ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

Wani babban mutum ne ya fito yana sanye da kayan gidan yari ajikinsa,  da ganinsa daga aiki yake. Yana zuwa Brr. Ra’eez ya mik’e ya bashi wajen zama. 

Bayan sun gaisa Brr. Ra’eez yace *KAWU* nayi nasara,  yanzu aka gama yanke hukunci anjima za’a kawo masu laifin nan. Murmushi wanda aka kira da Kawu yayi yana fad’in nasan zakayi nasara Ra’eez,  an haifeka ne domin Nasara, yanzu kam hankalina ya kwanta,  nasan k’arfin ka ya kawo,  zaka iya gogawa da kowa,  nayi farin ciki da aka maidoka wannan kotu da aiki,  nasan aikin *Alhaji Mansur* ne,  yana matuk’ar kok’ari akan ka,  yarik’e amana,  shima Allah bazai barshi ahaka ba. 

Brr. Ra’eez yace ai Kawu ban tab’a kukan rashin Mahaifina ba,  Abba Mansur ya gama mani komai arayuwa,  fatana Allah ya bani ikon saka masa. Kawu yace Allah yasa,  kai dai kacigaba da hak’uri arayuwa zaka cigaba da samun nasara,  kaje wajen Umman ka kuwa? Brr. Ra’eez yace yanzu dai zan biya. 

Kawu yace ka dubata da jiki,  sannan ka kiyaye da wannan Alk’alin,  zuwa gaba zaka gane nufina,  nasan Alhaji Mansur ya fad’a maka wasu abubuwa amma dole kasan komai domin ka shirya yakin kwato ‘yanci tare da d’aukar fansar Mahaifinka,  kada ka sake ka fad’ama kowa abinda MWD yake nufi har sai burinka ya cika,  shiyasa naji dad’i da akafi sanin mahaifinka da sunansa na biyu. Ra’eez yace insha Allahu zan kiyaye.  Tashi yayi ya mik’a masa kud’i yana fad’in sai na sake dawowa. Kawu yace Allah yayi maka albarka. 

***

    *PSYCHIATRIC HOSPITAL* (ASIBITIN MAHAUKATA) 

Zaune Brr. Ra’eez yake akusa da wata babbar mace,  duk wanda ya ganta yasan tana cikin yanayi na hauka,  zaune take tana kallon ‘Danta wanda ya bud’e ledar da yazo da ita wadda take d’auke da kayan motsa baki. 

Lemu ya d’auko yana kok’arin bud’e mata,  da sauri ta warce tana kok’arin fasa kwalin. Murmushi yayi ya mik’a hannu yana fad’in Ummu na bani na bud’e maki kinji. Kallonshi tayi kafin ta mik’a masa kwalin. 

Bud’e mata yayi ya zuba mata akofi ya bata. Amsa tayi ta shanye tana mik’a hannu. Aiba ya b’are mata ya bata. Rabi taci kafin ta mik’a masa rabin abaki,  amsa yayi ya gutsura hawaye suna zubo mashi. 

Hannu tasa ta goge masa hawayen tana fad’in Likita yace adena kuka,  yace Alhaji zai dawo,  ba dai sun kashe shi ba?  Idan na fito zamuje mu kashe su dukan su,  ai dai zaka siyo mani wuk’ar Makka ko?  Kasan ita kad’ai ce zata iya kashe su. 

Murmushi yayi yana fad’in Ummu bazan kyale jinin Abbu ya tafi abanza ba,  zanyi kwakkwaran bincike,  akwai rud’u acikin wannan lamarin,  dole sai nasa natsuwa kafin na gano su,  bazaki dawwama ahaka ba,  Allah zai baki lafiya.

 Dariya tasa ta kamo hannunshi tana fad’in nima binshi zanyi,  kai kad’ai zamu bari ai,  sai kaje makka kasiyo wuk’a ka kashe su. Wani likita ne ya k’ara so. Bayan sun gaisa Brr. Ra’eez yace nagode likita,  kana kok’ari akan Ummu na. Likita yace haba bakomai,  tana samun kulawa sosai,  yanzu ma lokacin shan maganinta ne,  kasan tana sha take bacci. Jinjina kai Brr. Ra’eez yayi yana fad’in nima tafiya zanyi,  nagode sosai likita. Hannu ya bashi yana fad’in Allah ya baka lada Brr. Ra’eez,  hakika da wuya asamu irin ka da yawa aduniya,  kana kok’ari akan Mahaifiyarka. Hawaye Brr. Ra’eez ya goge yana fad’in dole nayi Likita,  duk wanda yasan darajar *UWA* zaiyi fiye da abinda nakeyi,  Uwa ba abun wasa bace.

 Likita yace haka ne gaskiya,  Allah yayi mana jagora. Brr. Ra’eez yace amin. Sallama sukayi ya wuce yana kallon Ummunsa. 

