ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Tausayi Alhaji ya ba Malan Sani,  domin yasan yana son tabbatar da gaskiya amma be gama sanin kan wajen ba. Kallonsa yayi yana fad’in Alhaji kada ka karaya domin Allah yana tare da mai gaskiya,  bakomai kaje kotun kaji yanda komai yake Allah yaga zuciyar ka,  idan yaso daga baya sai kayi bincike. 

Murmushin jin dad’i Alhaji yayi yana fad’in nagode Malan Sani,  ina matuk’ar jin dad’in zamanka akusa dani,  insha Allahu zanyi kok’arin bincike domin na gano gaskiya,  kila ta wannan hanyar ne Allah zai haska mani komai. Malan Sani yace in Allah ya yarda. 

***** ****

Ranar litinin haka babbar kotu ta cika,  *Alhaji Usman* wanda shine  ya shigar da k’ara yana daga gefe shida sauran abokansa tare da lauyen daya d’auko. 

Alhaji Maiwada yana isowa Brr. Barau da Adebayo suka tarbeshi. Bayan sun gaisa Brr. Barau yace Alhaji komai ya kammala insha Allahu zamuyi nasara. Murmushin takaici Alhaji yayi yace Brr. Allah ya shige mana gaba. Brr. Barau yace amin. 

Cikin lokaci k’ank’ani  aka kammala shari’ar wanda Brr. Barau ne yayi nasara,  domin ya gabatar da shedun bogi wanda kowa ya d’auka da gaske ne. Alhaji Usman kusan zubewa yayi lokacin da Alkali ya yanke hukunci,  zama yayi ana ta yimasa fifitu. 

Alhaji Maiwada yana zaune kamar wanda aka dasa,  besan lokacin da idonshi ya cika da kwalla ba,  lallai duniya babu gaskiya,  yanzu shikenan an cuci wannan mutumin?  Kallon Brr. Barau yayi yaga suna kashewa da su Umar da Adebayo. Murmushin takaici kawai yayi ya bar kotun ko ta kan Brr. Barau bebi ba suka tafi ranshi a b’ace. 

****

Ranar Talata tunda safe Alhaji yaje ofis. Malan Sani shima be tafi ba saboda anyi suna,  tunda yazo suke zaune da Malan Bala suna ta fira,  a hankali Malan Sani yake tambayar Malan Bala yanda wajen yake. Haka Malan Bala yayi ta bashi labari. 

Har zuwa azahar Alhaji yana bincike  akan abinda ya faru,  wasu daga cikin ma’aikatan da ya yarda dasu yarik’a kira yana masu tambayoyi tun daga ranar da abun ya faru. 

Mutum d’aya ya samu mai suna *Abubakar*,  shine mataimakin mai kula da kaya,  kasancewar shima yana kwatanta gaskiya yasa ake maidashi baya tun lokacin tsohon shugabansu,   musamman idan akace kaya masu tsoka sunzo. 

Kallon shi Alhaji yayi yana fad’in Abubakar aranar da kayan Alhaji Usman suka zo ya akayi da aka rike masa wasu daga ciki suka b’ace?  Gyara zama Abubakar yayi yana fad’in wallahi Alhaji aranar da abun zai faru Adebayo da Umar ne suka karb’i kayan,  ina wajen amma sai Adebayo ya bani sako na kaima Alhaji Marusa,  ban dawo ba saboda dare yayi sai kawai na wuce gida. 

Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in dole sune suka d’auki kayan Alhaji Usman. Abubakar yace kuma sun amshi kud’i da yawa awajenshi kafin suka sakar masa kaya,  kuma ina tunanin kayan nan basu raba su ba,  dole akwai inda suka aje su,  akwai *Moses* abokina ne yasan sirrinsu domin suna yaga masa wani abu saboda sun san halinsa, ina ganin zai iya sanin yanda akayi da kayan. 

 Alhaji yace Abubakar kira mani shi Allah yasa ya bamu had’in kai. Abubakar yace kada ka damu nasan waye Moses,  mutumina ne sosai. Waya ya dauka ya kirashi. 

Beyi mintuna biyar ba sai gashi. Risnawa yayi ya gaishe da Alhaji. Wajen zama Alhaji ya nuna masa,  bayan ya zauna Abubakar yayi masa bayanin abinda Alhaji yake buk’ata. 

