ALKALI NE Page 1 to 10

K’arasa zuk’e sigarinshi yayi kafin ya fara magana cikin harshen turanci”Haba Omar kaima kasan hankalina bazai tab’a kwanciya ba matuk’ar wannan mutumin yana wajen nan, gobe ne kayan Alhaji Marusa zasu iso, kuma kaima kasan akwai abinda za’a sako aciki, gashi wannan Alhajin ya kawo wannan dokar, ya kake tunanin idan ya kama wani abu acikin kayan? Gaskiya akwai matsala, zan kira Alhaji na fad’a masa kada kayan nan su taho gobe, ya jira zuwa nan da kwana biyu kafin su taho.
Jinjina kai Umar yayi yana fad’in haka ne, kawai ka kirashi yanzu. Waya Adebayo ya ciro ya kira Alhaji Marusa, bayan ya d’aga Adebayo yace masa kada kayan nan su taho gobe. Alhaji Marusa yace yanzu nake da niyar kiran ka ai, d’azu muka gama magana da mutanan sunce cikin daren yau kayan zasu iso Lagos, kasan akwai kaya masu muhimmanci da tsada aciki, shiyasa nace zan kiraka naji ko Alhaji Mai Wada yasa hannu a wannan takardar? Adebayo yace akwai matsala fa Alhaji, komai ya b’aci, sabon tsari ya fito, wannan mutumin yazo da sabon tsari, yaki saka hannu a takardar, kuma yace dole a binciki kayan kowa, ina tsoron kada ace ya tsaya da dare idan ya samu labarin kaya zasu iso.
Cike da tashin hankali Alhaji Marusa yace mene? Haba Adebayo, ya zakayi mani haka, kai da nace kayi kok’ari cikin dabara ka shawo mani kansa sai ka fad’a mani bai amince ba, yanzu gashi kaya sun taho, dole nasan abunyi. Umar ne ya amshi wayar yana fad’in Alhaji kawai kayi waya daga can sama kasa ayi kiranshi da dare, idan yaje sai su rik’eshi da magana har kayan su iso idan yaso sai acire abinda ya kamata abar sauran zuwa safiya idan yazo sai yasa hannu a amshi kayan.
Shiru Alhaji Marusa yayi kafin yace maganar ka abun dubawa ce, ka kyaleshi bai isa ya sani cikin tashin hankali ba, zanyi magana da Mr. Kallah.
Kashe wayar yayi yana fad’in ai na fad’a maka Alhaji Marusa bazai bari yayi asara ba. Ajiyar zuciya Adebayo yayi yana fad’in dole ma mutumin nan ya bar wajen nan.
***
Bayan sallar magriba Alhaji Mai Wada ya samu sakon kayan Alhaji Marusa da suka taso. Bayan ya gama aikinsa saiga waya daga Mr. kallah akan yana nemansa k’arfe tara na dare. Cike da girmamawa Alhaji yace zai zo. Yana aje wayar yayi murmushi, tabbas hasashensa yayi dai-dai, dama irin wannan ranar yake jira. Dirowa ya jawo ya d’auko wani abu ya tashi yabar ofis d’in aranshi yana fad’in zanyi maganin ku.
Share this
[ad_2]