ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 1 to 10

Halima tace Malan hankalina yau ya tashi ganin ka dad’e a waje na d’auka ma ko kunyi tafiya waje mai nisa ne. Murmushi yayi yana fad’in wallahi nima hankalina yana wajenki musamman da nasan ke d’aya ce agidan,  yau nayi wani aiki ne shiyasa ban dawo da wuri ba,  a hanyar dawowa ta kuma na had’u da wani Alhaji har ya rago mani hanya, layin gaban mu yake da zama shine sabon shugaban Kwastam d’in da aka kawo,  to shine fa na tsaya dashi mukayi fira kamar mun san juna. 

Halima tace Allah sarki,  wallahi har hankalina ya kwanta na d’auka wani abun ne ya faru da kai,  musamman da naga yanayin daka fita da safe,  baka tab’a barina babu kud’in cefane ba sai yau,  acikin kwanakin nan sai nake gani kamar akwai abinda yake damun ka. 

Murmushi yayi yana fad’in babu abinda yake damuna kawai kicigaba dayi mani addu’a ina so na canza wannan aikin da nakeyi. Da sauri ta kalleshi tana fad’in ba dai korarka sukayi ba?  Murmushi yayi yana fad’in basu kore ni ba kawai nagaji dayi masu aiki ne saboda basu da lokacin tashi,  kina ganin kullum idan na fita sai dare nake dawowa,  gashi yanzu kinyi nauyi bana son ki haihu ace ina barin ki ke kad’ai,  gara na canza aiki kema kirik’a samun kulawa keda abinda zaki haifa. 

Halima mun dad’e da aure Allah be babu haihuwa ba,  yau gashi Allah ya amshi addu’ar mu kinga dole na tsaya na rik’a kula daku,  duk da kince d’iyar yayarki zata zo cikin sati mai kamawa amma nafison ace nima ina kusa da ke. 

Murmushi tayi tana fad’in to Allah ya zab’a maka wanda yafi wancan alkhairi, Allah ya kareka daga sharrin ko wane aiki da zaka samu. Hannunta ya kamo yana fad’in amin Halimatus Sa’adiya. 

Tashi tayi tana fad’in bara na kawo maka abinci yau dai faten tsaki nayi da wake sai nasa alaiyahu. Malan Sani yace  baiwar Allah,  ubangiji Allah ya biyaki da aljanna,  nasan dai akwai abinci agidan,  amma ban bar na cefane ba ashe kin samu kinyi?  Halima tace d’azu ne *JAMILA* ta aiko mani da d’ari biyun dana ara mata shine nayo mana cefane dasu. 

Malan Sani yace Allah yayi maki albarka,  kinga nima wannan Alhajin ya bani dubu biyu yace nayi cefane,  kuma gobe da safe yana nemana. Halima tace amma mungode masa Allah ya biyashi da alkhairi. Malan Sani yace amin. 

Wucewa ciki tayi ya bita da kallon tausayi,  baya so ya fad’a mata halin da yake ciki yasan halinta da damuwa,  ga tsohon ciki tana dashi idan taji an koresa a aiki zata shiga damuwa,  haka idan ya fad’a mata wasu sun biyoshi d’azu hankalinta bazai kwanta ba. Gara ya cigaba da b’oye mata har Allah yasa ya samu wani aikin. 

*WAYE MALAN SANI?*

   *MALAN SANI HASSAN*,  shine cikekken sunanshi,  d’an asalin garin Katsina ne,  neman kud’i ne ya kawosa Lagos,  tun yana kwana a k’asan gada har ya koma kwana a shago,  yasha wahala sosai arayuwarsa kafin ya samu na kanshi,  kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana yasa duk inda yayi aiki ake sonshi,  a hankali yarik’a tara kud’i har Allah ya bashi ikon siyen fili a unguwar *AGEGE*.  Da kad’an -kad’an ya fara gini,  da a kasuwa yake aiki sai kuma ya fara aiki da masu had’a buhun da ake rufe saman babbar mota dashi (TAMPOL) . 

Da wannan sana’ar sosai yake samu,  yana aikinsa kuma yana cigaba da gininshi,  ya dad’e beyi aure ba sai daga baya yayi aure inda ya auri matarsa Halima,  itama ‘yar Katsina,  gidansu gidan rufin asiri ne,  mahaifinta d’an kasuwa ne,  hakan yasa ta taso cikin tarbiya da sanin rayuwa. 

Bayan da yayi aure sai ya barta a gidan Mahaifiyarsa shi kuma ya koma Lagos,  sai ya samu lokaci yake zuwa wajenta,  sai dai duk wata yana yi mata aike. 

