ALKALI NE Page 1 to 10

Haka ya isa gida da wannan tunanin. Bayan ya adana hoton ya zauna yana tunanin hanyar da zai fara bibiyar Brr. Barau domin ya gano hakikanin gaskiya, dole ta kanshi ne zai fara aiki hakan zaisa ya gano komai, domin lokacin da aka kashe mahaifinsa bai bari kowa ya kai k’ara kotu ba yayi saurin amsar shari’ar Mahaifinsa yayi tsaye har sai da yaga an gama komai cikin k’ank’anin lokaci.
Saurin tashi yayi ya d’auko wani k’aramin littafinsa, sunan Brr. Barau ya fara rubutawa aciki kafin ya b’oye littafin ya kwanta yana kallon sama. Dole ya gano masu hannu akisan Mahaifinsa kodan ya sama ma Mahaifiyarsa lafiya domin ta silar mutuwarsa ta samu kanta acikin wannan hali. Ta ina ya kamata ya fara kenan? Dole yaje wajen aikin Mahaifinsa yasan zai samu wani abu, sannan lokaci yayi da Kawu zai bashi labarin Mahaifinsa, saboda Abba Mansur ya fad’a masa Kawu ne kawai zai iya bashi labarin komai. A zabure ya tashi ya d’auki mukullin motarsa ya nufi gidan Yari, bazai iya jira a k’ara kwana ba tare da yasan labarin Iyayensa ba.
Yaci sa’a alokacin da yaje suna hutawa, hakan yasa akayi kiran Kawu suka samu waje suka zauna. Kawu ya kalleshi cike da mamaki yana fad’in Ra’eez lafiya? Wannan zuwan fa? Kuka Ra’eez yasa yana fad’in daga wajen Alkali nake, yace mani yana son yarika aiki dani, gashi na gama duba sunayen ma’aikatan wajen banga sunan Brr. Barau ba, dan Allah Kawu ka bani labarin komai.
Murmushi Kawu yayi yana fad’in wannan Alkalin ai shine Brr. Barau, na fad’a maka ne saboda kasan ta yanda zaka cigaba da tarayya dashi, kuma tunda yanzu ka kawo girma dole na baka labarin komai saboda ka fara shiryama doguwar shari’a, yanzu zakaji komai……
*ASALIN LABARIN*
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka turo a whatsapp ta lambar k’asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub’e ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263*
0⃣3⃣
*ALHAJI HAMZA MAI WADA* shine cikekken sunansa, asalinsa d’an *MAIDUGURI* ne, aiki ne ya fito dashi daga garinsu, ma’aikacin *KWASTAM* ne, yayi aiki a garuruwa da yawa, tun yana a k’aramin matsayi har Allah ya d’agashi, mutum ne mai gaskiya da amana, kowa yasan yanda halin masu irin aikinsu yake a wannan zamani, duk wanda aka ce maka yana aikin Kwastam da wuya ka sameshi mai gaskiya, zaka sameshi mai dukiyar gaske musamman idan akace ya kai babban matsayi, kafin ka samu mutane masu irin wannan aikin da gaskiya a wannan zamani zaka sha wahala, akwaisu sai dai basu da yawa.
Alhaji Mai Wada ya kasance acikin mutane masu riko da gaskiya da amana, wanda hakan ya jawo masa bakin jini a wajen manyansa da kuma manya a najeriya, yayin da ya jawo masa farin jini a wajen masu k’aramin k’arfi musamman masu shigo da kayansu ta hanya mai kyau.
Saboda halinsa yasa ake yawan canza masa wajen aiki, wannan dalilin ne yasa yayi zama garuruwa da yawa, hakan ne ya jawo masa rashin yin aure da wuri, domin yana ganin akwai zalinci yayi aure ya bar matar ya tafi wajen aikinsa.
Sai da ‘yan uwansa suka matsa masa kafin ya amince su zab’a masa wata daga cikin danginsa dan baya son yaje wani waje ya samo mata. Kasancewar zuri’arsu akwai had’in kai, dan zaune suke a waje d’aya, katafaren gida ne mai b’angarori da yawa hakan yasa duk ‘yan uwan suke zaune awaje d’aya, dama basu da wani yawa a zuri’arsu.
Cikin lokaci k’ank’ani aka sama masa mata mai suna *BILKISU*, mace ce mai hakuri da juriya, masaniya ce a karatun addini, iya karta diploma a fannin girke-girke, lokacin da aka mata maganar anyi mata miji babu b’ata lokaci ta amince dan dama yana burgeta.
