ALKALI NE Page 11 to 20

A wajen aikinsa kuwa yana kokarin adalci ga na k’asa dashi, sai dai yana samun damuwa daga na sama dashi, yasha kama kaya amma ya samu sako akan ya sake su, wani lokacin kuma a hanashi ya duba kayan, sosai wannan abun yake damunsa.
***
Bayan shekaru biyu Ra’eez ya kammala makaranta, haka Alhaji yaje akayi taron yayesu. Bayan kwana biyu sukayi sallama dasu Alhaji Mansur zasu tafi hada Ra’eez kafin jarabawarsu ta fito. Ummun Ra’eez da Matar Alhaji Mansur hada kukan rabuwa.
Haka suka d’aga zuwa Lagos cike da kewar babbar aminiyarta.
Ur’s.
Nabeelert Lady????[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263.*
0⃣8⃣
*SURELERE* itace unguwar da suka koma, gida ne mai kyan gaske, domin Alhaji ya dad’e yana ginashi ta yanda zaiji dad’in rayuwa da Iyalinsa, acewarsa beda wasu dangi da suka wuce Iyalinsa, shiyasa ya tsara gida mai kyau saboda suji dad’in rayuwa aciki.
Tunda Ummun Ra’eez taga gidan taji ya burgeta, sosai tayi farin ciki da wannan gida. Ra’eez sai murna yake sun dawo gida mai kyau. ‘Dakinshi daban babu abinda ba’asa mashi ba. Haka d’akin Ummunsa komai akwai aciki, jitake kamar wata sabuwar amarya, saboda farin ciki rungume Alhaji tayi hada kukan farin ciki.
Murmushi yayi yana shafa bayanta yace haba Ummun Ra’eez, meyasa zaki rik’a kuka haka? Hannu tasa ta share hawayenta tana fad’in Abbun Ra’eez dole nayi kukan farin ciki, ban tab’a tunanin kasancewa a irin wannan gidan ba, duk da gidan ka na Kano yana da kyau amma wannan daban ne, ginin zamani ne had’e da kayan zamani aciki, unguwar kad’ai abun kallo ce, bansan da wane baki zan gode maka ba.
Rungumeta ya sakeyi yana fad’in bana buk’atar godiyar ki Bilkisu, addu’arki kad’ai nake buk’ata, domin kinsan halin irin aikina, addu’a kad’ai zaki bini da ita, Allah ya albarkaci Ra’eez ya kuma kawo wasu masu albarka a sabon gida.
Guduwa tayi d’akinta tana murmushi. Dariya yayi yana fad’in yau kuma an tuno da daren amarci ne? Tana jinshi ta shige tana dariya. Madu ne ya danna kararrawa hakan yasa Alhaji yaje ya bud’e.
Kwando ya gani mai d’auke da kuloli aciki sai babbar roba wadda aka cikata da zob’o. Kallonsa Alhaji yayi cike da mamaki yana fad’in Madu wannan kuma daga ina? Madu yace Malan Sani ne ya bani yace na kawo maku.
Murmushin jin dad’i Alhaji ya saki yana fad’in ikon Allah!, ina shi Malan Sanin yake? Madu yace yana bani ya tafi yace baya son a taso ka kana hutawa. Amsar kwandon Alhaji yayi yana fad’in gaskiya naji dad’i sosai, yanzu nake shirin na fito na aike ka ka samo mana abinda zamuci saboda Ummun Ra’eez ta gaji bazata iya girki ba, ashe Malan Sani yayi mana tanadi, Allah ya saka masa da alkhairi. Madu yace amin. Alhaji yace bara nashiga ciki sai na miko maka naka.
Ciki yashiga yana kiran Ummu, fitowa tayi tana amsawa. Alhaji yace kinga Malan Sani ya kawo mana abinci, matarsa ce ta dafa. Murmushi Ummu tayi tana fad’in kai amma naji dad’i sosai, wallahi dama yunwa nakeji ina tunanin abincin siyarwa.
Ra’eez ne ya fito yana fad’in Abbu nima zanci. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in ashe dai kowa yunwa yakeji? Taho kaci Kawun ka ne ya kawo mana. Ra’eez yace Abbu anjima zamuje naga Rumaisa ko? Dariya sukasa Ummu tace daga yau dai andena baka labarin Rumaisa zaka rik’a ganinta tunda mun dawo garin su. Alhaji yace anjima muna hutawa zamuje ka ganta. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in yauwa nagode Abbu.
***
Bayan sallar la’asar suna shirin zuwa gidan Malan Sani sai k’arar kararrawa sukaji, Alhaji ne yaje ya duba, saurin bud’ewa yayi yana fad’in ikon Allah, Malan Sani kune haka? Yanzu muke shirin zuwa Ra’eez ya matsa mana sai munje yaga Rumaisa.
