ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

Alhaji Kabir ya fito gaban kotu. 

Brr. Ra’eez… Kotu zata so tasan alak’ar ka da Marigayi. 

Alh. Kabir… E to,  kowa dai yasan Alhaji bai da amini daya wuce ni,  atare muka taso,  abotar mu ta wuce abota ta koma ta ‘yan uwantaka,  sirrina na Alhaji ne,  haka shima nashi nawa ne,  babu abinda muke b’oyema juna. 

Brr. Ra’eez…. A tsawon zamanka dashi ko ya tab’a fad’a maka yana da matsalar rashin haihuwa? 

Brr. Bajinta… Ina da ja ya mai shari’a,  be kamata  Brr. Ra’eez ya maido mana da hannun agogo baya ba,  kowa yasan munyi nisa a wannan shari’ar,  dan yazo daga baya bai kamata ya maido da komai farko ba. 

Alkali… K’orafi bai karb’u ba,  Brr. Ra’eez yana da ikon sako wannan shari’a daga farko matuk’ar yana da tabbacin ya kawo hujjojin da zasu gamsar da kotu. 

Brr. Ra’eez.. Murmushi yayi yana fad’in nagode ya mai shari’a. Ina jinka Alhaji. 

Alh. Kabir… Gaskiya tunda muke da Alhaji be tab’a fad’a mani yana da matsalar rashin haihuwa ba,  asali ma duk lokacin da zaije wajen duba lafiyarsa tare muke zuwa,  duk lokacin daya tashi zuwa asibiti baya yarda ya tafi da direba,  ko bana gari yana hak’ura har na dawo domin muje tare,  abu d’aya na sani shine yana fama da damuwa akan rashin haihuwa da Allah be basa ba,  wannan dalilin ne yasa shi aure har mata ukku,  domin munsha zuwa wajen likitoci daban -daban suna tabbatar mana lafiyarsa kalau kawai lokaci ne beyi ba,  wannan dalilin ne yasa na bashi shawarar ya k’ara aure kila adace,  sai gashi har Allah yayi masa rasuwa bai samu haihuwa ba,  a daren ranar da zai rasu bana gari ina hanyar dawowa ya kirani,  tabbas alokacin muryarsa cike take da  farin ciki,  duk da yana cikin hali na rashin lafiya hakan bai hana farin cikinsa bayyana ba,  bayan mungaisa nake tambayarsa dalilin farin cikinsa,  jin hayaniya ya gane ina tafiya hakan yasa ya kashe wayar yana fad’in idan na sauka zamuyi waya,  bamuyi wayar ba har Allah ya d’auki ransa. 

Brr. Ra’eez… Jinjina kai yayi yana fad’in mungode zaka iya tafiya. Juyowa yayi yana fad’in ina so nayima Hajiya Binta uwar gida ga marigayi tambaya. Hajiya Binta ta fito gaban kotu. 

Brr. Ra’eez…. Hajiya ko kin tab’a zuwa asibiti aka gwadaki domin a tabbatar da lafiyar ki? 

Hajiya Binta… Kwarai kuwa,  ni da Alhaji munsha zuwa asibitin nan garin har ma da k’asar waje,  duk inda mukaje amsar d’aya ce,  matsalar tana wajen Alhaji,  sun tabbatar mana bazai tab’a haihuwa ba,  alokacin yaso mu rabu amma nace masa ban yarda ba,  aurena dashi na saurayi da budurwa ne,  ban damu da haihuwa ba matuk’ar muna tare dashi,  alokacin na fad’a masa kada ya yarda da maganar likitoci domin ba maganar Allah bace,  nice nayi ta bashi kwarin guiwa akan yayi aure kila adace,  nayi mamaki da Alhaji Kabir yace wai sunje asibiti ance lafiyarsa kalau,  kuma so da yawa Alhaji yana zuwa asibiti shida direba,  dan haka maganar Alhaji Kabir ba gaskiya bace. 

Brr. Ra’eez. Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima likitan daya tabbatar da awon cikin Amina tambayoyi. Likita ya fito gaban kotu. 

Brr. Ra’eez…. Kai ne likitan Alhaji ko? 

Likita… E nine. 

Brr. Ra’eez.. Amatsayin ka na likitanshi ya akayi baka tab’a fad’a mashi bazai iya haihuwa ba tun yana da ranshi sai bayan mutuwarsa ne kayi rubutu sannan ka kawo kotu? Sannan ya akayi alokacin da ka auna Amina iya cikin kawai ka gani baka gano komai ba? 

Likita… Hannu yasa yana goge zufar data zubo mashi kafin ya furta,  iya abinda aka umarceni na auna kenan a kotu,  kuma dana auna na kawo sakamakon a kotu. Maganar Alhaji kuma kasan ana son a b’oye sharri a bayyana alkhairi,  Alhaji ya manyanta,  bazaiji dad’i yaji cewar bazai tab’a haihuwa ba,  yana matuk’ar son haihuwa har hakan ya jawo yayi aure har so ukku,  ganin haka yasa na kasa fad’a mashi gaskiya har sai da buk’atar hakan ta taso a kotu. 

