ALKALI NE Page 11 to 20

Juyowa Brr. Barau yayi yana fad’in ya mai shari’a inaso wannan kotu tayi duba da abubuwa guda biyu da zan gabatar mata yanzu, wanda sun isa su tabbatar ma kotu lallai Alhaji Maiwada shine ya d’auki wad’annan kaya.
Na farko Alhaji Maiwada ya gina katafaren gida na makudan kud’i, kuma babu wanda yasan lokacin daya fara ginin da lokacin da aka gama, sannan be gayyaci kowa ba alokacin da zai tare agidansa, haka zalika Alhaji Maiwada baya son kowa yasan inda gidansa yake acikin ma’aikatansa gaba d’aya, duk wanda yake son ganinsa sai dai su had’u a ofis, domin baya bari aje gidansa.
Abu na biyu alokacin da aka kawo kayan Alhaji Marusa bayan Alhaji da ma’aikatan da suke aiki aranar sun gama duba kayan aka barshi akan sai washe gari zasu k’arasa, bayan da kowa ya tafi Alhaji Maiwada shine wanda aka bari na k’arshen tafiya, wanda maigadi ya tabbatar mana da cewar ya dad’e kafin ya tafi, kuma kafin ya tafi sai da ya aikeshi ya d’auko masa wasu takardu wanda hakan ya d’aukeshi kusan mintuna ashirin kafin ya dawo, da wannan ne Alhaji Maiwada yayi amfani domin ya fitar da abinda yakeso wanda shine yasan ta yanda ya fitar da kayan a cikin lokaci k’ankani.
Da wannan nake rokon kotu data kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa. Nagode.
Bayan Alkali ya gama rubutu yace lauyen da yake kare wanda ake k’ara ko kana da abinda zakace? Tashi Brr. Kamal yayi yana fad’in ina dashi ya mai shari’a, ina so zanyima Mai gadin da yayi aiki aranar da aka kawo kayan Alhaji Marusa tambaya. Kotu ta baka dama.
Matsowa yayi kusa da Maigadin bayan ya fito yana fad’in ko zaka iya fad’a ma kotu wajen da Alhaji ya aike ka d’auko takardun da kace? Maigadi yace a cikin ofis d’in da ake aje kaya ne inda suka zauna shine ya mantasu acan sai yace na d’auko masa.
Brr. Kamal… Idan na fahimceka Kenan shi Alhaji ya fito wajen motarsa, daya tuna yayi mantuwa shine ya aike ka?
Kai Maigadi ya jinjina yana fad’in yashiga mota ma sai ya aike ni, to kafin na d’auko masa na d’an jima saboda ban gansu a inda ya fad’a mani ba.
Jinjina kai Brr. Kamal yayi yana fad’in ya mai shari’a inaso kotu tayi duba da abinda Maigadi ya fad’a, Brr. Barau ya ce Maigadi ya fad’a masu Alhaji ya aikesa bayan kuma Alhaji yana cikin mota, hakan zai nuna mana cewar Alhaji baya cikin d’akin da kayan suke taya zai d’aukosu ya fita dasu bayan Maigadi yana cikin d’akin? Inaso wannan kotu mai albarka da tayi duba da wannan sheda da aka gabatar, duk da an samu kaya a gidan Alhaji ba shine yake nuna Alhaji ne ya d’aukesu ba, nagode.
Tashi Brr. Barau yayi yana fad’in ya mai shari’a wannan hujja da abokin aikina ya kawo bata isa ta kare wanda ake k’ara ba, domin kowa ya sheda an samu wad’an nan kaya agidan Alhaji, idan akace yana cikin mota ya aiki mai gadi mai yasa da Maigadin yashiga baiga takardun a inda Alhaji yayi masa kwatance ba? Dama yana da wata manufa shiyasa ya barosu kuma ya aiki Maigadi domin yasan kafin ya gansu ya gama abinda yakeyi.
Ina rokon wannan kotu data yi amfani da shedun da aka gabatar mata domin ta kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa, domin ga kwararun hujjoji nan mun gabatar. Nagode.
Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d’ago kai yana fad’in Alhaji Maiwada kana da ja akan abinda aka gabatar? Girgiza kai Alhaji yayi wasu hawayen bakin ciki suka zubo masa, hannu yasa ya goge idonshi yana fad’in iya gaskiyata na fad’a, bani da sauran ja akan abinda aka gabatar ma kotu Allah ne kad’ai yasan gaskiya.
Gaba d’aya kotun akayi shiru, mutane da yawa jikinsu yayi sanyi akan maganar Alhaji, su Malan Sani sai kuka sukeyi.
