ALKALI NE Page 11 to 20

Idan kunso zaku iya tona asirin ku, amma ni dai babu wanda zan fad’a mawa, kuma bazan dakatar da albashin ku ba domin daga banki yake zuwa, matuk’ar nace zanje adakatar dashi dole sai manya sun san da maganar, amma ni zan yanka ma kowa abinda zai bayar a bama Alhaji Usman amatsayin tara, domin wannan shine adalci, kuma baza ku zo aiki ba har sai nan da wata d’aya, sannan kowa acikin ku zai bayar da dubu hamsin ga Alhaji Usman domin kun jawo masa asara, ko ya amshi kayanshi wasu kud’in bazasu dawo ba, idan kuma kuna ganin wannan abun beyi maku ba, shikenan sai muje kotu ta yanke maku hukunci.
Gaba d’aya suka had’a baki wajen fad’in sun amince. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in da kyau, daga yau ba sai kun sake zuwa aiki ba, kowa yaje ya huta. Adebayo yace Sir, ka barmu muzo aiki wasu zasu iya gano wani abu. Umar yace dan Allah Alhaji ka rufa mana asiri abarmu muyi aiki sannan zamu bayar da kud’in.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in shikenan, tunda wannan shine karo na farko dana fara kama ku da laifi zanyi maku uzuri, amma akan biyan kud’i babu uzuri, sannan zan rubuta na ba kowa yasa hannu akan duk lokacin da aka sake kamaku da irin haka babu sauran uzuri. Gaba d’ayansu suka amsa da sun amince.
Bayan da suka gama sa hannu akan kowa zai bayar da kud’in kuma sun amince da lifin da aka kamasu dashi. Haka kowa ya fita jiki a sanyaye. Adebayo da Umar waje suka samu kowa da abinda yake fad’a. Adebayo yace Omar wannan mutumin sai yasan yayi mana haka, Brr. Barau zan kira na fad’a masa komai.
Umar yace kada ka fad’a masa, kasan Brr. Barau da surutu zai iya fitar da maganar, tunda dai Allah yaso Alhaji zai rufa mana asiri to mu bar maganar. Adebayo yace shikenan, amma wallayi sai na rama kasanni ai. Umar yace ba yanzu ba, dole mu kwantar da kai har zuwa wani lokaci. Adebayo yace shikenan.
***
Bayan da akayi sallar isha’i Alhaji ya tashi domin yana son zuwa wajen Alhaji Usman. Haka suka nufi gidanshi suna bin kwatancen da ya turo masa. Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad’a masa, kuma ya jinjina adalcin da Alhaji yayi masu.
Zaune suke a cikin rumfar da take a harabar gidan. Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya sake bama Alhaji Usman hak’uri akan rashin adalcin da akayi masa. Alhaji Usman yace bakomai, nima ina baka hak’uri akan abinda nayi maka awaya, duk da nasan kai d’in sabon zuwa ne amma nayi tunanin kaima irin halin tsohon shugaba gare ka, domin daga zuwanka har na fara asarar kaya.
Alhaji yace bakomai, domin ni bansan da maganar ba sai da Brr. Barau yazo mani da maganar, alokacin bani da abinda zanyi hakan yasa nayi shiru da niyar nayi bincike bayan an gama komai. Alhamdulillahi kayan ka suna nan babu wanda ya b’ace, kuma na gano wad’an da suka aikata hakan.
Alhaji Usman yace acikin su akwai Adebayo. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in kaima kasan halinsa kenan? Alhaji Usman yace waye besan Adebayo ba, dashi da Mr. John halinsu d’aya, shegu arnan banza, babu Allah aransu sai cuta.
Alhaji yace nazo neman wata alfarma awajenka ne Alhaji, nasan zeyi wuya kayi mani ita, amma ina rokon ka da ka dubi girman Allah ka amince da abinda zan fad’a maka.
Alhaji Usman yace babu abinda zaka nema awajena banyi maka shi ba, domin kayi mani abinda Kotu ta kasa tayi mani, dan haka kayi maganar ka kawai…..
Bayanin abinda yake so yayi masa. Shiru Alhaji Usman yayi kafin can yayi murmushi yace saboda kai zanyi masu wannan alfarmar, domin ko alahira wani yana cin arzik’in wani, bakomai, ka d’auka baka fad’a mani komai ba, nayi maka alk’awarin babu wanda zaisan da faruwar haka, zan nuna cewar wasu kayan ne sukazo.
Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nagode sosai Alhaji Usman Allah ya k’ara girma. Alhaji Usman yace amin nagode, kuma acikin kud’in da zasu had’a dubu d’ari biyu da hamsin ka d’auki dubu d’ari na baka kyauta.
Girgiza kai Alhaji yayi yana fad’in hakkina ne nayi maka hakan, bana buk’atar komai. Alhaji Usman yace nima kyauta ce nayi maka ai. Alhaji yace Allah bazan amsa ba. Alhaji Usman yace shikenan na bama direban ka, domin nasan irin halinka gareshi. Alhaji yace to mungode sosai, anjima kad’an kayanka zasu iso. Alhaji Usman yace nagode.
****
Tun daga wannan rana Alhaji Maiwada yake aikinsa hankali kwance, kowa yashiga hankalinsa domin sun san Alhaji Maiwada ba wasa. Adebayo da Umar sun natsu tamkar babu su a wajen, su kad’ai sukasan abinda suke kullawa.
A yanzu duk wani wanda yake samun matsala da ma’aikatan kwastam na wajen su Adebayo yanzu hankalinsa akwance yake, domin idan kaya suka iso cikin lokaci k’ank’ani za’a duba a cike komai bisa tsari a sakar maka kayanka idan babu haramtattun kaya aciki.
Duk wanda aka kama da haramtattun kaya aciki babu batun ya bada cin hanci asakar masa, idan aka kama shikenan baza’a badasu ba. Alhaji Marusa yanzu ya dakatar da shigo da kayan da yake shigowa dasu, domin sun tattauna akan Alhaji Maiwada, sun yanke shawarar su d’aga masa k’afa zuwa wani lokaci ya gama zafin kanshi.
Kafin wani lokaci Alhaji Maiwada yayi suna a Lagos musamman a wajen wad’an da suke jin dad’in zuwansa.
Duk bayan wata yake zuwa Kano ganin iyalinsa. Alokacin Ra’eez yana aji ukku a primary, Alhaji yace zai maidasu Lagos saboda ya kusa kammala gininsa.
Nan Ummun Ra’eez ta nuna ya bari Ra’eez ya kammala firmare kada a lalata masa karatu. Alhaji yace shikenan Allah ya kaimu, kafin lokacin ma na kammala gini na, bara naje muyi maganar da Alhaji Mansur kada yaji maganar daga sama.
Lokacin daya fad’ama Alhaji Mansur yana so ya mai da Iyalinsa Lagos sai Alhaji Mansur yace wannan yana da kyau, bazai yuwu kayi ta zama babu mata akusa da kai ba, kasan yanda zuciya take, duk yanda muka kai da sabawa dole muyi hak’uri, amma kuma zumuncin mu yana nan, amma nafi so Ra’eez yayi makarantar kwana anan Kano, haka kawai bana so yaje yashiga cikin arnan nan, kaga anan akwai karatun addini a makarantar da nakeso na samar masu shida Labiba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad’in wannan ai bakomai, Ra’eez ‘Danka ne, duk abinda ka yanke akanshi yayi, nima ina masa kwad’ayin samun ilimin addini mai zurfi domin Kano dabance a wajen ilimin addini. Alhaji Mansur yace to nagode.
**** ***
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah Alhaji ya kammala gininshi, yayin da yasa Malan Sani ya sayar da gidanshi ya cika masa ya sayi wani gidan ya canza unguwa, yaso ya sama masa gida a unguwar da yayi gini amma babu gida mai k’aramin kud’i, hakan yasa ya saya masa a unguwa dai-dai kud’insa, sai dai tafi waccan unguwar da suke.
Sosai Malan Sani yaji dad’in abinda Alhaji yayi masa. Matarsa Halima tafishi jin dad’i, domin tunda taga Rumaisa tayi wayau kyanta sai fitowa yake ta fara tsorata da unguwarsu, domin unguwace ta marasa tarbiya, shiyasa har lokacin shigarta makaranta yayi Halima bata yarda ansata ba, lokacin da taji zasu tashi hada kukan farin ciki tayi, duk da zata rabu da makwabciyarta mai kirki.
Yanzu tsakanin Malan Sani da Alhaji yanda kasan ‘yan uwa, d’aya baya zartar da abu ba tare da shawarar d’aya ba, akwai girmamawa sosai atsakaninsu, Malan Sani bai tab’a tsallake maganar Alhaji ba amatsayinsa na direbanshi, duk da Alhaji ya sakar masa komai amma baya masa almubazzaranci. Haka Alhaji da kanshi ya saka Rumaisa makarantar kud’i mai sauki, kuma shine ya d’auki nauyin karatun ta.