Brr. Ra’eez… Amma gashi Babban aminin Alhaji ya tabbatar da sunje asibiti an tabbatar da lafiyarsa kalau. 

Likita… E to,  ai kasan ko wane likita da yanayin aikinsa,  kowa yasan yanda muka dad’e da Alhaji,  kuma Alhaji ya yarda da aikina,  to bazanyi mamaki ba dan wani likitan yace lafiyar Alhaji kalau ba,  domin koni abinda na fad’a masa kenan,  kasan mu likitoci masu ceto ne,  muna iya b’oye gaskiya domin farin cikin marar lafiyar mu,  wannan dalilin ne yasa na b’oye masa gaskiya. 

Brr. Ra’eez… Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari’a zan so nayima *IYA* mai aikin gidan Alhaji wasu tambayoyi. 

A firgice Hajiya Binta  ta mik’e tana fad’in ya mai shari’a Iya ta dad’e da barin gidan mu,  tun kafin ya rasu muka nemeta muka rasa acikin gidan wai bazata iya cigaba da aiki agidan ba,  yau kusan wata bakwai kenan da barin ta gidan. 

Bubbuga tebur Alkali yayi yana fad’in ki kama bakin ki nan kotu ce ba kasuwa ba,  dan haka kada ki sake magana idan ba kiranki akayi ba. Zama Hajiya Binta tayi tana goge zufa,  kallon kishiryata Zainab kawai take,  ita kuma ta kasa fahimtar halin da Hajiyar tashiga dan ankira Iya bayan tasan babu abinda ta sani Iyar tayi. 

Brr. Ra’eez…. Iya ko zaki fad’ama kotu tsawon shekarun da kikayi agidan marigayi kina aiki? 

Iya…. Gaskiya na dad’e ina aiki agidan Alhaji,  tun bayan da Hajiya Binta ta cika shekara d’aya agidanshi tasa k’awarta ta samo mata mai aiki amma tafison Babbar mace,  kuma bata son ‘yar birni ta fison wacce za’a nemo a kauye,  hakan yasa k’awarta taje har k’auyen mu da yake katsina wato ‘Danja ta samo ni,  tun daga lokacin na fara aiki agidan,  sosai Hajiya take mani kirki,  na d’auketa ‘yar uwa,  duk da na girmeta amma haka nake bauta mata,  itama kuma tana bani hakki na sosai. 

Brr. Ra’eez… Amma ya akayi aka wayi gari ba’a sameki agidan ba? 

Iya…. Hannu tasa tana goge hawayen da suka zubo mata,  kafin tace tabbas na cutar da Amina da Alhaji,  nayi kuka wanda beda amfani,  naso na nemi yafiyar Alhaji amma Allah be bani iko ba,  abu d’aya nasan nayi mashi wanda idan na tunashi nake jin sauki. Kamar yanda na fad’a maka aiki nake ma Hajiya Binta,  bayan shekara ukku sai Alhaji ya sake aure,  sosai hankalin Hajiya Binta ya tashi,  domin likita ya tabbatar mata bazata iya haihuwa ba,  alokacin atare mukaje da ita,  domin Hajiya ta aminta dani,  lokacin da ta fad’a mani abinda likita ya fad’a sai tace na rufe maganar bata so kowa yaji. Bayan da aka kawo amarya Hajiya Zainab sai tazo ba kamar yanda mukayi zato ba,  ta kasance mace mai kwantar da kai awajen Hajiya Binta,  ganin haka sai Hajiya Binta taji dad’i.  K’awarta ce ta kawo shawarar kada ta bari Zainab ta haihu agidan,  hakan yasa mukaje wajen wani k’asurgumin Boka ya bada maganin hana d’aukar ciki. 

Bayan da muka dawo na rik’a zubama Zainab magani a abinci tana ci,  kuma Allah ya taimaka bata d’auki cikin ba. Bayan shekara biyu da aurenta Alhaji ya sake aure inda ya auri Amina,  itama mace ce mai hakuri da kwantar da kai,  hakan yasa Hajiya Binta taji dad’in zuwanta,  anan itama mukayi kokarin bata magani a cikin abinci. 

Jin shiru bata d’auki ciki ba yasa hankalin mu ya kwanta,  sai dai abinda bamu sani ba ashe ciki ya shiga jikin Amina,  nice na fara sanin tana da ciki,  a hankali da wayau da dabara irin tamu ta manya na tambayeta rabon data ga al’adarta,  a yanda tayi mani bayani yasa na gano cikin watanshi d’aya da kwanaki,  anan nayi mata dabara nace kada ta fad’ama Alhaji zaiga rashin kunyarta,  ta bari na fad’ama Hajiya Binta ita zata masa albishir hakan zaisa yafi ganin darajarta. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button