ALKALI NE Page 11 to 20

****
Bayan la’asar Alhaji Mai Wada ya samu kira daga sama, Mr. Kallah ne ya kirashi yana tambayarsa abinda yasa basu sakar ma Alhaji Marusa kaya ba har yanzu? Alhaji yace Mr. Kallah akwai abinda na gani ne shiyasa nakeso ayi bincike kada mu bashi kayan bayan akwai cuta aciki.
Mr. Kallah yace wace irin cuta? Ka ce da kai aka duba kayan kuma babu komai aciki taya yanzu zaka kawo wata magana, tsaya kaji Alhaji Mai Wada, baza kazo ka kawo mana matsala ba, kowa yasan yanda aikin nan yake, matuk’ar aka duba kaya babu matsala, kuma mai kaya ya biya komai abisa k’aida to dole ne abashi kayansa, dan haka na baka nan da awa d’aya ka sakar masa kayansa.
Dafe kai Alhaji yayi yana fad’in Mr. Kallah ka tsaya nayi maka bayani, ana aikata binda bai dace ba, ana shigowa da kaya haramtattu idan bamu tsaya muka gyara ba tofa kan mu cutar zata dawo, domin idan ta tab’a yaran mu kamar ta tab’a mune, Allah kad’ai yasan abinda aka shigo dashi, ina da shedar da zan nuna maka ka tabbatar ina da gaskiya, kuma wallahi kaji na rantse komin girman Alhaji Marusa dole hukuma ta hukuntashi kuma sai tacisa tara, domin ya karya doka.
Ajiyar zuciya Mr. Kallah yayi yana fad’in wace irin sheda kake da ita fad’a mani? Alhaji yace bazan fad’a maka yanzu ba, amma zan kawo maka ka gani da kan ka, kuma ba kai kad’ai zaka gani ba dole sai an had’a taron manya kafin na fito da shedar.
Mr. Kallah yace shikenan Alhaji bazan hanaka aikin ka ba, wannan abun da kayi yana da kyau, nima na d’auka babu wata matsala a kayan shiyasa nashiga maganar bayan da Alhaji Marusa ya fad’a mani, amma tunda kaine shugaba a wajen bazamu hanaka aikin ka ba, domin irin ku k’asa take nema, bakomai Allah ya taimaka kayi aikin ka a natse. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nagode Yallab’ai.
Bayan ya kashe wayar yayi shiru yana tunanin ashe dai Mr. Kallah mutumin kirki ne, ya d’auka shima yana goyan bayan su ne, tunda har ya bashi goyon baya dole a gobe ya mik’a abinda ya d’auka manya su gani kafin a mik’a Alhaji Marusa kotu domin acan ne za’a yanke masa hukunci dai-dai laifinsa, kuma dole ya fito da kayan da aka b’oye domin asan abinda yake ciki.
Haka ya wuni yana aiki sallah kawai take fitar dashi, abinci ma anan Malan Bala ya kawo masa yaci. Har sukayi magriba kafin Malan Sani yazo ya d’aukeshi, sai da ya d’auki komai nashi hada kemarar kafin suka tafi.
****
Washe gari tunda safe ya kira Adebayo akan ya kula da ofis bazai samu zuwa da wuri ba zaije wajen taro. Murmushi Adebayo yayi yace sai ka dawo Sir.
Koda suka isa can babbar hedikwata haka Malan Sani ya koma gefe yana jiran Alhaji, kai tsaye Alhaji ya nufi hanyar shiga, yana dab da shiga wayarsa tayi k’ara. Yana dubawa yaga Mr. Kallah ne, saurin d’auka yayi. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji Mai Wada ka sameni a ofis d’ina yanzu, akwai maganar da nakeso muyi dan ban fad’a masu zakazo a zauna ba. Alhaji yace shikenan gani nan zuwa. Mota yashiga suka nufi ofis d’in Mr. Kallah.
Kallonshi Mr. Kallah yayi yana fad’in Alhaji Mai Wada nasan ka dad’e kana wannan aikin, kasan kuma yanda halin k’asar mu take, k’ananan mutane ma ka kalli yanda ake gogawa dasu bare kuma manya, nasan kasan kad’an daga cikin labarin Alhaji Marusa, babban mutum ne shi, bana so kaje kayi abinda zaisa mutuncinka ya ragu, kome zakayi ka tabbatar kana da kwakkwarar sheda kafin kayishi, ko kotu kaje idan baka da sheda kwakkwara kotu tana watsi da k’ara, ajiya ka fad’a mani kana da sheda akan abinda ka fad’a, nace ka fada mani amma kace sai kazo, gashi kuma baka fad’a mani ba amma kake kok’arin kai shedar gaban Manyan mu, wannan dalilin ne yasa ko ajiya daka kirani kace na fad’a masu zaka zo na amsa maka kawai, amma babu wanda na fad’ama wannan maganar, koshi Alhaji Marusan besan kana da wata sheda akanshi ba, shiyasa kaji nace kazo domin mu fara gano komai kafin mu mik’a maganar sama.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in wannan gaskiya ne, ya kamata ace mun zauna mun had’a komai kafin afitar da maganar, domin ance idan baka iya kama b’arawo ba shi sai ya kamaka.
