ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Kallon Alhaji yayi yana fad’in bincike ya k’are Alhaji,  dan haka zamu tafi da kai kafin gobe akoma kotu,  sai dai na lura kamar kayi amfani da wasu kayan saboda yanda na samu labari kayan sunfi haka yawa,  amma dai koma meye zamuji daga bakin ka gobe. Shiru Alhaji yayi ya kasa magana. DPO yasa mai d’aukar hoto ya d’auki komai kafin su tafi. 

Kallon yaransa yayi yana fad’in ku taho dashi. Alhaji yace zan iya sallama da Iyali na?  Wani d’an sanda yace babu inda zakaje. DPO yace barshi ka rakashi yaje yayi magana dasu. Bayansa Malan Sani yabi suka wuce jiki a sanyaye. 

Tunda Ummun Ra’eez taga Alhaji taji gabanta ya faad’i,  saurin k’arasowa tayi tana kuka. Rungumeta Alhaji yayi shima ya saki kuka. Sun dad’e ahaka kafin ya goge idonshi yana fad’in kiyi mani addu’a Ummun Ra’eez,  abinda nake tsoro ya tabbata,  Allah ne kad’ai zai fitar dani,  sun samu kayan a ginin Ra’eez wanda bansan da suba. 

Hannu tasa ta goge masa fuskarsa tana fad’in wallahi nasan k’arya ne,  nafi kowa saninka,  baka tab’a ciyar damu da haram ba,  kuma Allah zai fitar da kai. Gyaran murya d’an sandan yayi yana fad’in Alhaji kana b’ata mana lokaci. 

Cireta yayi daga jikinsa yana fad’in kada kiyi kuka,  kiyi mani addu’a gobe zan dawo. Kai ta jinjina tana hawaye tace Allah ya tsare mani kai. Ladi ma kuka takeyi tana masa addu’a. Haka suka tasa keyarsa Malan Sani da Madu sai kuka sukeyi. Suna kallo suka tafi dashi yayin da aka sa kayan amota aka tafi dasu. 

****

*Washe gari a kotu.*

Ur’s. 

Nabeelert Lady

[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne,  Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa,  idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar.  08028525263.*

1⃣1⃣

Zaune Alhaji Marusa da  Mr. Kallah suke a ofis d’in Brr. Barau. Dariya Alhaji Marusa yayi yana fad’in Mr. Kallah ai na fad’a maka bani da kyau,  yanzu Alhaji Maiwada zai san ya ja dani,  babu wanda ya isa yazo ya kawo mani matsala akan kasuwancina,  domin bana had’a kud’i da komai,  saboda ina samun had’in kai da ma’aikatan Lagos yasa ban damu da shigo da kaya ta bodar portcourt ba,  amma saboda shi sai da na koma ina shigo da wasu kayan ta can saboda ya kasa ya tsare,  duk da ba huruminsa bane diba kaya amma sai yayi hakan,  ya tsaya ofis yayi aikinsa bazeyi ba ya koma shine yake duba duk kayan da aka shigo dasu,  wanda yake kula da b’angaren duba kaya ya zama hoto,  kuma saboda raini yafi tsayawa ya duba kayana fiye dana kowa,  amma ai yanzu nayi maganinsa,  Mr. Kallah kayi mana wannan taimakon a saukeshi daga wannan matsayin,  naji dad’i da ya kasance kana hutu abun ya faru,  tunda litinin zaka koma Abuja idan kaje ofis inaso a aiko masa da takardar rage matsayi saboda an kamasa da babban laifi. 

Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad’in Alhaji Marusa baka da kyau,  kasan nine shugaban kwastam na k’asa baki d’aya,  duk da ina goyon bayanka dole wani abun sai an duba saboda idanuwan mutane,  ba kai kad’ai ba,  manya da yawa nine nake tsaya masu saboda nidai inason kud’i,  duk wanda zai yaga mani dole na bashi goyon baya,  amma duk da haka muna kimantawa saboda mu kauda hankulan mutane,  hutun dana d’auka litinin yake k’arewa,  tunda yau za’a yanke hukunci bayan na koma zamu tattauna akan abinda yayi. 

Brr. Barau yace rankaidad’e ai ko da abinda kotu zata yanka masa aka barshi ya isheshi ya tsani aikin kwastam,  domin miliyoyin kud’i zai biya,  inaji ma kila ya saida gidanshi saboda Kwamishna yace da suka binciki bankinsa babu wasu kud’i da yawa aciki duk ya zuba su a gini, domin wannan binciken sai da suka had’a da EFCC saboda babban abu ne,  kaga kuwa dole ya sayar da wannan makeken gidan ya biya kud’in da kotu zata yanka masa. 

Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad’in kuma nine nan zan sayi gidan,  sai dai banzan bari yasan haka ba,  zan aika wani yaje ya siya mani shi. Dariya sukasa gaba d’aya. Brr. Barau yace ina ganin lokacin shiga yayi. Mr. Kallah yace bara na fara fita kada azargi wani abu. 

***

Duk girman kotun sai da ta cika da jama’a,  domin tun jiya ake fad’ar an kama shugaban kwastam na Lagos da laifin satar kayan Alhaji Marusa,  wannan dalilin ne yaja hankulan mutane da yawa suka kawo ziyara a kotun,  hada manyan mutane sai da suka ziyarci kotun saboda suji abinda za’ayi,  ‘yan jarida kuwa sun cika kotun kowa yana jira ya samu abun k’araswa. 

Bayan da Alkali yashigo kowa ya natsu. ‘Yan sanda ne suka shigo da Alhaji Maiwada,  kowa kallonsa yakeyi yayin da Alhaji Maiwada yake ta addu’a,  gaba d’aya jikinsa rawa yake masa,  idanuwansa a k’asa ko kallon mutanan bayayi.

 Ummun Ra’eez kasa zuwa kotun tayi,  domin bazata iya ganin ana cima mijinta mutunci ba. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur kawai suka zo kotun,  shima a safiyar yau ya biyo jirgi saboda tun a jiya Ummun Ra’eez tayi masa waya. Maman Rumaisa da Ladi sune suke ta bama Ummun Ra’eez hakuri. 

Ma’aikatan ofis d’insu Alhaji Maiwada da yawa sun zubar masa da kwallah musamnan wad’an da suke jin dad’insa. Adebayo,  Umar da sauran mabiyansu sunfi kowa murna,  sai dai a fuskarsu suna nuna jimami. 

Bayan da Magatakarda ya sake karanto k’arar Alkali yace  a fara gabatar da shari’ar. Tashi Brr. Barau yayi yana fad’in inaso kotu ta bani izini na kira Alhaji Maiwada domin nayi masa wasu tambayoyi. Alkali yace kotu ta baka dama. 

Bayan ya fito Brr. Barau ya k’arasa wajensa yana fad’in Alhaji inaso kayima kotu cikekken bayani akan yanda aka samu kayan Alhaji Marusa wanda ake tuhumar hukumar ku dasu a gidan ka. 

Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad’in tabbas an samu kayansa a gida na,  amma maganar gaskiya bani da masaniyar zamansu agida na,  sai dai idan saka mani akayi,  domin duka kwali ukku ne aka samu a gidana. 

Murmushi Brr. Barau yayi yana fad’in Alhaji kada ka bama kotu wahala,  ‘Yan sanda sun tabbatar mana a cikin d’akin da yake bayan gidanka aka samesu,  kuma tambayar anan itace,  Alhaji Marusa ya bamu iya yawan kayansa da suka b’ace hada kud’ad’en su,  sai dai kuma kayan da aka samu a wajenka basu kai kwatar kud’insa ba,  haka kuma ko rabin wad’an da suka b’ace basu kai ba,  domin lokacin da aka duba gidanka an iske saura kad’an ka rage,  shine muke so muji ina ka kai sauran?  Idan kuma siyarwa kayi to ina kud’in suke,  domin a binciken asusunka da akayi kud’in da suke ciki ba wasu masu yawa bane,  shine muke so kayi mana bayani.

Wani lauya ne ya tashi yana fad’in ya Mai shari’a  nine lauyen da nake kare wanda ake k’ara. Sunana Brr. *Kamal Auwal*. Kai Alkali ya jinjina yana fad’in Brr. Kamal akwai maganar da kake da ita ne?  Risnawa yayi yana fad’in ya mai shari’a ya kamata lauyen da yake kare wanda yake k’ara ya sassauta maganarsa akan wanda ake k’ara,  be kamata yarik’a masa wasu tambayoyin ba. Nagode. 

Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in wanda ake tuhuma ba zarginsa ake ba domin anga zahiri a gidanshi,  dan haka dole ya amsa tambayar da akayi masa saboda shi kad’ai ne zai iya warware mana wannan matsalar. 

Murmushi Brr. Barau yayi yana fad’in Alhaji kotu tana sauraron ka. Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad’in kamar yanda nace bansan da zaman kayan Alhaji Marusa agidana ba,  haka zalika bansan ina sauran suke ba,  kuma ni ban siyar da komai ba saboda ban tab’a zaluntar kowa akan kayansa ba,  iyakar abinda na sani kenan. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button