ALKALI NE Page 11 to 20

Ganin Alhaji ya damu yasa Mr. Kallah yace ya kwantar da hankalinsa gara aje kotu za’afi saurin gano wanda ya d’auki kayan domin hukuma zata shigo ciki. Jin haka yasa Alhaji yaji hankalinsa ya kwanta domin shima yafi buk’atar hukuma tashigo ciki. Haka sukayi sallama ya tafi.
Yana barin wajen suka kwashe da dariya. Alhaji Marusa yace ai na fad’a maka, bani da kyau Mr. Kallah, dama can kyaleshi nayi amma yanzu yashigo hannu na, sai na sashi yayi dana sanin zuwanshi Lagos, haka kawai muna zaune lafiya wani yazo ya nemi tada mana hankali, wallahi rabon dana shiga damuwa har na manta sai zuwan wannan mutumin.
Mr. Kallah yace baka da kyau mutumina, wallahi banji tausayinsa ba, domin tun farko naso na d’orashi a hanya ya nuna mani shi mai gaskiya ne, yo yanzu waye yake wani aiki da gaskiya, ai yanda kazo kaga kowa da bindi kaima nemi ko tsumma ne ka d’aura domin agudu tare a tsira tare, wannan matsayin fa ba daga gidanku kazo dashi ba, anan ka sameshi kuma nan zaka barshi, ka bari kaci wasu ma suci amma ya tsaya yana nuna mana shi mai gaskiya ne, zaiga gaskiya kuwa Allah ya kaimu aje kotu gobe zai gane baida wayau.
Alhaji Marusa yace baka ga gidan daya gina bane, yasan beda gaskiya shiyasa ko walimar tarewa beyi ba. Mr. Kallah yace ai tunda kace mani a surelere yayi gidan nasan akwai wata ak’asa. Alhaji Marusa yace ka barshi da gidan zamu kamashi ai, yau da dare su *Peter* zasuyi aikinsu. Mr. Kallah yace kai dan Allah? Alhaji Marusa yace wallahi kuwa, ai kaidai kasa ido kayi kallo. Dariya suka kwashe da ita.
Ur’s.
Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣0⃣
A daren ranar Alhaji Maiwada kasa runtsawa yayi, Ummun Ra’eez ce take kwantar masa da hankali, sosai hankalinsa ya tashi domin jikinsa yayi sanyi, yana ji aransa kamar wani mugun abu ne zai faru, yayi mamaki da akace wai masu d’aukar kaya basu dauka duka ba, bayan yasan sai da aka gama komai suka tafi kafin ya bar wajen.
Haka yayo alwala ya fara nafila yana neman tsarin Allah daga kowane sharri da yake tunkaroshi. Bayan ya idar ya bud’e kur’ani ya fara karatu har sai da aka kira sallar farko kafin ya tashi ya yo alwala yayi nafila sannan ya fita zuwa masallaci.
Beshigo gida ba sai da gari yayi haske, yana shigowa wanka kawai yayi ya kwanta anan bacci ya d’aukeshi saboda gajiya. Sai k’arfe takwas ya farka dalilin wayarsa da aka kira. Sunan Adebayo ya gani, yana d’auka bayan sun gaisa Adebayo ya fad’a masa an aiko da takardar sammaci daga kotu k’arfe goma za’a shiga. Alhaji yace shikenan sai na fito.
Band’aki yashi bayan ya fito ya shirya sannan ya fito falo. Bayan sun gaisa da Ladi ta shige ciki yayin da Ummu ta zuba masa abinci. Ruwan shayi kawai ya sha yace ya koshi. Zama Ummu tayi tana fad’in haba Abbun Ra’eez, ka sani damuwa bata haifar da komai sai ciwo, ka yi addu’a Allah bazai barka haka ba, idan kuma kaga wani abu ya faru da kai kada kace addu’ar ka bata karb’u ba, kasa aranka Allah yana so ya jarabceka ne kawai, kuma kasan muhimmancin yadda da k’addara.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in naji dad’in maganarki, kuma tasa zuciyata tayi sanyi haka kuma kin k’ara mani kwarin guiwa, bakomai, duk abinda ya faru zan d’aukeshi amatsayin k’addarata, domin bawa baya zama haka dole sai da jarabawa.
Murmushi Ummu tayi ta zuba masa abinci ta fara bashi abaki tana kwantar masa da hankali, a haka yarika amsa har yaci sosai, yaji dad’in yanda Ummu tayi masa, shiyasa akoda yaushe yake k’ara sonta domin tasan yanda ake kula da miji.