Matsawa yayi yana fad’in kushigo, kamo hannun Rumaisa yayi yana fad’in kema kinzo ganin Ra’eez ko? Kai ta d’aga tana murmushi. Malan Sani yace ai mune ya kamata muzo muyi maku sannu da zuwa. Ciki suka shiga Alhaji yashiga kiran Ummu.
Kallon Malan Sani Halima tayi tana fad’in lallai Malan idan kana raye zakasha kallo, ashe haka gidan nan yayi kyau? Ai baka fad’a mani komai ba. Malan Sani yace dama ai gani da ido ya kori ji, duk yanda zan baki labarin gidan be kai yanda kika ganshi yanzu ba.
Rumaisa tace Baba ni dai anan zan kwana yau. Malan Sani ya d’aure fuska yana fad’in idan na sake jin wannan maganar abakin ki saina zaneki kina ji na? Kai ta d’aga cike da tsoro. Halima tace nima zaneki zanyi idan kika sake fad’ar haka, idan ma ance kizauna bance ki amince ba, nasha fad’a maki duk abinda zakiyi arayuwa kada ki hangi na wani, ban tab’a duba da k’arancin shekarun ki ba kullum nake fad’a maki haka saboda ya zauna a kanki, kwad’ayi bashi da amfani kinji Rumaisa? Kai ta d’aga tana fad’in bazan sake ba.
Murmushi Malan Sani yayi ya jawota yana shafa mata kai yace yauwa Rumaisar Baban ta, haka akeson yaron kirki ya kasance. Sallamar su Ummu sukaji hakan yasa suka maida hankalinsu wajen su suna amsawa.
Zama sukayi nan suka shiga gaisawa. Ummu tace Maman Rumaisa yau dai Allah yayi mun had’u, koda yaushe sai dai muyi waya yau gashi mun dawo garin ku. Halima tace wallahi kuwa, tunda Alhaji yace zaku dawo nake cike da farin ciki, Allah ya kare ki daga sharrin mahassada.
Ummu tace amin. Hannu ta mik’a ta kamo Rumaisa tana fad’in zonan ‘Diyata. Duk’awa Rumaisa tayi har k’asa tana gaishe da ita. Dariya Ummu ta saki don sosai Rumaisa ta burgeta, gaba d’aya shekarunta bazasu wuce biyar ba amma tana da tarbiya.
Shafa kanta tayi tana fad’in lafiya lau Rumaisa ya karatu ana zuwa ko? Kai ta d’aga tana fad’in duka biyu duk ina zuwa. Ummu tace da kyau, ki dage kiyi karatu kinji? Kai ta d’aga tana murmushi.
Ra’eez ne ya sauko daga sama sai sauri yakeyi dan lokacin da suka zo yana band’aki. Yana isowa falon ya dai-daita tafiyarsa, dan Ra’eez akwai natsuwa, ya samu tarbiya mai kyau. Da sallama ya shigo, gaba d’ayansu suka amsa suna murmushi.
Har k’asa ya duk’a ya gaishe da su. Malan Sani yace matsonan mugaisa abokina. K’arasawa yayi ya bashi hannu yana mai masa sallama. Dariya sukasa Malan Sani yace lallai Malaman Kano sun karantar da kai da kyau, to ya hanya, kazo lafiya ko? Ra’eez yace lafiya lau Kawu.
Sosai Malan Sani yaji dad’in yanda Ra’eez ya kirashi da Kawu. Halima tace Ra’eez ya karatu ka gama firamare sai ta gaba ko? Ra’eez yace na gama. Matsawa yayi ya kamo hannun Rumaisa yana murmushi yace yau baza kiyi mani magana ba bayan a waya muna gaisawa? Dariya tasa tana fad’in sannu da zuwa Yaya.
Gaba d’aya sai da sukayi dariya. Ummu tace ta waya ta k’are ai tunda ka dawo garin su, sai karik’a koya mata karatu. Ra’eez yace to Ummu kice ma Kawu ya barta nan. Kafin Ummu tayi magana Rumaisa ta kwace hannunta tana fad’in ni dai wajen Mama zan zauna.
Dariya sukasa Ummu tace nima ai Mamanki ce. Rumaisa tace ni dai gidan mu zan kwana. Alhaji yace nan ma gidan ku ne ai. Kafad’a ta mak’ale tana kwanciya saman cinyar Mamanta.
Ra’eez yace Ummu kinji abinda tace wai. Ummu tace kada ka damu zata rik’a zuwa, kaga itama ita kad’aice a wajen Mamanta, idan ta dawo nan za’a bar Mama ita kad’ai.