ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 11 to 20

Sai da suka bar unguwar sannan Umar ya fad’a ma Adebayo komai. Hannu Adebayo ya tafa yana fad’in da kyau,  anzo wajen,  wallayi sai Sir,  yasan yayi mana rashin mutunci,  wannan gidan daya gina sai yayi danasani,  ya hana mu jin dad’i ya tsare komai ashe kanshi yake tarama kud’i,  kalli gidanshi kamar na babban d’an siyasa,  Umar ka bani zuwa gobe zan nemo shawara. Dariya Umar yayi yace bana jinka Adebayo. 

***

Tun da safe Malan Sani yazo domin yau da wuri zasu fita. Ummun Ra’eez ce ta fito daga kicin hannunta rik’e da kwandon abincin data zuba masa. Kallonta Alhaji yayi yana fad’in sannu Ummun Ra’eez. 

Murmushi tayi tana fad’in sai kace nayi wani aiki babba. Alhaji yace aiki ne mana,  yanda kike faranta mani Allah ya faranta maki kema. Murmushi tayi tace amin Abbun Ra’eez. 

Amsa yayi yana fad’in yau zamu kai dare saboda wasu kaya za’a kawo kuma dole na tsaya a gama duba su domin kayan Alhaji Marusa ne kuma kinsan na fad’a maki yana shigo da kaya marasa kyau yanzu ne abun yayi sauki dana saka ido,  amma duk da haka idan aka kawo kayan manyan mutane dole sai na tsaya na duba duk da yanzu komai yayi sauki. 

Ummun Ra’eez tace to Allah ya tsare mun kai,  ya kareka daga sharrin mahassada,  domin wannan aikin naku akwai had’ari,  domin mutane basa son gaskiya gashi kai mutum ne mai gaskiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in kome zai faru dani bazan bari a aikata b’arna ba sai dai kawai addu’a. 

Ummun Ra’eez tace to Allah ya tsare. Yace amin,  yauwa na manta ban fad’a maki ba su Ra’eez zasuyi hutu amma nace ma Alhaji Mansur kada akawoshi ya zauna tunda sabuwar islamiya aka maidasu idan muka samu lokaci sai muje,  wani hutun sai yazo ko sati daya yayi. Ummu tace bakomai nima nafison ya zauna yayi karatu ai. 

Har bakin k’ofa ta rakoshi tana masa addu’a,  sai da ya fita kafin ta koma ciki. Malan Sani yana ganin Alhaji ya fito yayi saurin tasowa ya amshi kwandon hannunsa yasa a mota. Bayan sun gaisa da Madu suka fita. A mota ma labarin kayan da za’a kawo Alhaji yake bama Malan Sani har suka isa ofis. 

***

Yau har karfe biyun dare Alhaji yana ofis ana duba kaya,  aciki kuma sai da aka samu abinda aka fitar kafin yasa hannu suka gama biyan komai ya sallame su,  sauran kayan kuma yace sai zuwa gobe za’a duba,  acikinsu akwai sauran na Alhaji Marusa aciki. Haka sukayi sallama suka tafi hadasu Adebayo. 

Aranar dole Alhaji yasa Malan Sani ya tafi da mota saboda dare yayi. Bayan ya ajeshi yashiga ciki shi kuma ya wuce. Gaiswa sukayi da Madu wanda har yayi bacci,  bayan ya shiga ya rufe k’ofar shima yashiga d’akinsa domin Alhaji yace yarika shiga d’aki yana baccinsa idan ya dawo Allah ne mai tsarewa tunda suna addu’a. Hakan yasa da Alhaji ya dawo Madu yake kulle k’ofa yashiga ciki. 

***

Washe gari kasancewar asabar ce yasa Alhaji bai fita da wuri ba,  duk da yasan yana da aiki akwai kayan da zaije ya duba yasa hannu kafin a d’auka amma ya kwanta domin jiya agajiye ya dawo yace sai zuwa goma sai ya fita. Tunda ya tashi kawai yake jin kasala da fad’uwar gaba,  wanka yayi sai yayi nafila ya zauna yana karatun kur’ani. 

Sai k’arfe tara da rabi ya fito domin ya karya. Zaune suke yana cin abinci,  kallonshi Ummun Ra’eez tayi tana fad’in Abbun Ra’eez yau sai naga kamar kana cikin damuwa ko?  Murmushi yayi yace kawai na tashi da mutuwar jiki da fad’uwar gaba ne. 

Hannunshi ta kamo tana fad’in kacigaba da addu’a nima ina taya ka,  insha Allahu babu abinda  zai faru da kai,  Allah yana tare da kai domin kana rike da gaskiyar ka. Alhaji yace nagode kicigaba da yi mani addu’a kinsan aikin mu. Murmushi tayi tana mika masa abinci abaki. Amsa yayi yana sakar mata murmushi,  da haka tacigaba da bashi abaki tana masa fira har yaji damuwar ta tafi. 

