ALKALI NE Page 1 to 10

Aranar bayan na koma gida banyi bacci ba, yanda ya bani labarin na zauna na fitar da komai, washe gari na nufi gidan marigayi nida lauyen, bayan munje muka samu Amina ya fad’a mata nine zan karb’esa.
Sosai tayi farin ciki anan tashiga bani labarin gaskiyar abinda ta sani, bayan nayi mata tambayoyi anan na gano mai aikinsu bata gidan da dad’ewa, shine nace mata ina so ta fad’a mani inda zan samu Iya, shine ta fad’a mani ‘yar asalin ‘Danja ce, sai dai bata san gidanta ba, amma ta tab’a fad’a mata gidanta yana bayan kasuwa wata rana da suke fira.
Bayan na gama jin labarin Iya sai na nemi da ta fad’a mani aminin Alhaji data sani, shine ta fad’a mani sunan Alhaji Kabeer, nan nace mata zan tafi tunda babu lokaci, ina so naje can garin su Iya. Haka mukayi sallama da ita muka tafi.
A ranar nabi jirgi zuwa kano, washe gari na nufi funtua sai da na huta daga can naje garin su Iya, cikin ikon Allah bansha wata wahala ba na gano gidanta, alokacin da naje mata da bayanin daga Lagos nake nasan tayi aiki agidan Alhaji k’ark’ashin Hajiya Binta.
Fad’ar sunan Hajiya Binta yasa Iya ta fara kuka tana fad’in ba laifinta bane, tun anan na gano akwai wata ak’asa, hakan yasa na lallab’ata nace ta bani labarin abinda ta sani domin Alhajin ya rasu.
Haka ta warware mani komai tana kuka, na tausaya mata domin naga nadama a idanuwanta, nan na roketa akan ta biyoni idan har ta yarda tayi nadama kuma tana so ayi mata hukunci a duniya.
Babu b’ata lokaci ta amince, domin ta fad’a mani gara a yanke mata hukunci akan rayuwar da takeyi agarinsu, duniyar tayi mata zafi koda banje ba ta yanke shawarar barin garin ta koma wani gari ko zata samu sauki. Naji dad’in maganarta, aranar muka nufi Funtua da ita, dole ta mota muka dawo saboda naga zamu b’ata lokaci.
Bayan da muka dawo naje na samu ‘Dan sanda yayi mani jagora zuwa gidan Alhaji domin a bayanin Iya ta fad’a mani ta aika masa da takarda, bayan munje na tambayi Amina ko an samu wata takarda a d’akin Alhajin wadda aka fad’a masa tana da ciki? Sai tace gaskiya bata sani ba, ganin haka yasa muka nemi izinin Hajiya Binta muka shiga d’akin, cikin sa’a na samu wannan takardar dana gabatar.
Haka muka tafi na nuna masu ban samu komai ba. Bayan nan naje na samu Alhaji Kabeer, shima mun dad’e muna tattaunawa dashi kafin muka rabu, ana saura kwana d’aya a koma kotu na kammala had’a shedu na, cikin ikon Allah nazo na gabatar dasu kuma nayi nasara. Kaji yanda akayi na gano komai cikin lokaci.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in gaskiya Brr. Ra’eez kai na daban ne, basirar ka daga Allah take, kayi aiki da ilimi, sai kwararren lauye ne zai iya abinda kayi, sai gashi baka dad’e da aikin ba amma ka tafiyar da wannan shari’ar mai rikitarwa, gaskiya dole na yaba maka, kayi abinda ya kamata, kuma daga yau ka zama babban lauya a wajena, insha Allahu zan rik’a aiki da kai, domin ra’ayin mu iri d’aya ne, ina son mutum mai son zakulo gaskiya a duk inda take.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in nagode Yallab’ai. Alkali yace karik’a kirana da Abba kamar yanda Yarana suke kirana zanfi jin dad’in hakan domin nasan zakayi sa’an ‘Dana na biyu, duk da banyi aure da wuri ba da nasan sai dai kazo ana ukku ma.
