ALKALI NE Page 1 to 10

Hannu Adebayo ya mik’a ma Alhaji yana fad’in barka da safiya Sir, murmushi Alhaji yayi yana fad’in yauwa Mr. Adebayo ka tashi lafiya? Cikin harshen turanci ya maida mashi da lafiya lau, saboda Adebayo yafi son magana da turanci duk da yana jin hausa sosai, amma saboda bata zauna abakinsa ba yasa yafison yayi magana da turanci koda kuwa abokin maganarsa da hausa yake masa magana saboda yana jin hausa maidawarce take masa wahala.
Zama yayi yana mik’a ma Alhaji wata takarda yana fad’in *Alhaji Marusa* babban mutumin nan mai shigo da kayan na’urori da sauran kayan masarufi na k’asar waje shine ya aiko da wannan takardar akan yana son sa hannunka saboda yana samun matsala da ma’aikatan mu akan kayansa, duk da kowa yasanshi yasan matsayinsa amma ana samun wasu daga cikin ma’aikatan mu suna rik’e masa kaya, wani lokacin kuma suna bincikar masa kaya suna b’ata masa lokaci har hakan ya kan jawo masa asara, kafin zuwanka Oga ne ya tsaya masa, domin kowa yasan irin matsayin daya taka ak’asar nan, to bayan tafiyar Oga sai ya fara samun matsala da mutane, duk da akwai wad’an da suke kular masa da kayanshi amma wannan karon sai da ya kira Oga yayi masa magana, shine ma Oga yakirani akan nazo kasa hannu domin ya zama sheda akan duk wasu kaya da za’a shigo dasu nashi ba sai an bincike su ba tunda ansan abinda yake shigowa dasu.
Tunda ya fara magana Alhaji ya had’e hannu ya jingina da kujera yana kallonshi murmushi kwance a fuskarsa. Jin Alhaji yayi shiru bece komai ba yasa Adebayo yacigaba da fad’in Alhaji akwai babbar sallamar da muke samu daga Alhaji Marusa, sam beda rowa, yasan yanda muke masa mutunci shiyasa yake sakar mana kud’i, kuma munyi bincike babu abinda yake shigowa dashi wanda ya sab’a doka hakan yasa muka aminta dashi.
Wannan karon k’aramar dariya Alhaji yayi ya gyara zamanshi yana fad’in Mr. Adebayo taya kasan cewar baya shigo da kayan da suka karya doka? Saurin kallon Alhaji Adebayo yayi yana motsa baki. Takardar Alhaji ya amsa yana fad’in idan har zamu iya sa hannu akan wasu surik’a shigo da kaya ba tare da an bincike su ba ina ganin babu amfanin gwamnati ta ajemu tana biyan mu anan, idan muka kyale wasu wad’an da muke kamawa kuma su basu da hakki akan mu? Mr. Adebayo ina so ka fahimci wani abu guda, duk abubuwan da suke faruwa ak’asar nan mune muke haifar dasu, idan muka rik’e aikin mu babu yanda za’ayi arik’a shigo mana da haramtattun kaya a k’asar mu, kana ganin k’asashen da suka cigaba sai dai ashigo da kaya marasa kyau ta b’arauniyar hanya, domin ma’aikatansu sun rike gaskiya, mu kuma sai muka banzatar da aikin mu muka rik’a barin ana shigo mana da kaya ta hanyar daya kamata ace mun tsare ta, sam masu aikata hakan basu da damuwar bin b’arauniyar hanya domin sun san mud’in kwad’ayayyu ne, da sun watsa mana tsaba sai mu saki hanya mu koma muna tsintar abinda suka watsa, su kuma sai su koma suna abinda suka ga dama, duk abubuwan da suke faruwa anan babu wanda ban sani ba, wasu tun kafin nazo wajen nan nake da masaniya akan su, wasu kuma bayan zuwa na na karance su, wannan dalilin ne yasa tunda nazo bance komai akan aiki ba, na zuba ido domin na gama karantar kowa, kuma daga yau ne aikina zai fara, wannan dalilin ne yasa na cireka daga bakin boarder domin ba aikin daya kamata kayi ba kakeyi.
Wata takarda ya d’auko yana fad’in wannan sune sabon tsarin dana kawo, kuma yanzu nake jiran kashigo na fad’a maka k’arfe goma akwai taro domin kowa yaji sabon tsari, sai kuma gashi kazo mani da wannan maganar, dan haka ka fad’ama sauran ma’aikata sakona, ina fatan ka fahimce ni? Kai Adebayo ya jinjina zuciyarsa tana masa zafi, dama shi tunda Alhaji Mai Wada yazo haka kawai yaji baya sonshi, shiyasa yafi son akawo masu yaran su sunfi jin dad’in aiki dasu, amma idan aka kawo bahaushe musulmi da wuya ya basu goyon baya musamman idan mutumin bashida had’ama.
