ALKALI NE Page 11 to 20

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nima haka nayi tunani Malan Sani, ashe abun ba haka yake ba, duk yanda na d’auki Lagos ta wuce tunani na, shiyasa tunda nazo nake taka tsan-tsan da mutane, domin nasan yanda cin amana yayi yawa.
Malan Sani yace Alhaji maganar gaskiya kada ka sake yarda da kowa, ni jikina ma be yarda da Mr. Kallah ba, tunda kace mani yace kaje nasan akwai wani abu, dole akwai abinda ya sani shiyasa ya kira ka domin baya so kaji kunya, sai yayi amfani da wannan damar domin yasa ka yarda dashi.
Kallon Malan Sani Alhaji yayi cike da nazari. Kai Malan Sani ya jinjina kafin yacigaba da tuk’i yana fad’in Adebayo shu’umin mutum ne, kasan yaren mutum da kud’i, duk da bansanshi ba, amma labarinsa daka bani yanzu yasa na fahimceshi, bazan ce ga wanda nake zargi ya bada damar shiga ofis d’inka ba, domin nasan idan zakaje sallah dole ka rufe odis d’in ka, amma dole sai ka sake lura Alhaji.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in nagose sosai Malan Sani, hakika Allah ya had’a ni da abokin shawara, na yarda da kai, kuma daga yau bani da abokin shawara sai kai, insha Allahu zanyi kamar yanda kace, da sannu sai na gano gaskiya kuma sai na tabbatar da ita, wallahi kaji na rantse maka sai na tabbatar da ainihin fuskar Alhaji Marusa, domin fuska biyu yake da ita, amma zan kwantar da kai domin na samu damar aiwatar da komai cikin sanyi.
Malan Sani yace wannan haka yake, idan mage zata kama b’era kwantar da kai takeyi har sai ta cika burinta, dole sai kayi hak’uri kafin ka tabbatar da gaskiya. Alhaji yace nagode sosai.
Bayan da ya ajeshi ya wuce ofis, sam be nuna komai ba, haka yakira Adebayo yace a saki kayan Alhaji Marusa. Risnawa yayi yana fad’in angama Sir.
Bayan da ya dawo sallar azahar ya iske wasu mutane suna jiranshi. Izinin shiga ya basu. Bayan sun gama gaisawa d’aya daga cikinsu yace sunana Brr. Barau daga babbar kotu, wannan abokin aikina ne Brr. Hamza.
Alhaji yace madalla sannun ku da zuwa, akwai wani abu da kuke buk’ata ne? Brr. Barau yace wani mutumi ne ya shigar da k’ara a kotu saboda wani zalunci da akayi masa, ya kasance yana shigo da taliya dasu makaroni da sabulai daga waje, yau kusan sati d’aya kenan kayansa suka iso, yace ya biya komai amma kuma da aka tashi sakar masa kayan sai aka bashi ba yanda suke ba, wanda hakan ya jawo masa asara sosai, shine yashigar da k’ara, da muka duba sai naga a wajen ku ne, kuma ni ina mutunci da ma’aikatan wajen nan, wanda ya bar wajen ma nine Lauya d’inshi, hakan yasa nace zanzo domin naji yanda gaskiyar abun take, domin mutumin ya d’auko lauya, ni kuma ina giramama ofis d’in ku shiyasa nace zan tsaya maku domin a wanke ku daga zargi, dan idan har akayi shari’ar aka tabbatar daga cikin ku wasu sun danne masa kaya tabbas mutuncin ku zai zube, gashi kai sabon zuwa ne a nan baka gama sanin komai ba, idan akace ma baka da labarin abinda ya faru baza’ayi gardama ba, domin an fad’a mani ajiya ne ka fara sabon tsari.
Cike da mamaki Alhaji yake kallonsu, ak’asan ranshi yana fad’in kaji wata sabuwa kuma. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad’in kada ka damu Alhaji, ni da ku babu wani shamaki domin akwai taimakekeniya atsakanin mu, tsofaffin ma’aikatan wajen sun san da haka, domin kowa ya sanni, dan kana sabon zuwa ne, amma shi Adebayo mutumina ne sosai, dan haka kada ka damu a shigar farko zan kada su, domin ni shari’a cin abinci ma yafi mani wahala akanta, domin ni haka nake, wasu ma da *MAI NASARA* suke kirana. (Tsohon littafina,)
Murmushi Alhaji yayi danshi ya ma rasa bakin magana. Tashi Brr. Barau yayi yana fad’in kada ka damu, wannan itace takardar sammaci daga kotu, zuwa ranar litinin za’a shiga, sai kayi kokarin gano wad’an da suka aikata hakan idan baka da masaniya domin kaja masu kunne, zanyi magana da Adebayo sai mu k’arasa komai dan naga baka gama warware wa da wajen ba, gashi lokaci ya k’ure dole muyi sauri domin mu kare mutuncin ku, saboda kai d’in sabon zuwa ne bazamu so ka fara da haka ba.
