ALKALI NE Page 11 to 20

Brr. Barau.. Amma Alhaji Marusa yace kafitar da kwalaye biyu acikin kayansa kace sun sab’a doka, kuma gashi kai kace ba’afitar da komai ba? Alhaji yace ina nufin acikin kayansa da aka duba wanda nasa hannu babu abinda aka rage, wad’an da aka fitar kuma dama bandasu acikin wad’an da nasa hannu, haka ne nasa acire kwalaye biyu acikin kayansa domin sun sab’a doka.
Murmushi Brr. Barau yayi yana fad’in tun bayan zuwanka garin nan Alhaji Marusa ya fara fuskantar matsala da hukumar ku, kuma kowa yasan irin dad’ewar da yayi yana kasuwanci a k’ashashen waje, akwanakin baya ma sai da kayansa suka samu matsala, shin ko akwai wata matsala da take tsakanin ku ne? Girgiza kai Alhaji yayi yana fad’in nifa ma’aikacin al’umma ne, su nake ma aiki tare da k’asata, bani da wata matsala tsakanina da Alhaji Marusa, kamar yanda kowa yake shigo da kaya muke dubawa shima haka muke duba nashi, sai dai kawai kasan kowa da tsarin aikinsa, to nima haka nawa tsarin yake, matuk’ar kaya suka iso dole sai mun tabbatar da ingancin su kafin musa hannu a sake su, matuk’ar muka kama kayan da suka sab’a k’a’ida dole ne mu ciresu, bayan wannan ni banida wata matsala da kowa.
Brr. Barau… Amma yace kayan kwannasu d’aya da yini guda, baka tunanin kafin ku kammala duba kayan aka samu wani ya d’auke wad’an da suka b’ace? Alhaji yace babu wanda ya tsaya akan kayan, bayan da muka duba na farko haka kowa ya tafi sai washe gari aka k’arasa duba sauran, sai dai kasan zuciya bata da k’ashi, Allah ne kad’ai yasan gaskiya, tun bayan da aka fad’a mani wannan matsalar na tara duk wad’an da sukayi aiki aranar muka tattauna, sai dai maganar d’aya ce, babu wanda yasan inda suke, dan haka ina rokon wannan kotu mai albarka data bada izini hukuma tayi bincike akan wannan matsalar hakan zaifi mana sauki.
Jinjina kai Brr. Barau yayi ya juya yana fad’in ya mai shari’a, ina rokon wannna kotu mai albakar, kamar yanda Alhaji Maiwada ya nemi alfarma a d’aga wannan shari’a domin hukuma ta samu damar yin bincike hakan zaisa a samu cikakkar sheda. Nagode.
Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d’ago yana fad’in wannan kotu ta bama hukumar ‘yan sanda dama da su tsananta bincike zuwa nan da kwana biyu za’a dawo kotu domin acigaba da gabatar da wannan shari’a. Tebur ya buga gaba d’aya akace kottttt .
Gaba d’aya kowa ya fita yana jajanta abinda ya faru, yayin da wasu suke tausayin Alhaji Maiwada domin sun san halinsa.
Bayan da suka fito Mr. Kallah yaja Alhaji Maiwada suka nufi wajen motar kwamishinan ‘yan sanda wanda be dad’e da zuwa ba saboda wayar da sukayi da Mr. Kallah.
Bayan sun gama gaisawa Mr. Kallah yayi masa bayanin halin da ake ciki akan abinda Alkali yace. Kwamishina yace kada ka damu Alhaji zansa yarana suyi bincike, ina so ku bamu had’in kai ta haka ne zamu ji dad’in yin aikin. Alhaji yace insha Allahu bazaka samu matsala da mu ba.
Haka suka gama tattaunawa kafin sukayi sallama ya shiga mota suka nufi ofis. A hanya Malan Sani sai kwantar ma Alhaji da hankaki yakeyi har suka isa.
***
A can ofis kuwa hankalinsa atashe yake, Adebayo da Umar ne kawai hankalinsu yake kwance domin sun san bakin zaren, Alhaji ya sake tara kowa ya rokesu akan idan akwai wanda yake dasa hannu akan wannan abun ya taimaki mutane ya fito da kanshi kafin hukuma ta ganoshi, domin duk wanda aka gano shi kad’ai za’a kama.
Nan kowa yace beda masaniya akan abun. Haka dai taron ya tashi babu wani labari. Haka Alhaji ya wuce ofis jiki a sanyaye. Yinin ranar haka yayishi jiki babu kwari.