Murmushi Moses yayi yana fad’in Sir,  wannan abu ai ya dad’e yana faruwa a wajen nan,  tun lokacin da nazo Oga John yake abinda yaga dama shida su Oga Adebayo,  Omar shima baya da gaskiya,  saboda sun san nasan komai yasa suke yaga mani kasona,  Sir kasan zuciya da kud’i shiyasa nima nake amsa,  amma wancan ranar da suka sace kayan Alaji Osman ni nasan inda suka b’oyesu,  sunce sai anyi kamar wata d’aya ko biyu komai ya wuce sai suzo cikin dare su kwashe abunsu su raba,  acikinsu akwai wasu ma’aikatan da suke bin bayan su. Sir ina fad’a maka a wajen nan fa akwai b’arayi,  ni dai bana sata,  amma idan aka bani ina amsa 

Alhaji yace yanzu Moses a ina suka aje kayan? Moses yace Sir,  zan fad’a maka amma du Allah kada ka beri su gano nine na fad’a maka,  ina son kud’i kuma idan suka gano bazasu rik’a bani ba. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in zan rubuta sunanka acikin wad’an da zan dakatar har na tsawon watanni biyu kuwa,  domin kana amsar cin hanci wata rana zaka fara d’aukar kayan wasu. 

Zubewa Moses yayi yana fad’in du Allah Alaji ka rufa mani asiri,  wallayi daga yau zan zama kamar Abubakar,  zan rikayin gaskiya. Alhaji yace naji,  amma idan na gano kacigaba da karb’ar cin hanci sai na dakatar da kai. Tashi Moses yayi yana murza hannu yace na yarda. Nan ya fad’a masu inda kayan suke. 

Jinjina kai Alhaji yayi yace suje. Bayan sun fita yayi shiru yana tunanin yanda zai b’ullo ma al’amarin,  baya so ya watsa ma Brr. Barau k’asa a ido,  domin idan yace zai bayyanar da gaskiya tamkar yaci masa fuska ne,  amma dole ya hukunta duk wanda yake dasa hannu a cikin wannan abun. 

Waya ya d’auka yakira Adebayo. Ba’afi mintuna biyar ba sai gashi ya shigo yana ladabin munafurci. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in Adebayo na samo inda kayan Alhaji Usman suke,  kuma za’a mayar masa da abunsa. 

A zabure Adebayo ya mik’e yana fad’in Sir,  waye ya fad’a maka inda suke?  Alhaji yace kasan b’oyesu akayi kenan? Zama yayi jiki a sanyaye yana fad’in Sir,  ba haka bane,  naga an gama komai a kotu be kamata amaido maganar baya ba. 

Tashi Alhaji yayi yana fad’in na baka nan da anjima ka rubuto mani sunayen wad’an da suke dasa hannu a abinda kukayi,  a sunan farko kasa naka dana Umar. 

Hannu Adebayo yasa yana goge zufa, hannuwa yahad’e yana fad’in Sir,  kayi hak’uri,  shikenan zan fito da kayan amma kada a koma kotu domin zamu iya rasa aikin mu kuma za’a iya kaimu gidan yari. 

Alhaji yace abu d’aya zakayi,  matuk’ar ka rubuta mani sunayen wad’an da suke dasa hannu a abinda kukayi to bazan kai ku kotu ba,  amma ina da sharad’i wanda dole ne ku bishi. 

Da sauri Adebayo yace yanzu zan fad’a maka,  mu biyar ne hada Omar,  kuma zamubi sharad’in ka. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in doka zata fara aiki daga kanku,  sai dai zan maku sauki zan dakatar da ku na wata d’aya kawai,  sannan zanyi magana da Alhaji Usman,  idan ya yafe maku shikenan,  idan kuma yace sai an koma kotu bani da zab’i. 

Cike da damuwa Adebayo yace ka bashi hak’uri kayansa suna nan babu abinda muka tab’a amma kada a koma kotu. Alhaji yace tashi kaje zamuyi magana dashi. Jiki a sanyaye Adebayo ya fita. 

Bayan ya fita Alhaji ya d’auki waya ya kira Alhaji Usman domin ya samo lambarsa. Koda ya d’auki wayar ya gane har lokacin yana cikin damuwa. Bayan sun gaisa yayi masa bayanin kansa,  cike da masifa Alhaji Usman ya fara magana,  sai da ya gama Alhaji yace idan zaka yarda ina son ganinka amma agida,  domin maganace akan kayanka dana gano,  amma inaso kayi shiru kada ka fad’ama kowa. Cike da farin ciki Alhaji Usman yace kayi hakuri ban fahimceka daga farko ba,  shikenan zaka iya zuwa anjima bayan sallar isha’i. Alhaji yace shikenan ka turo mani da kwatancen gidan ka. Sallama sukayi ya kashe wayar. 

***

Bayan sallar la’asar su Umar da sauran mutane ukkun da Adebayo ya rubuta sunan su suka hallara ofis d’in Alhaji. Bayan ya gama masu bayani duk suka shiga bashi hak’uri. Alhaji yace bana magana biyu,  kunci sa’a da na rage maku wata biyu,  sannan zanyi kok’arin kare mutuncin aikin ku,  amma daga yau idan na sake kama ku da aikata makamancin wannan abun to maganar sai taje sama. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button