Da haka Allah ya bashi ikon kammala gininshi,  inda yayi d’akuna biyu ciki da falo sai band’aki da kicin sai tsakar gida,  daga gefen tsakar gidan kuma an fitar da wani d’aki sai dai bai fara ginashi ba ya fitar dashi ne saboda zuwa gaba idan ya samu hali ya gina d’akinshi sai ya bar ma Halima wancan koda ta haihu. 

Bayan daya gama komai yaje ya d’auko matarsa suka dawo nan da zama. Sun dad’e basu samu haihuwa ba har Allah ya taimakeshi kamfanin Fanta suka d’aukeshi aikin direba. 

Sosai yayi farin ciki da wannan aikin daya samu musamman daya maido da Iyalinsa Lagos nauyi ya k’aru sai gashi kuma Allah ya taimakeshi da aiki mai kyau. Haka suka cigaba da zaman rufin asirin su yayin da Halima ta fara sana’ar saide-saide a cikin gida har Allah ya basu k’aruwa. 

  *Wannan shine labarin Malan Sani.*

***** ****

Washe gari bayan sun gama karyawa wajen k’arfe goma Malan Sani ya fita domin ya cika alk’awarin da yayi ma Alhaji Mai Wada. Tafiya yake yana tunanin dalilin da yasa Alhaji yake zaune a wannan unguwar,  yasan dai duk wanda aka kawo aiki na Kwastam ana bashi wajen zama bare kuma shi da ya kasance shugaba,  sai gashi yazo wannan unguwar ya zauna. Da wannan tunanin ya isa k’ofar gidan Alhaji Mai Wada.

Yana kwankwasawa Maigadi ya bud’e. Bayan sun gaisa ya fad’a masa yazo wajen Alhaji ne. Murmushi Maigadin yayi yana fad’in Malan Sani ko?  Kai ya d’aga yana mamakin yanda akayi har Alhaji ya fad’ama Maigadi zuwanshi. 

Wajen zama ya nuna mashi yana fad’in ai tun jiya Alhaji ya sanar dani zuwanka,  shiyasa kana zuwa nayi tsammanin kaine,  domin babu wanda yake ma Alhaji sallama da safe haka musamman irin wannan ranar da baya fita aiki da wuri. 

Malan Sani yace Allah sarki,  ai da yake yau asabar ma’aikata kowa yana hutawa ba aiki. Maigadi yace gaskiya banda Alhaji,  gobe ne kawai nasan baya fita wajen aiki,  amma asabar yana fita sai dai bada wuri ba,  sannan baya wuce magriba ya dawo gida sai ya wuce masallaci wajen da suke d’aukar karatun asabar da lahadi. 

Gyara zama Malan Sani yayi yana fad’in gaskiya ban tab’a ganin mutum irin Alhaji ba,  a sanina duk wanda ya kai matsayi irin nashi musamman a aikin Kwastam gidan kud’i da wuya kaga yana rayuwa makamanciyar tashi,  unguwar da yake zaune kad’ai abun mamaki ne,  sai irin yanda yake rayuwa kuma. 

Maigadi yace indai Alhaji ne yanzu ka fara ganin abubuwan mamaki a wajensa,  sam be d’auki duniya da zafi ba,  mutum ne shi mai saukin kai,  ga addini,  kana ganin yawancin masu irin aikinsu yanda suke kasancewa musamman idan akace su kad’ai suka zonan ba tare da Iyalin su ba,  sai kaga sun aikata abinda suka ga dama. 

Ka ganni nan tun farkon zuwan Alhaji garin nan Allah ya had’ani dashi,  yazo unguwar nan yana neman gidan haya mai kyau shine naji wasu suna neman damfararsa,  ina gefe sai banyi magana ba,  asalima sai na tashi nabar wajen dan bana so su fahimci ina wajen kasan yanda rayuwar Lagos take yanzu zasu far maka. 

Bayan da suka gama shima kamar ya san mai suke nufi sai yace masu bara yaje ya dawo,  ganin basu samu nasara ba sai suka wuce suka kyaleshi. Har yashiga mota yayi hanyar fita na tarbeshi,  bayan ya fito na fad’a masa gaskiya abinda wad’an can mutanan suke da niyar yi masa. Murmushi yayi yace mani ai ya fahimcesu shiyasa ya kyalesu. 

Anan yake fad’a mani abinda yakeso,  an bashi gida acan wajen aikinsu amma yafiso ya shigo cikin mutane ya zauna kafin ya gama gane komai na garin sai ya canza wajen zama. Jin haka yasa nayi masa jagora wajen mai wannan gidan,  domin wani ne ya zauna daya tashi kuma bakowa ciki. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button