ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Bayan ya gama dubashi ya bashi magunguna yayi masa allurar bacci,  cikin lokaci kad’an bacci ya d’aukeshi. Fitowa sukayi likita yana fad’in jininsa ya hau,  dole ya samu bacci mai yawa hakan zai taimaka masa. Godiya sukayi masa ya tafi. 

Kallon Ummu Alhaji Mansur yayi yana fad’in ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru,  abarshi ya samu hutu zuwa gobe zamuyi maganar. Ummu tace mungode Abban Labiba,  kashiga ga d’akin baki can ka huta Ladi ta kai maka abinci. Jinjina kai yayi ya nufi wajen Malan Sani. 

Bayan yayi masa bayanin da likita yayi masa Malan Sani yace shikenan abari zuwa goben sai muji abinda za’a yanke. Sallama sukayi masu suka tafi. Alhaji Mansur ya nufi d’akin da aka saukeshi. 

***

Dariya ce take fitowa daga harabar gidan Alhaji Marusa inda suke hutawa,  Mr. Kallah ne sai Brr. Barau,  Adebayo,  Umar sai Alhaji Marusa a zaune,  daga gefe guda wasu manyan maza ne sunci sun k’oshi,  fuskarsu babu alamun fara’a,  d’aya daga cikinsu Peter ne,  sai abokinsa na hannun damarsa. 

Lemu Mr. Kallah ya kurb’a yana fad’in gaskiya Alhaji Marusa wannan karon bansan dame zan saka maka ba,  rabon da muyi irin wannan samun har na manta,  kodan an dad’e ba’a samu masu irin halin Alhaji Maiwada ba?  Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad’in ai dama haka irinsu suke k’arewa,  yanzu gashinan ya rasa kimarsa,  zai rasa dukiyarsa abanza,  kaga mu gaba ta kaimu,  wata kilama hukumar ku ta dakatar dashi. 

Mr. Kallah yace baza’ayi haka ba,  kasan dan an kama mutum da laifi so d’aya ba’a saurin dakatar dashi,  tunda dai nasan abinda ya faru bazan bada goyon baya a dakatar dashi ba domin ya bani tausayi zafin zaiyi masa yawa,  amma ranar litinin zan koma aiki hutuna ya k’are,  zamu tattauna dole aja masa kunne kuma ya tsaya a aikinsa ya bar masu kula da sauran wajen suyi nasu aikin,  idan ya kama dole saiya duba abu sai yaje amma ya tsaya a inda ya kamata. 

Adebayo yace Wallayi Sir da an canza manashi kawai. Mr. Kallah yace kada ka damu da kanshi zai nemi canjin wajen aiki,  yana nema kuma zamu masa sai mu kawo wanda mukeso. Umar yace shikenan ma mun huta. 

Alhaji Marusa yace idan komai ya kammala kowa zaiji sak’o a asusunsa,  Peter kunyi kok’ari dole wannan karon ku samu k’ari. Murmushi Peter yayi yana fad’in mungode Oga. Haka suka cigaba da tattaunawa suna shagalinsu. 

***

*Alhaji Marusa da Mr. Kallah*,  *menene labarin asalin su*? 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button