Bayan ya gama Malan Sani yazo ta rakashi tana ta masa addu’a suka tafi.

 Bayan da sukaje ofis suka kammala duba sauran kayan yasa hannu kafin aka d’auka. Aranar haka ya wuni baya jin dad’i,  ko la’asar beyi ba ya tashi suka dawo gida. 

**** 

 Washe gari tunda safe wayar Mr. Kallah ta tadashi,  yana ganin sunan sai da gabanshi ya faad’i,  d’auka yayi tare da yin sallama. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji jiya na samu waya daga Alhaji Marusa wai kayansa sunzo amma babu rabi acikin kayan kuma masu tsadar ne aka cire masa,  ya fad’a mani abubuwan da babu kuma naji babu abinda ya sab’a doka bare ace an ciresu. 

Ajiyar zuciya Alhaji ya saki yana fad’in Alhaji gaskiya babu wasu kaya da aka cire na Alhaji Marusa,  wani kwali guda biyu ne kawai aka cire acikin kayansa domin akwai abinda ya karya doka,  kuma agabana aka gama komai nasa hannu aka d’auki kayan kafin nabar wajen. 

Mr. Kallah yace Alhaji Marusa yace bazaiyi asara ba dole a nemo masa kayansa ko kuma yashigar da k’ara domin yana da hoton komai kuma an kawo masa kaya babu wasu aciki,  shiyasa nace bara na kira ka domin kayi bincike kafin yashigar da k’ara. Alhaji yace shikenan zan bincika tunda kace ayi haka. Sallama sukayi ya kashe wayar. 

Kai Alhaji ya dafe yana fad’in innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Da sauri Ummun Ra’eez ta tashi dan tunda aka kirashi ta farka. Dafashi tayi tana fad’in lafiya Alhaji?  Labarin abinda ya faru ya bata. Jinjina kai tayi tana fad’in kayi binciken kamar yanda ya fad’a,  gaskiya Mr. Kallah yana sonka da har ya iya kiranka ya fad’a maka,  kila dai bayan daka gama duba kayan aka samu matsala bayan ka bar wajen. 

Alhaji yace Ummun Ra’eez matuk’ar ba’a gano inda kayan suke ba akwai matsala,  domin kayan da suka b’ace na miliyoyin kud’i ne,  dole Alhaji Marusa bazai kyale ba domin hakan zai jawo masa babbar asara,  dole ma yashigar da k’ara saboda kayan suna da tsada. 

Ummun Ra’eez tace yanzu idan ba’a gano inda suke ba mai zai faru kuma? Alhaji yace Allah kad’ai ya sani,  domin sai abun ya shafemu duk wani wanda yake wajen alokacin da aka duba kayan. Ajiyar zuciya ta saki tana fad’in insha Allahu haka bazata faru ba. 

Tashi yayi yana fad’in bara nayi wanka na fita. Ummun Ra’eez tace yau fa lahadi taya zaka fita da wuri haka. Alhaji yace dole na fita domin wannan babbar matsala ce. Waya ya d’auka ya latso Adebayo. 

Bayan ya d’auka ya fad’a masa su had’u ofis ya kira sauran wad’an da sukayi aiki ajiya da shekaran jiya. Adebayo yace Sir,  zanje coci anjima sai dai idan mun dawo. Alhaji yace na manta,  shikenan zan jira ku a ofis. Kashe wayar yayi ya kira Umar,  yana dauka yace su had’u a ofis. Kashe wayar yayi yashige band’aki. 

****

Zaune suke a d’akin taro kowa yayi shiru yana jimamin abinda ya faru. Alhaji ya rasa abinda yake masa dad’i,  tun d’azu da yazo yake bincike amma be samo komai ba,  har sauran ma’aikatan sukazo aka cigaba da bincike. Adebayo yashiga damuwa yanda kasan kayanshi ne. Sallah kad’ai take fitar dasu. 

Har yamma suna bincike amma basu gano komai ba,  sun duba komai gashinan kayan sunzo,  kuma an duba su amma gashi ba’a kaisu ba,  hatta da wad’an da suka d’auki kayan sun tabbatar iya abinda suka kai sune abinda aka basu. Sosai abun ya d’aure ma kowa kai,  haka suka gaji kowa ya tafi. 

Alhaji kuwa wajen Mr. Kallah ya wuce,  alokacin suna tare da Alhaji Marusa,  acan ma maganar d’aya ce Alhaji Marusa yace k’ara zai shigar,  gaba d’aya ya tashi hankalinsa saboda kaya ne na makudan kud’i suka b’ace. Mr. Kallah sai hakuri yake bashi amma yaki hakura,  yaki bari ma a cigaba da binciken yace yayi magana da lauyenshi gobe za’a shigar da k’ara. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button