ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

A ranar muka koma wajen Boka,  anan ya bamu maganin da za’a rufe mata baki bazata fad’ama kowa tana da ciki ba,  zata manta da wani ciki ma ajikinta,  sannan Boka ya bamu maganin zubar da cikin,  sai Hajiya tace tana tsoron yaki fita,  gara dai a kwantar dashi zata san abinyi. Anan Boka yayi mana aiki muka dawo gida. 

Tun daga ranar maganar cikin Amina tasha ruwa,  bata sake maganar ba,  har gwada ta nayi amma ta nuna ita bata san da maganar ba bata da wani ciki. Muna cikin haka Hajiya Binta ta samo maganin da zai kwantar da Alhaji ta bani na zuba mashi a abinci,  tunda yaci bai sake lafiya ba. 

Wata rana na dawo daga cikin gari kai tsaye na wuce d’akin Hajiya Binta,  abinda naji ya firgitani,  magana suke da k’awarta akan ta kashe ni,  domin ita bata yarda da kowa ba,  tunda ina da son kud’i wata rana zan iya juya mata baya idan na samu wasu kud’in. Nan take ta amince akan washe gari zata kashe ni,  sannan Alhaji yana mutuwa zata koma wajen Boka ya tashi cikin domin ta jama Amina sharri kuma aki amincewa da cikin jikinta,  ita kuma Zainab zata nuna mata soyayya domin ta bata dama su kwarema Amina baya,  idan komai ya kammala itama tasa akasheta sai taci dukiyar ita kad’ai. 

Cike da firgici Hajiya Binta ta mike tana fad’in wallahi k’arya take,  Zainab kada ki yarda da abinda tace makirar tsohuwa ce. Bubbuga tebur Alkali ya buga hakan yasa ta natsu. Kallon tuhum kawai Zainab take binta dashi. 

Brr. Ra’eez… Iya cigaba da bayaninki muna sauraron ki. 

Iya… Aranar hankalina ya tashi,  cikin sand’a na shige d’akina na had’a kayana na bar gidan,  ko mai gadi be ganni ba dan yashiga sallah,  kafin na bar garin sai da na samu wani yaro da nake mutunci dashi na sashi ya rubuta mani wasik’a,  anan na sheda ma Alhaji Amina tana da ciki,  alokacin zai kai wata biyu,  ban iya fad’ama Yaron komai ba dan bana son ya gano ni,  kawai nace masa ina jin kunyar Alhaji nafiso ya karanta a rubuce. 

Bayan ya gama nace ya taimaka muje ya bama maigadi kuma ya tabbatar mashi Alhaji zai bamawa. Ina tsaye har Yaron ya bama Mai gadi takardar,  bayan ya dawo ya fad’a mani Mai gadin yace zai bama Alhaji duk da baya fitowa amma zaiyi kok’arin kai mashi. 

Godiya nayi mashi na bashi kud’i na bar garin,  a ranar cikin dare na isa Funtua,  a tasha na kwana sai washe gari na isa kauyen mu,  ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai lokacin da kaje gidana,  nayi mamakin ganinka da bayanin da kazo mani dashi,  nayi kukan mutuwar Alhaji domin hada ni aka kashe shi,  naso na nemi yafiyarsa babu dama saboda banyi ilimin boko ba dana rubuta mashi a wannan wasikar,  zuwanka yasa naji kwarin guiwa kuma na amince zanzo na bada sheda akan abinda na sani domin duniyar ta juya mani baya.

Brr. Ra’eez… Zaki iya tafiya mungode. Ya mai shari’a iya kar mutanan da zanyi ma tambaya kenan,  wannan takarda ce dana samu a d’akin marigayi alokacin da mukaje gidan bincike nida ‘Dan sandan da yayi mani jagora. 

Takarda ce mai d’auke da rubutun Marigayi tare da sa hannunshi,  tun daga ranar daya samu labarin cikin Amina ya rubuta kwanan watan,  ya nuna farin cikinsa,  har yayi fatan Allah ya tashi kafad’arsa domin yaga jininshi,  atare da takardar da Iya ta aika masa ya had’esu ya b’oye a cikin dirowarsa,  Allah ne ya bani ikon ganinta,  domin gaba d’aya takardun dirowar an kwashe su,  itama daga k’asan dirowar akwai wajen da yake b’oye abubuwan sirrinsa anan ya aje ta. 

Mik’ama Magatakarda yayi yana fad’in ya mai shari’a,  iya abinda zan fad’a kenan,  ina rokon wannan kotu mai alfarma data yanke hukunci ga mutanan da suka zalunci Amina da Marigayi,  sannan ta hukunta Likita daya goyi bayan k’arya. Nagode ya Mai shari’a. 

