ALKALI NE Page 1 to 10

Jinjina kai Mama tayi tana goge hawayen idonta tace haka ne Ra’eez, hakika kai ‘Dah nagari ne, ko wace Uwa zatayi alfahari da samun ka, kada ka sake cewa ta silar Mahaifinka Malan yashiga wannan halin, dama can Allah ya rubuto masa K’addararsa a haka, fatan mu Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar. Ra’eez yace amin.
Sallamar Rumaisa ce ta katse su, amsawa sukayi. Da sauri ta k’araso tana fad’in Yayana sannu da zuwa. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Rumaisa ya gidan? Tace lafiya lau, an gama shari’a lafiya? Ra’eez yace lafiya lau nayi nasara.
Tashi tayi tana murmushi tace naji dad’i Allah ya k’ara d’oraka akan makiya. Ra’eez yace amin ‘Yar K’anwata. Mama tace an samo komai ko? Rumaisa tace an samo.
Tashi Mama tayi tana fad’in bara na tayaki naga lokaci ya kure. Da sauri Ra’eez yace aa Mama kinyi aikin ki, yanzu mune zamu shiga ofis. Dariya sukasa, Mama tace ai shikenan ayi aiki lafiya bara naje na gyara cikin kafin Abdallah ya dawo makaranta.
Ra’eez yace ina ruwan Autan Mama, ina fatan dai yana karatun sosai? Rumaisa tace ai Abdallah ba wasa, dana fad’a masa zaka zo sai kaga ya dage. Ra’eez yace saura ke, tunda kin gama makaranta.
Turo baki Rumaisa tayi tana fad’in Yaya kaima dai ka san ra’ayina ai. Harara ya wurga mata yana fad’in wannan tsohuwar magana ce, dan haka dole kiyi karatu.
Duk’awa tayi tana hawaye tace dan Allah Yaya bana son karatu. Murmushi yayi yana fad’in Rumaisa kina nan da ra’ayinki, da ace baki da kok’ari da bazan takura maki ba, kada ki manta kece zakara a makarantar ku fa, tun kafin kishiga makaranta fa kike da kok’ari, meyasa baza kiyi amfani da iliminki ba? Kece babba agidan nan, kina ganin halin da Mahaifinki yake ciki, ga Abdallah k’aninki yana makaranta, baki so yayi koyi da ke? Idan yaga baki karatu shima sai abun ya fice masa arai ai.
Hawaye ne suka zubo ma Rumaisa. Ra’eez yace ba kuka nasa kimun ba, gaskiya nake fad’a maki, a zamanin nan kowa yana son auren mace mai ilimi, ko ba dan kanki ba zaki taimaki yaranki, Rumaisa duk kok’arin ki matuk’ar baki wuce karatu ba wata rana zaki nemi ma’anar kalma d’aya ki rasa, domin shi ilimi sai ana tilawarsa yake zama, duk da kinayin islamiya amma zakisha wahala matukar bakiyi karatun boko ba, bance dole kiyi aiki ba, amma idan kikayi karatun wata rana kwalin zaiyi maki amfani, kin ganni nan bazan iya auren macen da iyakarta sakandire ba.
Da sauri Rumaisa ta d’ago tana kallonshi. Jinjina kai yayi yana fad’in da gaske nake, nafison na auri mai ilimi kodan saboda yaran mu, idan kuma auren kike so badamuwa ki fito da wanda kike so ni zan maki aure.
Mama ce ta fito tana fad’in gara dai kayi mata fad’a, kullum maganar da nake mata kenan amma ta toshe kunnanta, tunda Rumaisa ta taso take fad’in baza tayi karatu ba bayan ta gama sakandire, ada na d’auka yarinta ce ashe har zuciyarta abun yake, ko auren da kake magana ai bata kula kowa, na rasa inda tasa gaba.
Ra’eez yace barni da ita Mama, kada ki sake mata maganar karatu, nima bazan sake mata ba, kuma dole tayi aure. Murmushi Mama tayi ta shige tana fad’in aiko zan fara shirin biki.
Da sauri Rumaisa ta tashi tana dire-dire ta nufi kicin tana gungunai. Dariya Ra’eez yasa yana rufe baki. Tashi yayi yana fad’in bani alaiyahun na yanka maki. Baki ta murgud’a tana fad’in bana so. Dariyar da yake b’oyewa ce ta kwace masa, sosai yake dariya. Kayan miyar ta d’auka ta cigaba da aikinta tayi banza dashi.