Kai Alhaji ya jinjina danshi gaba d’aya kanshi ya k’ulle, beda masaniya akan komai, bazai iya shiga abinda bai sani ba, dole ya zuba masu ido yaga abinda zasuyi dan shi yanzu yanda zai b’ullo ma Alhaji Marusa kawai yake damunsa.
Hannu Brr. Barau ya bashi yana fad’in sai ka jini mungode da lokacin daka bamu. Alhaji yace bakomai nagode. Bayan sun fita Alhaji yashiga dogon tunani, tabbas lokacin da aka aikata wannan abun beda masaniya, yanzu shikenan haka za’a danne ma bawan Allah kayansa kuma kotu ta bashi rashin gaskiya? To idan ma yace zai taimaka mashi ta yaya? Dole wannan karon ya aikata laifi kodan kare mutuncin aikin su, amma matukar aka gama da kotu saiya gano wad’an da suka aikata wannan abun kuma sai ya d’auki mataki, dole yajira litinin yaje kotu yaji komai.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.*
0⃣7⃣
Tafe suke a mota ya kalli Malan Sani yana fad’in wato Malan Sani idan kana da rai zakayi ta ganin abubuwan al’ajabi. Malan Sani yace wani abun akayi maka ko Alhaji? Murmushin gefen baki yayi yana fad’in maganar da mukayi da kai jiya itace ta rushe, an duba kemarar babu komai aciki, an samu wani mai wayon ya goge abinda ta d’auka.
Kallonshi Malan Sani yayi cike da mamaki yana fad’in amma Alhaji ya akayi haka ta faru? Alhaji yace mai son abunka yafika dabara ai, naje sallar azahar lokacin ne aka shiga ofis d’ina.
Malan Sani yace ina Malan Bala to? Alhaji yace atare muka je masallaci dashi kum na rufe ofis d’in. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in lallai ko waye ya san takan ofis d’in. Alhaji yace ko waye yayima kansa, kuma insha Allahu matuk’ar ina raye sai na kawo k’arshen zaluncin da akeyi.
Yanzu haka ranar litinin kotu zamuje, d’azu wani Brr. Barau yazo ya kawo mani takardar sammaci wai an zalunci wani ya shigar da k’ara, kayansa ne sukazo sai aka rik’e, bayan daya amsa sai ya samu abubuwa da yawa sun b’ata, yayi asara sosai shine yashigar da k’ara, abinda na lura dashi Brr. Barau ya dad’e yana ma ofis d’in mu aiki, da alama shid’in marar gaskiya ne.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in Alhaji waye besan Brr. Barau ba, wannan mutumin idan beyi wasa ba sai yaci wutar Allah, duk wata k’ara da aka kaita babbar kotu matuk’ar mutum ya saki kud’i Brr. Barau zai tsaya masa, kafin a kadashi a shari’a da wuya, shi kuma Alkali kwakkwarar sheda yake nema, matuk’ar ya sameta shikenan zai yanke hukunci, wannan adalci da Alkali yakeyi shine yasa mutane suke sonshi, duk da wani lokacin ba akan gaskiya yake yanke hukuncin ba amma babu yanda ya iya, domin abinda ya gani dashi yake aiki, kuma baya yanke hukunci sai kowa ya sheda gaskiyar abinda aka gabatar, shiyasa nake fad’a maka Brr. Barau shine babban azzalumi.
Alhaji yace abinda yake fad’a mani kenan da yazo, wai ni sabon zuwa ne shiyasa yazo da kanshi dan baya so daga zuwana na samu matsala, shiyasa yake so ya wanke mu. Girgiza kai yayi yana fad’in Malan Sani a wannan karon bani da zab’i, domin lokaci ya kure mani, idan nace bazan bi yanda yace ba tabbas nine a k’asa, domin bansan da wannan maganar ba sai zuwanshi.