhaji yace lafiya lau,  Malan Sani ina masu jego?  Malan Sani yace suna lafiya. Alhaji yace ai da ka bari sai gobe ka fara zuwa. 

Malan Sani yace haba Alhaji nida ba mace ba,  na gama masu komai shiyasa na fito,  nima bazanji dad’in zama agidan ba,  nagode Allah da yasa na samu wannan aikin da yanzu haka zanyi ta gararan ba. Murmushi Alhaji yayi ya mik’a masa mukullin yana fad’in haka ne,  gashi muje. 

Sallama suka yima Madu suka tafi. Malan Sani yayi mamaki ganin Alhaji ya zauna agaba,  kasa daurewa yayi ya kalleshi yana fad’in Alhaji ai daka zauna a baya. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in hakan ma yayi nafi buk’atar na zauna agaba. Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in Alhaji kai na daban ne. Beyi magana ba yacigaba da duba wasu takardu.

Lokacin da suka isa ofis mutane sunyi mamaki ganin Alhaji Mai Wada tare da wani,  sai dai basuyi tunanin direba bane saboda sun ganshi agaban mota. 

Sai bayan da suka tsaya Malan Sani ya fito ya d’auko masa takardunsa yabi bayansa sukayi tunanin direba ne. Haka yayi ta gaisawa da mutanan wajen anan ya gabatar masu da Malan Sani amatsayin direbansa. Sunyi mamaki da jin haka domin sunyi tunanin acikin masu aikin wajen zai d’auki direba. 

Kai tsaye suka wuce ofis d’inshi,  bayan ya aje masa takardu Alhaji yace Malan sani zaka iya tafiya idan ina da buk’atar wani abu zanyi maka waya tunda kana da hidima. 

Risnawa Malan Sani yayi yana fad’in nagode,  mukullin motar ya d’ora masa saman teburi yana niyar barin ofis d’in. Sunanshi Alhaji yakira yana fad’in idan ka bar motar anan ai babu abinda zanyi da ita,  kawai ka tafi da ita kayi abinda ya dace. 

Dawowa yayi ya d’auki mukullin yana sake masa godiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in agaishe da Maijego. Fiya yayi yana murmushi yace zataji. 

Kwankwasa k’ofar akayi hakan yasa Alhaji ya bada izinin shigowa. Masinjansa ne yashigo yana gaishe sa. Alhaji yace *Malan Bala* katashi lafiya?  Nashigo ban ganka ba nazo da sabon direbana naso in had’aku amma ya tafi. 

Risnawa Malan Bala yayi yana gaishe shi kafin yace na zagaya baya ina d’auraye tsumman dana goge ofis d’in ne,  amma ai zai dawo ko?  Alhaji yace zai dawo yaje gida ne matarsa ce ta haihu. 

Malan Bala yace masha Allah,  Allah ya raya,  gaskiya naji dad’i daka samu direba,  domin wasu suna tunanin baka son ka d’auki direba saboda karik’a cinye kud’in da ake fidda masu. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in hada kai acikin masu fad’in haka kenan?  Zaro ido Malan Bala yayi yana fad’in haba dai Alhaji,  kaima zaka mani shedar kirki ai,  wallahi ko d’aya bana maka mugun zato,  domin tun bayan zuwanka nan rayuwata ta canza,  mezaisa na shiga cikin masu zagin ka?  Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in wasa nake ma Malan Bala,  kada ka damu da duk abinda mutane zasu fad’a akaina,  domin idan kana biye ta mutane bazaka tab’a yin gaba ba,  kai dai kasa Allah aranka. 

Malan Bala yace insha Allahu.  A had’o maka shayin ne?  Alhaji yace sai zuwa anjima nasha agida. Risnawa yayi yana fad’in ahuta lafiya. Yana kok’arin fita sai ga mataimakin Alhaji yashigo ofis d’in,  gaishe sa Malan Bala yayi kafin ya fita. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button