ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Jinjina kai yayi yana fad’in to nima zan rik’a zuwa gidansu. Dariya suka sa. Tashi Malan Sani yayi yana fad’in bari mu koma yamma tayi kada mu hana ku aiki. Alhaji yace ba wani aiki da mukeyi kuyi zaman ku. Malan Sani yace zamu dawo wani lokacin akwai gajiya ai. 

Tashi Ummu tayi tana fad’in ina zuwa. Tsarabar data kawo masu ta d’auko tana fad’in Rumaisa ga tsarabar ki. Kin amsa Rumaisa tayi tana nok’e kafad’a. Murmushi Ummu tayi tana fad’in Rumaisa da wayau kike,  gaskiya Maman Rumaisa kin bata tarbiya me kyau,  a garin nan dama idan yaronka be samu tarbiya mai kyau ba abun tsoro ne. 

Alhaji yace indai Rumaisa ce zakisha mamaki,  wayonta har ya wuce shekarunta. Dariya sukasa Malan Sani yace ai Hajiya Lagos abun tsoro ce,  addu’a kad’ai zamu rik’e. Ummu tace haka ne. Mik’ama Halima ledar tayi tana fad’in ga tsarabar kanawa. Amsa tayi tana fad’in mungode sosai. Ummu tace haba bakomai,  munci abinci yayi dad’i angode. 

Haka suka rakasu har bakin mota,  sai da suka tafi sannan suka dawo. Ra’eez sai fushi yakeyi. Kamoshi Ummu tayi tana fad’in haba Ra’eez ai zaka rik’a ganinta tunda gari d’aya kuke. Alhaji yace ka bari zan kai ka  wuni acan kaji. 

Ummu tace wallahi dama su dawo wancan b’agaren na waje. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nayi tunanin haka tun farkon da aka fara zanen gidan,  amma abinda nayi tunani ya hanani aikata hakan,  akoda yaushe idan zaka taimaki mutum to kayi kok’arin d’orashi a hanyar da zai samu ba hanyar da zaka rik’a bashi ba,  hakan yana kashe zuciya,  hausawa suna fad’in daka d’auki abinci kaba mutum gara ka nuna masa hanyar gona,  koba komai zai dogara da kanshi kuma zaifi tattala abinda ya samu,  na duba naga gara na canza masa unguwa na cika masa ya sayi gida akan na kawoshi gidana ya zauna,  domin kawoshi gidana da zama zai kashe masa zuciya ya kasa mallakar nasa,  kuma zumuncin mu zaifi kwari idan akace muna nesa da juna,  kinji dalilin da yasa ban maidosu nan ba. 

Ummu tace kana da gaskiya kuma,  shikenan Allah ya karemu daga sharrin mahassada kuma ya bamu zama lafiya. Alhaji yace amin. Ra’eez yace Abbu a wace islamiyar za’a sani?  Abbu yace Ra’eez zamanka Lagos ba mai dad’ewa bane,  bana son ma ka saba da ita har sai bayan ka mallaki hankalin kan ka,  dan haka babu makarantar da zan saka, jarabawarku  tana fitowa zaka tafi Kano,  ko hutu akayi sati biyu kawai zaka zo kayi ka koma saboda islamiya,  nafi buk’atar kayi ilimi mai zurfi dana zauna da kai anan,  duk lokacin daka kammala karatun ka sai kazo mu zauna tare,  domin wancan filin dana bari gidan ka ne za’a gina idan kayi aure ka zauna da matar ka. 

Hannu Ra’eez yasa ya rufe fuskarsa ya bar wajen da gudu. Dariya sukayi Ummu tace Yarona fa akwai kunya. Alhaji yace ashe Yaron ki,  Yarona  dai. Murmushi Ummu tayi tace Yaron mu dai. Alhaji yace idan kina son naki to ki haifo Mamana. Murmushi tayi tana fad’in Allah ya kawo masu albarka,  yace amin Ummun Ra’eez.

**** ***

Tunda suka dawo Lagos Alhaji ya k’ara samun natsuwa,  aikinsa yake sosai,  yayin da Ummu suke zumunci da Maman Rumaisa sosai,  Ra’eez yana zuwa gidan su yayita koya mata karatu,  itama ana kawota idan ba makaranta,  sai dai babu wanda yake kwana gidan kowa,  Malan Sani shine yake kaita kuma ya d’aukota koda tayi bacci,  haka ma Ra’eez shine yake maidashi. 

A wajen aikin su Alhaji Maiwada babu wanda yasan yana da ‘Da,  domin babu wanda ya fad’ama ya maido iyalinsa,  ko walimar shiga sabon gida beyi ba,  yayi addu’a kamar yanda addini ya koyar,  shiyasa babu wanda yasan ya tare a sabon gida, asalima babu wanda yasan yana gini,   dan Alhaji mutum ne mai son sirri,  duk yanda kuke dashi baya bari ka sameshi agida musamman akan maganar data shafi wajen aiki. 