Hannu yasa ya ciro kemara yana fad’in ajiya ma naso na tura a (flash) sai kuma bacci ya d’auke ni, da safe kuma na manta kawai na taho da ita. Kunnawa yayi ya mik’a ma Mr. Kallah yana fad’in tun lokacin dana samu labarin kayan zasu iso cikin dare nayi niyar tsayawa ayi komai agabana, sai kawai na samu kira daga wajenka, hakan ya b’ata mani rai, har nayi tunanin wani abu, to da zan tafi sai na mak’ala wannan kemarar domin ina zargin wani abu, washe gari dana zo aka duba kaya babu komai na laifi aciki, bayan dana koma na duba kemarar sai na gano ajiyan an cire wasu kaya kusan kwalaye bakwai wanda bansan abinda yake ciki ba, kuma na tabbata kaya ne marasa kyau aciki, gashinan ka duba zakaga abinda na gani.
Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad’in Alhaji ai banga komai aciki ba, duhu kawai nake gani babu komai aciki. Da sauri Alhaji ya mik’e ya amshi kemarar yana dubawa, ya duba ko ina amma babu abinda ya d’auka aciki sai wata d’auka da akayi ta kusan mintuna talatin amma kuma duhu ne aciki, lokaci ya duba sai yaga k’arfe 1:30 ne lokacin sallar azahar.
Komawa yayi ya zauna jiki a sanyaye kamar an zare masa lakka. Kallonsa Mr. Kallah yayi yana fad’in kaga abinda nake fad’a maka ko? Yanzu da ace kaje agaban mutane ka gama wannan bayanin kazo kunna masu sukaga wannan abun ai zasuce kayi wasa da tunanin su ne, babu wanda ya tab’a kawo k’arar Alhaji Marusa, yanzu idan kaje ka kai kuma ka kasa kawo sheda me kake tunanin za’ace? Tun daga ranar za’a dena gazgataka, ko wata rana kazo da wata maganar bazasu d’auketa da muhimmanci ba.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in nagode da wannan taimakon da kayi mani, insha Allahu dana koma zan sakar masa kayanshi. Mr. Kallah yace bakomai ka k’ara kiyayewa, aikin kwastam akwai had’i acikinsa. Tashi yayi ya bashi hannu kafin ya fita.
Tunda suke tafiya yayi shiru, gaba d’aya kanshi ya d’aure, tabbas wani ne yashiga ofis d’insa ya goge abinda ya d’auka aka d’aukar masa wannan abun, amma *WAYE NE* (tsohon littafi na) yayi masa wannan abun? Babu wanda yasan ya d’auki wannan abun amma gashi an goge masa, da ace ya fad’ama Mr. Kallah yayi d’auka da sai ya zargeshi.
Hannu yasa ya dafe kanshi. Tabbas maganar Mr. Kallah gaskiya ce, aikin kwastam akwai had’ari acikinsa, kuma ya godema Allah da bai kai wannan shedar ba, dole ya sake sabon taku, domin Lagos tasha ban-ban da sauran wajen da yayi aiki, Lagos shu’umin gari ne, k’aramin yaron daya taso acikinta ma sai yayi maka wayau.
Malan Sani ne yace Alhaji kamar akwai abinda yake damun ka ko? Ajiyar zuciya yayi yana fad’in Malan Sani duniya babu gaskiya, son kud’i ya rufema mutane ido, zasu iya aikata komai akan kud’i, wani babban al’amari ne ya faru ajiya zuwa yau, amma na faad’i, domin ban samu damar aiwatar da aikina ba. Ai kasan Alhaji Marusa ko? Malan sani yace sosai kuwa, a Lagos waye bai sanshi ba……..
Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Sosai Malan Sani ya tausaya mashi, kallonsa yayi yana fad’in Alhaji haka Lagos take, shiyasa nake tausayin bakon daya zo cikinta, mutane da yawa suna shan wahala idan suka zo Lagos kafin su waye da ita, haka idan aiki ya kawo ka nan matuk’ar baka da masaniya akan komai kana shan wahala, wasu sun sha rasa ransu akan aikin su, a tunani na dad’ewar da kayi kana aiki zaka iya aiki a Lagos, domin nasan ka zagaya garuruwa da yawa.