Ra’eez yace to Abba nagode. Alkali yace a ina kake da zama ne? Yace a Apapa nake. Alkali yace kayi aure ne ko kana zaune da Iyayen ka? Murmushi yayi yana fad’in banyi aure ba ni kad’ai nake zaune. Alkali yace Allah sarki, Iyayenka ba anan suke ba ne? Baki Ra’eez ya bud’e zai bashi labarinsa sai kuma ya tuna da maganar Kawu ( *Ra’eez ka koyi b’oye sirrin ka, a ciki hada labarin zuri’ar ka, kasan dai yanda kake kok’arin gano wad’an da suka aikata ma Iyayenka wannan abun, kuma nasan dole asan Mahaifinka agarin nan tunda babban mutum ne, kuma ana da tabbacin akwai sa hannun manyan mutane a kisanshi, a ciki hada lauyen da nake zargi domin Mahaifinka ne ya hanasu sakewa hakan yasa suke kokarin ganin bayansa, bani da sheda a hannu amma ina zarginsu domin sune abokan fad’an mahaifinka, dole ka b’oye labarinka har sai komai ya kammala domin gujema matsala, bana son kowa yasan ko kai waye, dan haka bana son ka fad’ama kowa labarin ka.*)
Gyara zama yayi yana fad’in Iyaye na suna Gombe ni kad’ai ne anan. Alkali yace Allah sarki, lallai kayi nisa da gida, bakomai ka d’auke ni tamkar Mahaifinka, idan ka tashi kajira ni sai muje na gabatar da kai a wajen Iyalina domin karik’a zuwa kuna gaisawa, ina zaune a *SURELERE*.
Ra’eez yace bakomai zan jira ka. Alkali yace nagode zaka iya tafiya. Wayar Alkali ce tayi k’ara, sallama Ra’eez yayi masa ya fita. Bayan ya d’auka suka gaisa, alamu sun nuna abokinsa ne ya kira. Shiru yayi yana jin bayanin da yake masa. Kai ya jinjina yana fad’in haba *Alhaji Marusa* wannan ai ba abun tada hankali bane, shikenan na gane bayanin ka, insha Allahu bamu da sauran matsala, na kammala shari’ar da nake fad’a maka kuma an gano gaskiya, sabon lauya ne ma ya gano komai, ai ina fad’a maka yanzu ya bar ofis d’ina, gaskiya yaron yana da hazak’a, dan haka abinda ya kamata zan rik’a bashi, sauran kuma sai aba Brr. Bajinta saboda kasan shine namu bazamuyi saurin nuna fuskar mu a wajen sabon zuwa ba. To shikenan sai kazo. Wayar ya aje yana murmushi.
Tunda Ra’eez ya shiga ofis ya gama duba takardun da suke akan teburinsa ya janwo hoton da sukayi shida Iyayenshi, alokacin bai wuce shekara takwas ba, yana tsakiyarsu suna dariya aka d’auki hoton. Koda yaushe yana tare da wannan hoto dan shine yake d’ebe masa kewar Mahaifinsa.
Zaroshi yayi daga cikin jakar da yake ajeshi (wallet) aranshi yana fad’in dole ya maidashi gida ko dan gudun b’acin rana, tunda Kawu yace ya kikaye barin duk wata alama da zata nuna koshi waye har sai ranar da burinshi ya cika.
A hankali yasa hannu cikin dabara ya goge hawayen da suka kusa gangaro masa ta gefen gilashinsa, tashi yayi yasa hoton a aljihu ya d’auki mukullin mota domin yaje ya aje hoton agida dan hankalinsa yaki kwanciya akan ya kara ko mintuna biyu a wajenshi, hakan yasa ya fita domin yaje gida ya adana hoton.
A waje suka had’u da Brr. Bajinta ya rako wasu manyan mutane, da ganinsu ba sai an fad’a maka naira ta zauna masu ba, har sun gaji da kud’i a yanayin jikinsu, motar da suke tsaye ajiki kad’ai abun kallo ce bare kuma suturar da take jikinsu. Yanda yaga Brr. Bajinta yana wani risna masu ya k’ara tabbatar masa da su d’in wasu ne.
Kai tsaye wajen daya aje motarsa ya nufa ba tare daya sake kallon su ba, maganar Kawu ce take masa yawo akan tsohon ma’aikacin wannan kotu mai suna *Brr. Barau*, akoda yaushe yafi tsayama masu hannu da shuni akan talakawa, hakan ya nuna masa yana danne gaskiya akan k’arya, tunda ya kasance shine ya tsaya har aka yanke ma Kawu hukunci amatsayin ya kare hakkin Mahaifinsa wannan ya nuna akwai wata ak’asa, duk da hakkin mahaifinsa ya kare amma kuma ai ba Kawu bane ya aikata laifin meyasa ya tsaya har sai da yaga an yanke masa hukunci? Gaskiya dole ya fara bincikensa akan Brr. Barau, to wai ma yana ina? Yasan dai zuwa yanzu kila ya aje aiki ko kuma ya zama shugaba, gashi kuma Kawu bai fad’a masa komai akansa ba, ko hotonsa bai sani ba bare idan ya ganshi ya ganeshi, amma zai tambayi Kawu inda yake.