Kai tsaye gidanshi yawuce da yake unguwar  ( *APAPA*). Kwance yayi a falo hawayen da suka zamar masa jiki suna kwaranyo masa,  gaba d’aya baya jin dad’in ranshi,  duk lokacin da ya kai ziyara wajen Ummunsa haka yake kasancewa,  kuma duk da haka baya iya faashi wajen zuwa ganinta,  can ne kad’ai yake zuwa yaji dad’i aranshi. Runtse ido yayi yana fad’in Allah gani gare ka,  Allah kayi mani jagora akan wannan al’amari,  bani da gata sai kai ya Allah,  kashige mani gaba wajen gano gaskiyar wannan al’amari,  Allah ka tona asirin wad’an da suka aikata ma Mahaifina wannan abun,  Allah ka tona asirinsu ta yanda bazasu iya k’aryatawa ba. Juyi yayi yana sakin kuka marar sauti. 

 *GA DUK WANDA YAKE SON CIGABAN WANNAN LABARI ZAI TURO NAIRA 200 KACAL, MTN CARD TA WANNAN LAMBAR.. 08147669770, SAI KAYI SCREEN SHOT KA TURA TA WHATSAPP A LAMBAR K’ASA,  IDAN KUMA BANK TRANSFER NE,  KA  TUNTUBE NI TA WHATSAPP NO 08028525263 ZA’A SAKA GROUP DIN DA ZA’A RIKA POSTING. NAGODE. SAI KUYI HAKURI DA YANDA LITTAFIN YAZO.*

Ur’s. 

NABILA RABI’U ZANGO

(Nabeelert Lady) 

08028525263

[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne. naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa,  idan kuma bank transfer zakayi sai  ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar.  08028525263*

0⃣2⃣

Da kyar ya tashi yayi wanka,  bayan yayi sallah ya fita zuwa gidan Kawu dan can ne waje na biyu da yake d’ebe masa kewa,  duk da Kawu ya so ya koma can da zama amma yaki komawa, acewarsa yafi son kad’aici. 

Da sallama yashiga cikin gidan,  a tsakar gida ya iske matar gidan tana kok’arin kauda kayan da suke a tsakar gidan. Amsa sallamarsa tayi tana fad’in Ra’eez sannu da zuwa. 

Zama yayi yana fad’in yauwa sannu da aiki Mama,  ina *RUMAISA* kike aiki ke kad’ai? Murmushi Mama tayi tana fad’in na aiketa siyen kayan miya ne shiyasa nake rage aikin kafin ta dawo. 

Jinjina kai yayi yana fad’in Kawu yana gaishe ku. Mama tace ka je kenan?  Ra’eez yace naje na sanar dashi yanda shari’ar tamu ta kasance ne. Mama tace ikon Allah,  ashe fa yau ka fara shiga babbar kotu ko?  Ina fatan dai komai yayi dai-dai?  Ra’eez yace Alhamdulillahi Allah ya amsa addu’ata,  komai ya tafi yanda ya kamata,  domin nine nayi nasara. 

Mama tace kai amma naji dad’i,  Ubangiji Allah ya baka ikon yin nasara akan shari’ar da zaka fara nan gaba domin kwato hakkin mu da aka danne. 

Ra’eez yace amin Mama. Hannu tasa ta goge kwallar data zubo mata tana fad’in ina Kawun naka babu dai abinda yake damunsa ko? Ra’eez yace lafiyarsa lau yace agaishe ku ma. 

Mama tace amma yana cikin wahala ko?  Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Mama ki daina damuwa,  sam basa sashi aikin wahala domin akwai mutane na acikinsu,  muna mutunci sosai hakan yasa suke sauk’ak’a masa,  addu’a itace abinda zamuyi masa. 

Mama tace haka ne,  shiyasa fa bana son zuwa wajensa,  duk lokacin da naje ina dad’ewa kafin na warware,  ya jikin Ummun ka? Duk’ar da kai Ra’eez yayi yana fad’in kamar kullum Mama. 

Girgiza kai tayi tana fad’in Allah ya bi mana hakkin mu,  an zalince mu an tauye mana hakkin mu,  Allah ne kad’ai zai iya saka mana,  Allah ya baka ikon jure wannan jarabawa Ra’eez,  hakika an zalince ka,  an rabaka da Mahaifinka,  ga halin da Mahaifiyarka take ciki,  Allah ya baka ikon gano gaskiya kuma ya baka sa’a akan kosu waye suka aikata hakan,  babu abinda zamuce da kai sai godiya,  Allah ya saka maka da alkhairin abinda kake mana,  karike mu amana tamkar jininka. 

Ra’eez yace amin Mama,  amma bana so kina mani wata godiya,  kun wuce duk yanda kuke tunani a waje na,  bani da kowa a garin Lagos sai ku,  duk da bamu had’a komai da ku ba amma Allah ya had’a mu,  ku da Abba Mansur kun zame mani ‘Yan uwa na jini,  ku kad’ai nake kallo naji dad’i arayuwata,  ta silar Mahaifina Kawu yashiga halin da yake ciki,  tunda babu Abbu dole na maye gurbinsa awajen ku,  domin nasan da yana raye shi mai rik’e ragamar gidan ku ne,  dan haka kada ki sake mani godiya,  ke Uwace agare ni. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button