ALKALI NE Page 1 to 10

Haka Alhaji Mai Wada ya tafi cike da fatan nasara, duk lokacin da akayi masa canjin wajen aiki yana sawa ayi masa sauka da addu’oi saboda neman tsari daga mahassada.
Tun farkon zuwanshi Lagos ya fara gano ta’asar da akeyi a wajen aikinsu, baiyi yunkurin hanawa ba duk da ya kasance shugaba, domin abinda ya sani shine ba’a saurin nuna ma mai laifi kuskurensa musamman idan kana bakon waje, ba kamar gari irin Lagos, domin ya dad’e da sanin garin, babu labarin da bai sani ba a hukumar Kwastam ta Lagos, tun kafin yazo garin yake da labari hakan yasa yayi masu kwanciyar b’auna domin ya gano komai cikin sauki ta yanda zai san yanda zai b’ullo masu.
Kowa yasan yanda aikin Kwastam yake, kowa baya da buri wanda ya wuce ya tara abin duniya. Haka ya kasance a wajen da Alhaji Mai Wada yake, akwai mataimakinsa mai suna *ADEBAYO*, d’an *kudu* ne, Allah yayi masa son kud’i ga karb’ar cin hanci kamar me, yana harka da manyan mutane na garin Lagos har ma dana waje, duk wani wanda ake shigo masa da kaya yasan da zaman Adebayo, kafin a canza ma shugabansu wajen aiki shima jirgi d’aya ne ya kwaso su, shiyasa alokacin masu kaya basa jin dad’in abinda ake masu, domin ana karb’ar kud’i awajensu sosai, idan bakaci sa’a ba wani lokacin a kama kayan ka, sai ka saki kud’i masu yawa kafin a sakar maka su.
Da yawa ma’aikatan da suke aiki ak’ansan su basa jin dad’insu, domin idan suka samu sai abinda sukaga damar yaga masu, wasu suna fatan a kawo masu canji yayin da wasu sunfi buk’atar abar masu su kodan samun na cefane da sukeyi.
Tun bayan zuwan Alhaji Mai Wada ya amshi komai a rubuce daga wajen Adebayo, sai rawar jiki yake dan yana so ya samu shiga awajenshi.
Bayan da Alhaji Mai Wada yayi wata guda a wajen sai ya canza wanda yake kula da karb’ar haraji domin ya gano ta wajenshi ana babbar b’arna, haka ya canza wanda yake kula da shigowar kaya da saukesu, haka duk ya tarwatsa kowa Adebayo kuma yace ya tsaya a matsayinsa baya so yana shiga abinda ba aikinsa ba.
Tun daga wannan rana daya tarwatsa kowa mutane da dama sunji zafinsa, yayin da wasu sukaji dad’i, wasu daga cikin wad’an da ake shigo masu da kayansu sunyi farin ciki da zuwan Alhaji Mai Wada, yayin da wasu suke bakin ciki.
Hatta da direban da ya iske wanda yake tuk’ashi sai da ya canza, domin Alhaji Mai Wada bashi da saurin yarda da mutane, tunda ya lura direban yana da kusanci sosai da Adebayo yaji bai kwanta masa ba, domin yasan wasu daga cikin halayyar Adebayo.
Ya dad’e yana tuk’a kanshi kafin ya samu direba mai suna *MALAN SANI*. Ya had’u da Malan Sani wata rana bayan ya dawo daga ofis da dare wajen k’arfe goma da rabi, ya tsaya domin ya sayi biredi sai kawai ya hango Malan Sani ya fito daga wani lungu da gudu sai waige -waige yakeyi, yana tsaye har yazo ya wuceshi sai yaga ya b’oye a bayan motarsa yana lekowa yana kallon hanyar daya fito.
Bayan daya gama siyen biredin sai ya zagayo domin yashiga mota, sam baiji tsoron komai ba ya dafa Malan Sani, a firgice ya jiyo jikinsa yana rawa. Alhaji Mai Wada yace kwantar da hankalin ka babu abinda zanyi maka, zan tafi ne kuma naganka ajikin mota ta shine na tab’o ka.
Hannu Malan Sani yasa ya goge zufar data keto mashi kafin yace na rokeka da Allah ka taimaka mani na fita daga wajen nan, wallahi kashe ni zasuyi. Cike da mamaki Alhaji Mai Wada ya kalleshi, har zai masa tambaya sai kuma yayi saurin bud’e bayan motarsa yana fad’in shiga amma ka duk’e kada aganka.