Bayan ya gama ta rakashi har k’ofar gida inda suka gaisa da Malan Sani kafin tayi masa fatan alkhairi ta koma ciki. Amsar jakarsa Malan Sani yayi yana fad’in Alhaji yau ka makara. Murmushi yayi ya shiga mota bece komai ba.
Bayan sun fita ya kalli Malan Sani yana fad’in babbar kotu zamuje. Da sauri Malan Sani ya kalleshi yana fad’in maganar ta tabbata kenan?…….. ……. Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Malan Sani yace ikon Allah, Alhaji wannan abu akwai alamar tambaya fa.
Alhaji yace Malan Sani kawai mu barma Allah komai, jikina yana bani akwai abinda suka shirya, dan haka zan d’auki duk wani abu da zai taso. Tausayin Alhaji ne ya kama Malan Sani, yasan wani kullin ne suke so suyi mashi. Malan Sani yace Allah ya saukaka koma menene. Alhaji yace amin.
****
Bayan sun isa kotu da Mr. Kallah ya fara had’uwa, wucewa yayi wajensa suka gaisa kafin ya jashi suka nufi wajen motarsa. Kallon Alhaji yayi yana fad’in kayi hak’uri da duk abinda zai faru, nayi magana da kwamishinan ‘yan sanda yace zasuyi bincike dole a gano inda aka b’oye kayan, dan haka zasuzo suyi bincike duk inda ya kamata, Adebayo ya bani sunayen mutanan da suka tsaya akan kaya tun daga kanka har k’asa, kuma kowa za’a bincikesa, dan haka kada ka damu idan suka zo bincike, hakan ne kawai zaisa a gano gaskiya.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in babu damuwa, suzo zan basu damar yin bincike duk inda suke so, nima nafison hukuma suyi bincike domin na kasa gano komai.
Ganin motar Alkali yasa sukayi saurin nufar cikin kotun. Haka kowa yashiga ciki ya samu waje ya zauna suna jiran shigowar Alkali.
Brr. Barau ne yashigo bayansa Alhaji Marusa yana bayansa suna magana a hankali, wajen zamansa ya wuce Alhaji Marusa ya zauna gefen Mr. Kallah. Alkali yana shigowa kowa ya tashi, bayan ya zauna kowa ya zauna.
Gaba d’aya kotun tayi shiru ana jiran a fara. Magatakarda ne ya tashi ya fara karanto k’ara kamar haka…. *Yau sha biyu ga watan janairu shekara ta dubu biyu, (12/1/2000), wannan kotu zata saurari k’arar da Alhaji Marusa ya shigar akan tuhumar hukumar Kwastam da salwantar masa da kayansa na mukudan kud’i bayan sun iso a jirgin ruwa, wanda aka rik’esu har tsawon kwana d’aya da yini guda kafin aka sake su, sai dai aciki babu wasu daga cikin kayan da suka iso wanda ya tabbatar da zuwan su kuma an dubasu kafin a kaisu wajenshi aka cire wasu daga ciki. Alhaji Marusa yana rokon wannan kotu mai alfarma data kwato masa hakkinsa a wajen hukumar kwastam*.
Risnawa yayi ya mik’a takardar wajen Alkali. Bayan daya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari’ar su fara.
Brr. Barau ne ya tashi yana fad’in sunana Brr. Nuhu Barau, nine lauyen da yake kare wanda yake k’ara. Alkali yace ina lauyen da zai kare wad’an da ake k’ara? Tashi Alhaji Maiwada yayi yana fad’in bamu d’auki lauya ba domin yau da safe takardar sammacin ta same mu, nine zan kare hukumar mu.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in Brr. Barau zaka iya farawa. Risnawa yayi kafin ya fito yana fad’in ina so nayima shugaban kwanstam wasu tambayoyi. Alkali yace an baka dama.
Bayan Alhaji ya fito Brr. Barau yace kotu zata so taji sunanka da kuma matsayin ka.
Sunana Alhaji Hamza Maiwada, nine shugaban kwastam.
Brr. Barau yace kaji bayanin da aka karanta yanzu, shin ko zaka iya yima kotu k’arin haske akan abinda ake tuhumar hukumar ku dashi? Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad’in tabbas nine wanda ya duba kayan Alhaji Marusa, kuma sai da na tabbatar da komai lafiya kafin nasa hannu aka gama komai sannan muka sakar masu kayan suka d’auka, agaban mu suka d’auki kayan babu abinda aka rage kafin muka bar wajen.