Bayan anyi bikinsu da wata d’aya aka sake masa canjin wajen aiki zuwa Kano. Haka ya tafi ya kwashi kusan wata biyu kafin ya dawo, da zai koma Mahaifinsa yace daga yanzu duk inda aka maidashi ya d’auki matarsa su tafi, be amince masa yarik’a barinta ba, da ace tare suka tafi kila da yanzu ta samu rabonta, amma ya tafi har wata ukku taya zai tara zuri’a a haka.
Haka ya d’auki matarsa sukayi sallama da ‘yan uwa sai kuka Bilkisu take kamar kada ta bishi. Haka suka tafi cike da kewar gida. A wannan karon ya dad’e a Kano ba’ayi masa canjin wajen aiki ba.
Har Bilkisu ta haifi d’anta namiji suka koma gida domin ayi suna acan. ‘Yan uwa sunyi matuk’ar farin ciki, domin Alhaji Mai Wada shine babban ‘Dah a zuri’arsu, kuma gashi Allah ya bashi magaji. Anyi taron suna na gani na fad’a, anyi hotuna kowa yayi farin ciki, inda aka sama yaron *RA’EEZ*.
Bayan suna haka ya tafi ya barta anan sai bayan tayi arba’in kafin ta koma. Kwanan su talatin da biyar Mahaifinsa yayi masa waya akan yazo ya d’auki matarsa.
A washe gari ya taho. Bilkisu kuka tasa da taji zasu tafi dan asonta tayi kwana hamsin, sauran matan ma hakuri suka bama Mahaifin Alhaji Mai Wada amma yace sai sun tafi baiga amfanin zamanta ba ta bar mijinta shi kad’ai.
Haka suka tafi sai kuka takeyi. Tafiya suke Alhaji Mai Wada yana tunanin maganganun da sukayi da Mahaifinsa adaren da zasu taho, haka kawai yake jin jikinsa yana sanyi.
Bayan komawarsu da sati biyu fad’a ya kaure a Maiduguri, gaba d’aya babu wanda ya tsira a gidansu. Lokacin da suka samu labari sumewa Alhaji Mai Wada yayi, kwanansa biyu a asibiti kafin ya farfad’o.
Bilkisu ma duk ta fita hayyacinta. Babban aminin Alhaji Mai Wada wato *ALHAJI MANSUR*, shine wanda yake tsaye akansu, shima d’an Kano ne babban d’an kasuwa ne, tunda Alhaji Mai Wada ya dawo Kano ya tab’a taimakonsa akan wasu kayansa da wasu suka so dannewa, tun daga lokacin suka kulla abota, sun zama tamkar ‘yan uwa, matarsa *AISHA* suna zumunci da Bilkisu sosai, dan halinsu yazo d’aya.
Bayan da aka sallamesu Alhaji Mai Wada yaso su tafi can garinsu amma Alhaji Mansur ya hanashi dan garin a hargitse yake. Sai da aka rik’a had’a masu da rokon Allah kafin suka samu natsuwa.
Sai da akayi watanni da faruwar abun kafin suka je domin su duba ko akwai wad’an da suka rayu. Haka sukaje ofishin ‘yan sanda anan suka samu labarin yanda abun ya kasance. Lokacin da sukaje unguwar su sunsha kuka, dan kamar ba’a tab’a gini a wajen ba. Sun sha kuka haka akayita basu hakuri.
Kasa zama agarin sukayi aranar suka koma Kano. Tun daga lokacin Maiduguri ta fitar masa arai, bai sake tunanin zuwanta ba, domin babu abinda zeyi bayan zuri’arsu sun mutu babu kowa, be tab’a tunanin yaje ko Allah zaisa wasu sun tsira ba, dan har lokacin ance ba’aga gawar wasu ba kuma ba’aji labarinsu ba kawai yacigaba da rayuwarsa da matarsa da d’ansa.
Lokacin da Ra’eez ya isa sawa makaranta haka aka sashi tare da d’iyar Alhaji Mansur *LABIBA*, tare ake kaisu a maidosu tare. A lokacin ne kuma Alhaji Mai Wada ya samu k’arin matsayi inda aka maidashi Lagos aka bashi matsayin shugaban Kwastam acan.
Alhaji Mansur yafi kowa shiga damuwa shida matarsa, domin sun shaku dasu Alhaji Mai Wada, Bilkisu hada kukanta, duk da ta rasa danginta sai Allah ya had’ata da Aisha, tana jinta tamkar ‘yar uwarta, sai gashi kuma yanzu zasu rabu.
Ganin halin da suka shiga ita da Aisha har ma da Alhaji Mansur sai Alhaji Mai Wada ya yanke shawarar barin Bilkisu anan domin Ra’eez ya k’arasa makarantarsa. Lokacin da sukaji haka sosai sukayi farin ciki, duk da Alhaji Mansur yaji dad’i amma kuma zaiyi rashin amini nagari.