Gaba d’aya kotun ta d’auki hayaniya,  mutane da yawa Brr. Ra’eez ya burge su,  acikin sati d’aya ya gano gaskiya,  abinda akayi wata anayi sai gashi acikin sati guda ya gama komai. 

Bayan da kowa ya natsu Alkali ya d’ago yana fad’in kotu tana son ganin Hajiya Binta,  Iya da Likita agabanta. Haka suka fito jiki a sanyaye,  Hajiya Binta sai kuka take dan tasan ta k’are mata. 

Kallon Hajiya Binta Alkali yayi yana fad’in kinji shedun da aka kabartar ma kotu,  ko kina da ja akan abinda aka fad’a? Girgiza kai tayi tana goge hawaye tace na amince da abinda aka fad’a,  amma wallahi sharrin shed’an ne,  son zuciya da neman duniya yasa na aikata abinda ban tab’a yi ba,  ina rokon wannan kotu da ta mani sassauci. 

Alkali yace Likita kana da ja akan abinda aka fad’a?  Girgiza kai yayi yana goge zufa yana fad’in na amince,  amma wallahi Hajiya Binta ce ta bani mak’udan kud’i akan nayi rubutu akan k’arya kuma nazo na bada sheda,  dan Allah arufa mani asiri. 

Alkali yace kotu wajen adalci ne,  duk wanda kaga yazo kotu to yazo ne domin abi masa hakkinsa,  babu batun wani rufin asiri a kotu domin wajen tonon asiri ne,  dan haka kowa ya tsaya yaji hukuncinsa. 

Hajiya Binta…. Kinfi kowa laifi anan,  dan haka kotu ta yanke maki hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari,  sannan zaki biya Amina tarar dubu d’ari biyar abisa kok’arin ki na b’ata mata suna da kikayi. 

Iya…. Kema kotu ta yanke maki d’aurin rai da rai agidan yari,  amma kin samu sassaucin aikin wahala abisa kokarin da kikayi na warware gaskiya da kikayi. 

Likita….. Kaci amanar aikin ka, an had’a baki da kai anyi rashin gaskiya,  dan haka kotu ta yanke maka d’aurin wata biyar agidan yari,  kuma zaka biya Amina tarar dubu d’ari biyu abisa b’ata mata suna da kayi. 

Wannan kotu tana yima Brr. Ra’eez jinjina akan namijin kok’arin da yayi wajen gano gaskiya,  da fatan kowa zai d’auki darasi akan wad’annan mutanan,  sannan kotu ta wanke Amina daga zargin da ake mata,  ciki na mijinta ne, kuma dole yaci gadon mahaifinsa…. Kotttttt!!!! 

Gaba d’aya mutanan mik’ewa sukayi suna ma Alkali tafi,  sosai mutane suke son Alkalin su,  domin suna ganin shi d’in adali ne,  yana kokarin zartar da hukunci akan duk wanda aka kama da laifi. 

Hannu Brr. Bajinta ya mik’a ma Brr. Ra’eez yana fad’in ina taya ka murna akan wannan nasara da kayi,  ba’a tab’a samun wanda ya kada ni a shari’a ba,  sai gashi sabon zuwa yayi mani warwas,  duk da ba yaune ka fara aiki ba,  anyi maka canjin wajen aiki ne  amma duk da haka kayi kok’ari,  sai mun had’e wani lokacin. 

Murmushi Brr. Ra’eez yayi yana fad’in nagode.

 Har kusa da Brr. Ra’eez dangin Amina suka zo suna masa godiya. Brr. Ra’eez yace haba ai bakomai ku godema Allah. Sallama yayi masu suka fita shida Jabeer. 

Bayan sunyi sallama da Jabeer ya zo shiga mota yaji ana masa magana,  yana juyowa yaga *ALKALI NE,* murmushi yayi yana masa sannu. Alkali yace kaine da sannu,  gobe idan kashigo ina son ganinka a ofis. Jinjina kai yayi yana fad’in to yallab’ai. Sallama yayi mashi ya tafi.

 Da kallo Alkali ya bishi yana sakin murmushi, a zuciyarsa yana nanata sunanshi (Brr. Ra’eez Hamza MWD), kamar ya san mai shigen sunansa sheru da yawa,  sai dai kuma wancan ba haka sunansa yake ba, to me MWD take nufi kuma?  Kafad’a ya d’aga yayi gaba. 

**** ****

Kai tsaye babbar gidan yari ya nufa,  bayan sun gama gaisawa da masu gadin yashiga ciki ya zauna yana jiran akira masa wanda yazo wajensa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button