Bayan Alkali ya gama rubutu ya d’ago yana fad’in abisa kwararun shedu da aka gabatar ma kotu, kuma wanda ake tuhuma ya kasa kare kanshi a gaban kotu, wannan ya tabbatar mana cewar Alhaji Hamza Maiwada yana dasa hannu acikin b’acewar wad’annan kaya, inda wasu daga ciki suka salwanta.
Abisa adalci irin na wannan kotu Alhaji Maiwada zai biya Alhaji Marusa duk abinda ya kashe akan kayan da suka b’ace, tun daga siyosu, kud’in kawosu zuwa nan, sauran da suka rage kuma za’a mik’asu ga Alhaji Marusa, ‘Yan sanda da hukumar bincike zaku tsaya a kammala komai, domin a tabbatar Alhaji Maiwada ya biya komai daya b’ace, hukumar kwastam sai ku d’auki mataki domin akiyaye sake faruwar irin wannan.
Tebur ya buga gaba d’aya akace kotttt!.
Duk’awa Alhaji yayi ya d’ora kanshi saman katakon da yake tsaye wasu zafafan hawaye suna zubo masa. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur ne kad’ai suka k’araso wajenshi.
Kamoshi Alhaji Mansur yayi yana lallashinsa. Haka suka fito ‘yan sanda suna binsu abaya. Mr. Kallah ne yayi magana da DPO tare da mai jagorantar cibiyar bincike akan su bar Alhaji ya koma gida zasuyi magana da Kwamishna dan ayi komai cikin hankali kwance tunda Alhaji babban mutum ne.
Haka Mr. Kallah ya samu su Alhaji Mansur yayi masu bayani, sosai sukaji dad’in abinda yayi masu, godiya sukayi mashi sannan suka k’arasa wajen Brr. Kamal sukayi masa godiya akan abinda yayi masu domin sun san basu d’aukeshi ba amma ya tashi domin ya kare Alhaji.
Brr. Kamal yace haba bakomai, wallahi naji tausayinsa hakan yasa na tashi domin na kareshi, rashin hujjoji yasa aka kadamu, amma bakomai Allah yana gani.
Godiya sukayi masa suka wuce gida. Duk yanda ‘yan jarida suka so suyima Alhaji tambaya hakan be samu ba dole suka hakura.
***
Zaune suke a falo Alhaji yana kwance saman doguwar kujera zazzab’i ya rufeshi. Alhaji Mansur ne yasa Ladi ta had’o masa shayi dan Ummu tana zaune kusa dashi sai kuka takeyi, sosai hankalinta ya tashi da abinda aka fad’a mata.
Malan Sani yana gefe ya kalli Alhaji Mansur yana fad’in Alhaji yanzu shikenan haka zamu kyalesu an yanke ma Alhaji hukuncin zalunci? Alhaji Mansur yace Malan Sani najeriyar kenan, gashi dai munsan sharri ne aka kulla masa amma babu yanda zamuyi, domin sun fimu hujja, kasan ita kotu da hujja take amfani, duk wasu hujjoji da zasu tabbatar Alhaji ne ya d’auki kayan Alhaji Marusa sun gabatar dasu, babban abinda yasa suka k’ara cin galaba akan Alhaji shine samun kayan a gidanshi, amma dan sun gabatar da irin ginin da yayi wannan ba hujja bace, sunyi amfani da hakan ne dan su k’ara ma hujjarsu girma, amma bakomai, akwai Allah, kuma shi kad’ai ne zai bayyana gaskiya.
Ummun Ra’eez tace wallahi na tsani garin nan, bana son wannan aikin na Abbun Ra’eez, tunda abun ya fara zuwa da haka dan Allah Abban Labiba kasa baki ya aje masu aikin su yazo mu koma Kano mucigaba da rayuwar mu, sun fara neman kassarashi ta hanyar dukiyarsa da goga masa bakin fenti, nan gaba wallahi rayuwarsa zasu nema, bani da kowa saishi, idan suka rabani dashi ina zansa kaina.
Rungumeta Maman Rumaisa tayi itama tana kuka. Alhaji Mansur da jikinsa yayi sanyi ya kamo Alhaji Maiwada yana mik’a masa kofin shayin.
Amsa yayi ya shanye dan yunwa yakeji saboda beci komai ba. Komawa yayi ya kwanta yana runtse idonshi. Alhaji Mansur ne ya kamashi suka mik’e tsaye, kallon su Malan Sani yayi yana fad’in bara nashigar dashi ciki nayi waya da likitansa zaizo ya dubashi yana buk’atar hutu saboda jininsa yana iya hawa.
Tashi Ummu tayi tana fad’in ko zaiyi wanka? Alhaji Mansur yace aa abarsa yayi bacci. Ciki suka nufa wani d’aki da yake ak’asa. Bayan sun kwantar dashi wayar Alhaji tayi k’ara, Alhaji Mansur ne ya duba sai ya ga likitan ne, fita yayi yana fad’in bara nashigo dashi.