ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Jinjina kai Alhaji yayi cike da gamsuwa yace Malan Sani abun mamaki baya k’arewa a duniya,  gaskiya naji tausayinta,  kuma tunda ka yabeta nasan tana da hali mai kyau,  dan haka kayi mata magana sai muji yanda kukayi. Malan Sani yace insha Allahu bazaku samu matsala da ita ba. Alhaji yace amma ka fad’a mata gidan mu zata dawo da zama,  idan yaso sai ta bada hayar nata. Malan Sani yace angama. 

****

Cikin sa’a Malan Sani ya samu Ladi da maganar,  kasancewar Ladi tasan Malan Sani sosai,  kuma taji shima a gidan yake aiki hakan yasa ta amince. Sosai tayi farin cikin samun wannan aikin,  domin sana’ar babu kasuwa yanzu,  hakan yasa ta fara addu’ar samun aiki sai gashi Allah ya kawo mata. Babu b’ata lokaci ta amince tace zuwa jibi yazo suje gidan kafin ta samu wanda zai tsare mata gidan kafin a samu mai haya. 

Malan Sani yace Ladi haya a Lagos ai bata wahala,  ayau idan aka tallata gidan zaki samu wanda zai kama. Ladi tace yauwa dan Allah ka taya ni tallata gidan. Malan Sani yace insha Allahu,  abinda nake so da ke ki k’ara kok’ari akan wanda na sanki dashi, domin nasan kina da Amana da gaskiya. Ladi tace insha Allahu zan kiyaye. Sallama yayi mata yana fad’in sai nazo jibin,  idan kuma na samu wanda zai kama gidan zaki ganni. Ladi tace nagode sosai Malan Sani. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne,  Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar… 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k’asa,  idan kuma bank transfer zakayi ka  tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar.  08028525263.*

0⃣9⃣

Cikin kankanin lokaci Ladi ta fara aiki agidan su Ra’eez,  d’aki guda mai had’e da band’aki aka bata wanda yake a k’asa kusa da kicin,  basu dade ba suka saba da Ummun Ra’eez saboda Ladi mace ce mai tsafta,  kirki da natsuwa,  rayuwar Lagos ta ratsata shiyasa take a waye,  idan ka ganta sai kace bata manyanta ba,  domin sam jikinta baya nuna shekarunta,  yanda kasan tayi boko haka take,  gata da ilimin addini. 

Itace take shara,  guga da wanke-wanke,  sannan tana yima Ummun Ra’eez wanki da guga,  duk da a injin wanki ne takeyi,  abinci kuma Ummun Ra’eez ce takeyi duk da Ladi tana tayata wani abun,  haka idan tana da sako a kasuwa itace take zuwar mata saboda tasan ta kan kasuwa sosai. Ummun Ra’eez tana jin dad’in zama da Ladi sosai,  sam bata jin kad’aici yanzu. 

**** ***

Adebayo ne da Umar zaune a ofis d’in Alhaji Marusa,  bayan sun gama gaisawa Alhaji Marusa yace Adebayo maganar gaskiya hak’urina ya k’are,  jiya mukayi magana da Brr. Barau akan wannan mutumin Alhaji Maiwada,  duk wata dabara da zamuyi akan a d’aukeshi daga nan munyi amma abun yaki aiki,  Mr. Kallah ya fad’a mani bazai yuwu a canzashi yanzu ba,  da ace ba amatsayin shugaban kwastam aka kawoshi nan ba da tuni an canzashi,  amma yanzu dole sai nan gaba kafin a canzashi. 

Saboda haka jiya na yanke shawara ina ganin idan muka bita zamu samu mafita. Adebayo yace Alaji wace shawara ka yanke?  Murmushi yayi yana fad’in mai zai hana idan kayana suka shigo musan yanda zamuyi a b’oye wasu idan yaso sai muce shine ya kwashe su. 

Gyara zama Umar yayi yana fad’in Alhaji akwai abinda nake zargi a wajen Alhaji Maiwada,  ina tunanin kamar ya samu wani canji mai tsoka,  domin da alama ya maido Iyalinsa nan garin,  ada nasan agidan haya yake zaune,  domin lokacin da yazo aka nemi abashi gida yace baya so,  to sai yaje ya kama haya,  abinci ma direbanshi yake siyo masa alokacin na gane Iyalinsa basa nan,  to a kwanan nan naga canji sosai,  da alamu ya maido Iyalinsa nan,  domin ina ganin Malan Sani yana kawo masa abinci da azahar tayi,  kulolin da ake zubo abincin sun sha bamban da abinda yake kawo masa abinci da,  sannan alamu sun nuna ya tashi daga tsohon gidanshi,  domin shekaran jiya ina bayansu naga ba hanyar tsohon gidanshi suka bi ba,  kuma alokacin ya tashi gida zaije. 