Yana shiga yaja motar suka bar wajen, babu wanda yayi magana har sai da suka iso unguwar da Alhaji Mai Wada yake kafin ya tsaya agefen hanya ya juyo yana fad’in Malan anan nake da zama kai ina zakaje? Tashi Malan Sani yayi yana kallon inda suke, ajiyar zuciya ya saki yana fad’in ai nazo gida Alhaji, nima anan unguwar nake gidana yana can layin baya.
Alhaji Mai Wada yace nima ga gidana can idan bazaka damu ba mu k’arasa akwai abinda nake son na tambayeka. Malan Sani yace Alhaji yanzu dare yayi, kaga har goma ta wuce, nasan Iyalina suna can cikin damuwa dan bana wuce goma awaje, amma muje ka nuna mani gidan ka ni kuma nayi maka alk’awarin gobe da safe zanzo na sameka.
Kallon Malan Sani Alhaji Mai Wada yayi na wani lokaci, tabbas haka kawai yake jin ya yarda dashi, domin beyi kala da macuci ba, magidanci ne sosai yana da fuskar kamala. Ajiyar zuciya yayi yana fad’in kana da gaskiya, nima bani da iyali shiyasa banyi tunanin dare yayi ba, badamuwa muje kaga gidan nawa.
Har bakin gate suka isa kafin suka fito. Kallon Malan Sani yayi yana fad’in sunana Alhaji Hamza Mai Wada, kuma ni mutumin Maiduguri ne, sai dai Iyalina suna zaune akano, banfi wata d’aya dana dawo nan ba dan anyi mani canjin wajen aiki nine shugaban Kwastam na wannan garin.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in ikon Allah, dama kaine naji ana ta magana a wajen aikin mu? Wallahi ko d’azu naji ana maganar sabon shugaban da aka kawo a wajen da naje. Ni sunana Malan Sani, d’an Katsina ne ni, neman kud’i ya kawo ni Lagos nafi shekara goma sha biyu anan, tun ina k’aramun aiki har Allah ya bud’a mani na samu aikin tuki a kamfanin Fanta, da buga-buga har Allah yasa nayi gidan kaina.
Murmushi Alhaji Mai Wada yayi yana fad’in lallai Malan Sani ka zama d’an Lagos, bara na barka kada ashiga hakkin Iyali, tunda gobe asabar babu inda zanje zanyi jiranka dan akwai abinda nake son ji daga gareka.
Malan Sani yace insha Allahu wajen k’arfe goma zanzo nasan zuwa lokacin ka tashi. Dubu biyu Alhaji Mai Wada ya mik’a mashi yana fad’in ga wannan kayi cefane. Malan Sani yace haba Alhaji ka bar su nagode da wannan taimakon ma da kayi mani. Alhaji Mai Wada yace bafa roko na kayi ba, dan haka ka amsa dan Allah. Amsa yayi yana fad’in nagode sosai Allah ya k’ara bud’i.
Sallama yayi masa ya tafi cike da farin ciki, har sai da kwallar farin ciki ta fito masa. Allah mai jink’ai kenan, ko sisi be tashi dasu ba yau, haka ya fita domin neman aiki har dare be samo komai ba sai rayuwarsa da akaso illatawa, gashi yayima matarsa laifi, ya b’oye mata sallamarsa da akayi daga aiki kusan kwana ukku kenan, a nufinsa idan Allah yasa ya samu aiki yau sai kawai ya fad’a mata ya canza wajen aiki, sai gashi bai samu ba kuma ko kud’in abincin safe bedasu, sai gashi Allah ya kawo masa wannan Alhajin ya bashi har dubu biyu bayan taimakonsa da yayi. Lallai mutanan kirki basa k’arewa duniya.
Haka ya nufi gida cike da farin ciki, yaji dad’in samun kud’in nan domin yana tausayin matarsa saboda tana da tsohon ciki.
Ur’s.
Nabeelert Lady????[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770 kayi screen shoot ka tura a whatsapp ta lambar k’asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263*
0⃣4⃣
Da sallama Malan Sani ya shiga gidanshi fuskarsa d’auke da fara’a. Matarsa tana zaune a tsakar gida tana hutawa bayan ta gama shan fatan tsakin da tayi, amsa masa sallamar tayi tana kok’arin tashi tana fad’in sannu da zuwa Malan.
Saurin k’arasowa yayi ya kamata suka zauna yana fad’in haba *HALIMA* kada ki wahalar da kanki kina fama da jikin ki. Murmushi tayi tana fad’in ai bana jin komai. Malan Sani yace ai dai kinyi nauyi kidena yunkurin tashi da sauri haka.