Bayan anyi sallar azahar sai ga DPO da yaranshi sun iso. Haka suka fara nasu binciken cikin kwanciyar hankali. Duk ma’aikatan da sukayi aiki aranar sai da aka d’auki komai nasu tun daga kwatancen gidansu da bayanin bankinsu. Bayan da suka gama sukayi sallama da Alhaji sukace akowane lokaci za’a iya ganinsu a gidan mutum. Godiya Alhaji yayi masu suka tafi.
Sunayin la’asar ya tafi gida domin baya jin dad’in jikinsa. Malan Sani bayan ya ajeshi yace zaisa Malamin unguwarsu ayi addu’a. Alhaji yace nagode sosai Malan Sani, bara na baka kudin da za’a basu sadaka. Malan Sani yace wallahi bazan amshi ko sisi ba, nine nayi niya dan haka ka barni kawai. Murmushi Alhaji yayi yace nagode agaishe da Rumaisa.
****
Ana gobe za’a koma kotu da misalin k’arfe bakwai bayan anyi sallar magriba Alhaji yana zaune a tsakar gida shida Malan Sani da Madu suna fira kawai sukaji k’ararrawa. Da sauri Madu ya tashi ya nufi k’ofa, sai da ya lek’a kafin yayi saurin bud’ewa.
Tashi Alhaji yayi tsaye ganin ‘yan sanda, lokaci guda yaji gabanshi ya faad’i, duk da yasan suna zuwa gidaje suna bincike amma haka kawai yaji gabansa ya faad’i.
Bayan sun gama gaisawa DPO yace Alhaji sai dai kayi hak’uri yau gamu munzo bincike yazo kan ka. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in haba ai bakomai, ai haka mukeso domin ta haka ne za’a gano gaskiya. Bismilla ku shigo, bara nayima Iyalina magana. DPO yace bakomai kayi masu magana.
Suna tsaye suna k’arema gidan Alhaji kallo ya fito yana fad’a masu su shigo. Suna shiga suka iske Ummu da Ladi a falo sanye da hijabi suna zaune. Gaishe dasu sukayi Alhaji ya samu waje ya zauna yana fad’in DPO kushiga ko ina abud’e yake. Jinjina kai yayi kafin yasa yaranshi suka fara bincike.
Tunda suka haura sama Ummu tasa kuka, rungumeta Alhaji yayi yana fad’in kidena kuka, ina da gaskiya ta dan haka su shiga duk inda suke so. Ummu tace yanzu har d’akin kwanan mu sai sun bincika mana? Alhaji yace daga binciken fa shikenan, bana so kisa damuwa aranki.
Suna nan zaune kusan mintuna goma sai gasu sun sauko, DPO yace zamu shiga kicin Alhaji. Jinjina kai yayi ya nuna masu hanyar kicin d’in. Bayan sun gama duba komai suka fito. DPO yace Alhaji babu abinda muka samu acikin gidan ka, sai dai zamu duba can waje zuwa bayan gidan ka dan kamar naga akwai ginin da kakeyi acan baya wanda ba’a kammala ba.
Alhaji yace akwaishi muje ku duba. Cire Ummu yayi ajikinshi yabi bayansu. Suna fita Malan Sani yace Alhaji mujirasu anan kada suga kamar muna binsu. Kai Alhaji ya jinjina ya samu waje ya zauna.
Kusan mintuna ashirin sai ga wani d’an sanda ya fito da gudu, Alhaji yana ganinshi yayi saurin tashi tsaye. Yana zuwa yace Alhaji Oga yana son ganinka. Jiki a sanyaye Alhaji da Malan Sani hada Madu suka bi bayan shi.
Tun kafin su k’arasa suke hango kaya daga cikin wani d’aki da aka bud’e. Da sassarfa Alhaji ya k’arasa wajen. Turus ya tsaya yana kallon DPO. Girgiza kai DPO yayi yana fad’in meyasa haka Alhaji? Meyasa ka zab’i ka bamu wahala bayan kasan komai? Salati kawai Alhaji yakeyi jikinsa yana rawa, idan ba gizo idanuwansa suke masa ba kaya yake gani a cikin d’akin da yake gabanshi kuma kayan da ake tuhumarsu akansu, sai dai kayan da suke wajen basu kai rabin wanda akace sun b’ace ba, da alamu ba duka bane a d’akin.
Da sauri Malan Sani ya rik’e Alhaji yana fad’in wallahi Yallab’ai bamu da masaniya akan wannan kayan, sai dai idan wani ne ya shigo dasu.
Murmushi DPO yayi yana fad’in meye matsayinka awajen Alhaji? Malan Sani yace direbansa ne. Dafashi DPO yayi yana fad’in Malan Direba ka tsaya amatsayinka, wannan mune muke da ikon yin bincike, dan haka kaja bakinka kayi shiru domin duk abinda zaka fad’a zai iya zama hujja akan ka.