Tashi yayi ya d’auki takardar da ya bama Alhaji yana fad’in shikenan zan koma ofis sai zuwa anjiman. Murmushi Alhaji yayi yana d’aga masa kai. Haka ya fita cike da jin haushi. Murmushi kawai Alhaji yayi yacigaba da aikin da yake gabansa.
***
Cike d’akin taron yake da ma’aikatan wajen tun daga masu gadi, masinjoji har zuwa manyan ma’aikata. Bayan an bud’e taro da addu’a Alhaji Mai Wada ya bama Adebayo izinin yayi ma sauran ‘yan uwansa jagoranci suyi tasu addu’ar. Bayan sun gama Alhaji ya bama Adebayo takardar yace yarik’a karantowa sai shi yayi bayani.
Zuciyar Adebayo a cunkushe ya mik’e, sai dai da yake d’an duniya ne babu wanda zai iya fassara abinda yake a fuskarsa. Haka ya fara karanto sabon tsarin Alhaji yana bayani d’aya bayan d’aya.
Gaba d’aya wajen kowa yayi shiru, masu jin dad’i sunayi masu jin haushi sunayi. Bayanin da Alhaji yayi na k’arshe yafi d’aga ma wasu hankali, musamman masu aikata irin laifin.
Kallon mutanan wajen Alhaji Mai Wada yayi yana fad’in wannan dokar itace doka ta k’arshe acikin jerin dokokin dana rubuta, shiyasa na barta a k’arshe domin ba abu bane na wasa.
Kamar yanda na fad’a zan sake maimaitawa, duk wanda aka kama da laifin karb’ar cin hanci daga wajen masu kaya za’a dakatar dashi har na wata ukku ba tare da albashi ba, idan aka maidoshi ya sake aikata hakan to kora ce, ba haka dokar take ba, nine na sassautata domin bana fatan na zamo wanda zaiyi silar korar wani daga wajen nan, domin bazanji dad’i ace nine silar katse mashi hanyar abincinsa ba, amma abinda nakeso daku shine ku daure ku bani had’in kai domin mu gyara tare, kowa yasan yanda yankin mu na nan garin Lagos yayi suna, domin mune manya, inaso na kawo cigaba, ba dole sai mun amshi cin hanci zamu samu kud’i ba, akwai mutanan da suke bada kyauta saboda kawai an tsare masu kaya sun sauka lafiya, dan haka kowa yayi kok’arin kiyayewa, insha Allahu zaku sameni mai adalci agare ku.
Sai magana ta biyu, kowa ya tsaya a inda aka ajeshi, duk wanda kayansa suka iso zamu tsaya muyi binciken daya kamata kafin mu badasu, babu wani dalili da zaisa ace baza’a binciki kayan wani ba, komin matsayinsa, komin ikonsa matuk’ar kayansa suka iso dole a tabbatar da ingancinsu kafin a sake su, duk wanda muka kama da wannan laifin zai fuskanci hukunci, ku daure ku tsaya a binciki kaya, gara su dad’e ba’a sake su ba da muyi sauri mu saki kaya bayan akwai haramtattu aciki.
Wannan shine iya sabon tsarin dana kawo, ina fatan kowa zai fahimceni, nasan wasu zasuji haushi, dama haka abun yake, dole sai anyi b’arna kafin ayi gyara, kuma sai an daure kafin a tsaida gaskiya, dan haka wanda beji dad’in wannan sabon tsarin ba ina mai bashi hak’uri haka aikin kwastam yake.
Gaba d’aya wajen ya d’auki tafi, masu jin haushi ma haka suka daure suka tafa masa, Adebayo bazaka tab’a gane yanayin da yake ciki ba. Haka taro ya tashi kowa ya koma wajen aikinsa.
Tsaye Adebayo da Umar suke a jikin mota, gaba d’aya fuskar Adebayo ta canza kala daga fari zuwa ja, zuk’ar sigari kawai yake kamar wanda zai hadi’ye bakinsa saboda b’acin rai.
Dafashi Umar yayi cikin harshen hausa yake fad’in haba abokina kadena damun kanka akan wannan abun, kada kamanta an kawo wad’an da suka fishi tsanani ma amma cikin ruwan sanyi manyan k’asar suka sa aka canza masu wajen aiki, kasan dai wajen aikin mu babba ne, duk wani maiji da kud’i bazai so ace an kawo wanda zai rik’a bincikar kayansa ba, hakan yasa ba’a barin irin su Alhaji su dad’e anan, to ka kwantar da hankalin ka, babu wanda ya isa yazo ya kawo mana wani sabon tsari, yanda muka saba facaka da kud’i taya za’a zo lokaci guda akawo mana wani tsarin banza, kuyi magana da Alhaji Marusa koshi kad’ai ya isa yasa acanza masa wajen aiki.