Alhaji Marusa yace ko dai yayi sabon gini ne?  Umar yace da alama,  domin hanyar da naga yabi wajen Surelere ne. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in kasa mashi ido,  idan har zargin mu ya zama gaskiya ina mai tabbatar maku Alhaji Maiwada ya shigo hannu. 

Murmushi Adebayo ya saki yana tambayar Umar abinda suka fad’a dan be fahimta duka ba. Bayani Umar yayi masa. Saurin tashi yayi yana fad’in idan ya kasance gaskiya yayi gini Alaji kabarni dashi,  zan kulla masa sharrin da zaiyi kuka. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad’in nasanka Adebayo baka da kyau,  idan kana nan bani da sauran damuwa,  dan haka na baka wuka da nama. Jinjina kai Adebayo yayi. Kud’i masu yawa Alhaji Marusa ya basu kafin suka tafi. 

**** ***

Lab’e su Umar suke a wani waje suna kallo motar Alhaji Maiwada ta tsaya a bakin gate suna jira a bud’e masu. Mamaki ne ya kamasu ganin irin tsalelen gidan da zasu shiga. Basu gama mamaki ba sai da aka bud’e k’ofar gidan,  k’ara matsowa sukayi domin su gane ma idanuwan su. 

Bayan da suka shiga Madu ya rufe k’ofa. Umar yace Adebayo ka gani ko?  Adebayo yace tunda naga sun shigo wannan unguwar nasan Sir ba k’aramin sata yayi ba,  kalli yanda gidan yake kamar na shugaban k’asa. Umar yace ka bari yashiga dole muje wajen maigadin muji ko gidansa ne ko kuma haya yakeyi. 

Suna nan sai ga Malan Sani ya fito daga gidan shi kad’ai suna sallama da Madu,  dan anan yake barin motar yana hawa ta haya,  duk da Alhaji yace yarik’a tafiya da ita amma Malan Sani yace nan yafi tsaro acan yana tsoron b’arayi. 

Har suka gama sallama da Madu yazo ya wuce su be gansu ba. Bayan ‘yan mintuna suka fito suka nufi gidan. Umar yace Adebayo ka tsaya anan,  bana so maigadin yayi saurin gane mu,  kaga idan ya fad’ama Alhaji akwai wanda baya jin hausa zai iya d’agowa,  dan haka ka tsaya naje. Murmushi Adebayo yayi yace shikenan kaje. 

Madu yana zaune yaji alamun sallama daga waje. Lek’awa yayi sai yaga Umar atsaye. Fitowa yayi ya bashi hannu suka gaisa. Umar yace sannu da aiki kayi hakuri na tadoka kana zaune. Madu yace haba ai bakomai,  dama aikina ne na kula da k’ofar ai. 

Umar yace ni bako ne,  akwai gidan da akayi mani kwatance anan unguwar gashi nazo kuma wayata ta mutu bare nakira azo a d’auke ni kuma kwatancen ya b’ace mani shine nace bara nayi tambaya. 

Madu yace ka kyauta kuwa,  domin matambayi baya b’ata,  ya sunan Maigidan da kazo wajenshi?  Murmushi Umar yayi yace ina neman gidan Alhaji Hamza mai naira ne. Murmushi Madu ya saki yana fad’in duk da sabon zuwa ne ni nasan Alhaji Hamza,  muma ba mufi wata biyar da muka dawo nan ba,  maigidana ne ya gina wannan gidan shine muka dawo kasan shine shugaban kwastam. 

Umar yace lallai kace agidan shugaban kwastam kake aiki,  lallai kaja kaya abokina. Madu yace sosai kuwa,  domin Alhaji ba ruwansa,  yana da kirki sosai,  yafi shekara biyu da rabi yana gina wannan gidan sai wannan shekarar muka dawo bayan ya d’auko Iyalinsa. Umar yace kaji dad’in ka,  ina ne gidan Alhaji Hamzan? 

Madu yace da ka shiga wancan layin zakaga gida mai babbar katanka fitilu sun haske layin,  gidanshi yafi na kowa tsawo a layin zaka ga hada sojoji a k’ofar gidan. Umar yace nagode sosai. Madu yace bakomai agaida gida. 

Har ya k’arasa wajen Adebayo yana mamakin irin kud’in da Alhaji Maiwada ya kashe a wannan gidan. Yana zuwa yaja Adebayo suka nufi wajen da suka aje motar su. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button