Tashi yayi yana fad’in bara na d’auko maki tsarabar ki amota na manta. Bata kulashi ba yayi waje. Bayanshi tabi da kallo hawaye suna zubo mata, dole ma ta amince tayi karatu matuk’ar tana son Yayanta, da sauri ta d’auko wayarta ta rubuta mashi ya samo mata makarantar aikin lafiya ta unguwar zoma (Mid-Wife) zatayi karatun.
Tun a zaure Ra’eez yake dariya, sai da yasha dariyarsa kafin yashigo ciki, dama yasan idan ba haka yayi mata ba baza tayi karatun ba, yana matuk’ar son Rumaisa amma yafi so ya auri mai ilimi, kamar tasan yana son mace tayi aikin asibiti ta zab’i haka. Ciki yashiga ya fara taya ta aiki be nuna mata yaga sakon ta ba.
**** ****
Kwankwasa k’ofar ofis d’in Alkali yayi kusan sau biyu kafin daga ciki aka bashi izinin shiga. Tare da Brr. Bajinta ya iske Alkali. Murmushi Alkali yayi yana fad’in kaga d’an halak d’in ma, yanzu muke maganar ka ashe kana hanya.
Hannu Ra’eez ya mika masu suka gaisa cike da girmamawa. Kujera Brr. Bajinta ya nuna mashi yana fad’in bismillah. Zama yayi Alkali yace ba dai yanzu kashigo ba? Ra’eez yace tun d’azu nazo nasan baka shigo ba shiyasa na zauna a ofis.
Alkali yace ya gajiyar aikin jiya kuma? Ra’eez yace Alhamdulillahi. Brr. Bajinta yace ai jiya Brr. Ra’eez ya caza mana kwakwalwa, na rasa yanda akayi ya iya had’a wannan aikin acikin sati d’aya.
Alkali yace shiyasa nace ya sameni domin naji yanda akayi yayi wannan kok’arin, gaskiya ban tab’a samun mutum irinka mai hazaka ba, shiyasa tun ajiyan nayi masa jinjina. Brr. Ra’eez ko zaka fad’a mana yanda akayi kayi wannan aikin haka? Kada ka damu nasan ba hurumi na bane nayi maka wannan tambayar, kawai dai naga kok’arin ka ne shiyasa zan so naji daga gareka.
Murmushi Ra’eez yayi ya kauda kai bece komai ba. Tashi Brr. Bajinta yayi yana fad’in Yallab’ai zanje ana jira na a ofis. Alkali yace to badamuwa nagode.
Bayan ya fita Ra’eez ya d’ago kai, dama saboda Brr. Bajinta yaki yin magana, taya Alkali zai tambayeshi agaban abokin aikinsa bayan yasan tare suka kara.
Alkali yace yi hak’uri nayi maka tambayar da bata dace ba. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in haba ba komai. Alkali yace kawai ina so naji yanda akayi ka iya gano gaskiya ne dan gaskiya ka burgeni, zan so ka saki jiki dani, ka d’auke ni tamkar d’an uwanka dan gaskiya ka burge ni, da alama ba’a garin nan kake ba ko? Kai Ra’eez ya girgiza yana fad’in a garin nan nake, sai dai ba anan nayi karatu ba shiyasa, nayi aiki a babbar kotu da take kano na kusa shekara d’aya kafin na nemi canjin wajen aiki aka maido ni nan.
Alkali yace zuwanka alkhairi ne a kotu ta, domin ina da buk’atar mutane irin ku, domin tunda na saurari bayaninka na gano kana da gaskiya, dan haka kacigaba da rik’e gaskiya dan ita ce cikar darajar mutum.
Ra’eez yace nagode da wannan karamcin daga gare ka, kuma insha Allahu ba zaka sameni da rashin gaskiya ba. Hakika lokacin da nazo wannan kotun na kawo takardar canjin aikin da akayi mani aranar na iske wannan shari’ar, zaman da nayi ina jiranka alokacin na tsinci kad’an daga cikin shari’ar, alokacin Lauyen da yake kare Amina naji yana fad’in bazai iya cigaba da shari’ar ba, domin yayi iya bincikensa ya kasa gano komai, gashi Brr. Bajinta ya fishi sanin makamar aiki bazai iya gogawa dashi ba, yaso ya taimaka ma Amina amma dole ya hakura har ya fad’a mata ta samu wani lauyen kafin lokaci ya kure mata.
Bayan dana gama jin firarsu bayan da kazo nashiga muka gama komai kasa a nuna mani ofis d’in mu shine naje nayi masa sallama na gabatar masa da kaina na nuna masa naji firarshi ko zai iya bani dama na amshi shari’ar da yakeyi? A lokacin da nayi masa magana sosai farin ciki ya bayyana a fuskarshi, babu b’ata lokaci yashiga warware mani komai akan shari’ar.