***

Zuwa yanzu Boda d’insu ta samu lafiya,  domin aiki ake sosai,  duk wanda aka kama da laifi nan take ake yanke masa hukunci,  shiyasa kowa yake kaffa-kaffa da aikinsa. Manyan masu kud’i wad’an da suke kasuwancin shigo da kaya sam basa son Alhaji Maiwada,  sunyi-sunyi a canza shi sai dai abun yaki tasiri,  domin har yanzu ba’a canzashi ba,  ganin haka yasa suka fara shirya masa mugunta,  sai dai har yanzu basuci galaba akansa ba. 

*****

Jarabawar su Ra’eez ta fito kuma ya samu makarantar kwana shida Labiba,  inda suka samu *FGC DAURA*,  yayin da aka canza masu islamiya mai kyau idan suka dawo hutu surik’ayi. Sosai yayi farin ciki da samun makarantar kwana,  saboda yana son makarantar kwana. 

Haka aka kammala masa komai,  lokacin da zai tafi hada kukan rabuwa da Rumaisa,  Ummu tace tare da ita zata tafi domin tayi masa rakiya. Haka suka shirya kasancewar ta jirgi zasu bi hakan yasa basu tafi dasu Malan Sani ba. 

Kwanansu biyu sai da suka kaisu har makaranta kafin suka koma Lagos. Rumaisa sai kuka take Ummu tana lallashinta. 

Bayan komawarsu ne Ummu tace gidan yayi mata shiru tana son ta samu mai aiki. Alhaji yace ina tsoron mutanan garin nan,  wane aiki ne agidan da sai kin samu mai aiki?  Ummu tace kawai ina so na samu abokiyar fira ne,  kaga idan ka tafi baka dawowa sai dare,  wani lokacin ma har sai nayi bacci kake shigowa, bazan iya zama ni d’aya ba. 

Alhaji yace ga Madu nan ai babu abinda zai sameki,  wallahi ina tsoron mu kawo abinda zai halaka mu. Marairaice fuska tayi tana fad’i kayi magana da Malan Sani kila ya samo mana tagari. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in shikenan,  tunda kince Malan Sani nasan bazai tab’a kawo mana abinda zai cutar damu ba. 

***

Koda ya samu Malan Sani da maganar sai yace akwai wata mata mai suna *Ladi*,  makwabtansu ne acan tsohuwar anguwarsu,  ta iya aiki dan tayi aiki sosai agidajen mutane,  yawanci abinda yake sa tana barin gidan aikinta wulakancin mutane,  wasu kuma idan taga ana aikata wani abu marar kyau bakinta baya iya shiru sai tayi magana,  wannan ne yake sa a koreta,  ko kuma idan aka so had’a baki da ita ayi cuta sai taki yarda to sai su rabu,  aikin da tayi na k’arshe wanda dagashi tace ta daina aikatau,  dalilin barinta gidan aikinta shine,   matar gidan tasa ta zuba ma kishiyarta guba a abinci,  data ki amincewa sai matar taso taja mata sharri ta zuba abincin a b’oye kuma ta kai maganin cikin kayanta,  gashi dama itace take dafa masu abinci,  sai akaci sa’a matar bata ci ba,  ta zuba zataci ta tashi ta shiga d’aki,  da yake suna da mage sai tazo ta saci nama taci,  tana gamaci ta fara shure-shure sai gawarta aka iske ga kumfa abakinta. 

Tunda aka ga haka akace guba ce a abinda taci,  da aka duba sai akaga abincin matar ne taci,  nan aka fara bincike sai ga magani an samu akayan Ladi,  da yake Allah yana tare da mai gaskiya sai tayi sa’a mai gidan ya yarda da rantsuwar ta ya sallame ta da kud’i yace ta bar aikin. Mutuncin da Mai gidan yayi mata yasa ta sameshi ab’oye ta fad’a masa gaskiya,  kuma ya yarda domin yasan halin matarsa. Tun daga lokacin ta dawo gidanta tace bazata sake aiki ba,  domin wata rana za’a jawo mata d’auri,  a bayan gidan mu take,  ita kad’ai take zama a k’aramin gidanta mai d’aki d’aya,  na mijinta ne daya mutu taci gado,  da ba anan suke ba cirani ya kawo su har ya samu ya gina gida suke zaune shekara da shekaru,  da ya rasu sai ta cigaba da zama dan tace bata da kowa,  hakan yasa take aikatau. To yanzu sana’ar k’osai takeyi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button