ALKALI NE Page 21 to 30

D’aukar jakar kamfutar sukayi suka kamo Malan Sani suka fito dashi sai layi yake dan sam baya cikin hankalinsa. Turashi sukayi hanyar gate, sai da sukaga ya kama hanya yana tafiya yana layi kafin suka fice ta bayan gidan.
Saurin tasowa Madu yayi ganin Malan Sani yana tangad’i, kamoshi yayi yana fad’in lafi… Tsayawa maganar tayi ganin jini a jikinsa, zeyi magana Malan Sani ya tureshi har sai da ya faad’i yayi tafiyarsa ya fice daga gidan.
Yana fita su Lucky suna jiransa bakin k’ofa, saurin kamashi sukayi sukasa a mota suka tafi. Koda Madu ya lek’a sai kurar motar ya iske.
Mamaki ne ya kamashi, me yasamu Malan Sani haka? Me ya aikata acikin gida tunda yasan Ladi bata nan? Ga jini ajikinsa, ko dai wani abu yayima Hajiya? Ai kuma yaso yaji ihu, Saurin komawa Madu yayi, cikin gidan ya nufa jikinsa sai rawa yakeyi.
Yana shiga falo yayi mutuwar tsaye, da sauri ya fito yana gudu yayi wajen gidan yana neman taimako. Makwabcin su ya gani shida abokinsa, da sauri ya k’arasa wajensu jikinsa na kyarma.
Tsayawa sukayi ganin Madu. Makwabcinsu mai suna *Alhaji Musa* yace Madu lafiya kuwa? Kuka Madu yasa yana nuna masu cikin gidan. Mamaki ne ya kamasu sukace meya faru? Madu yace ya kasheta wallahi gata can a kwance cikin jini Alhaji.
Wanda aka kira da Alhaji yace waye ya kashe ta kuma wa aka kashe? Madu yace Hajiya ce, Malan Sani ne yashigo kuma shi kad’ai ya dawo ba tare da Alhaji ba, hannunsa d’auke da jaka kamar ta kud’i, yana shiga cikin gidan sai ihun Hajiya naji, band’au ka wani abu bane ina zaune sai gashi ya fito jikinsa duk jini, dana rik’esa saiya tureni ya fito, kafin na fito wata b’akar mota ta d’aukeshi sun bar wajen.
Abokin Alhaji yace tabbas naga bak’ar mota har nake maka magana nace mai motar can yana tukin hauka ashe da abinda suke ma sauri.
Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad’in lallai duniya babu gaskiya, yanzu bazamu shiga gidan ba, bara nayi waya a turo ‘yan sanda idan suka zo sai mushiga saboda tsaro.
***
Sai da suka d’auki yaron daya gano masu gidan Malan Sani sannan suka wuce unguwarsu, har k’ofar gida suka kaishi, kuma sukaci sa’a ba mutane a wajen, ajeshi sukayi suka kama gabansu.
Cikin layi Malan Sani ya k’arasa cikin gidansa yana rik’e da kanshi. Halima da Rumaisa suna zaune tsakar gida suka ga Malan Sani yashigo ko sallama babu. Da sauri Halima ta tashi tana fad’in Malan lafiya kuwa? Hannu ya d’aga mata, beyi magana ba yayi hanyar d’akinsa, bayansa tabi cike da damuwa ga jini ajikinsa duk sai hankalinta ya sake tashi. Yana shiga ya rufe k’ofar yasa mukulli, zubewa yayi saman gadonsa nan take nannauyen bacci ya d’aukeshi.
Kamo Rumaisa Halima tayi suka zauna nan take hawaye suka wanke mata fuska, gaba d’aya jikinta yayi sanyi ganin Malan Sani a cikin wani yanayi wanda betab’a shiga ciki ba.
***
Bayan ‘yan sanda sun gama bincike motar asibiti ta d’auketa aka nufi asibiti da ita dan sunce ba mutuwa tayi ba. Gaba d’aya unguwar hankalinsu atashe yake saboda abinda ya faru. Madu kuwa kamar wanda aka watsama ruwan zafi, gashi yakira Alhaji wayar bata shiga.
Ana shirin rufe gidan sai ga wata motar ‘yan sandan sunzo. Bayan sun shigo suka tambayi maigadin gidan. Madu ya taso yana fad’in gani nan. Tambayarsa sukayi nan ne gidan Alhaji Maiwada shugaban kwastam? Jiki a sanyaye Madu yace nan ne.
Hannu babban cikinsu ya mik’ama d’an sandan da suka samu, Alhaji Musa makwabcin su Alhaji ya matso yana tambayar lafiya? ‘Dan sandan yace mun samu gawar Alhaji Maiwada ne a motarsa shine akayi mana kwatancen gidansa, yanzu haka gawarsa tana asibiti an wuce da ita domin ayi bincike, tare ma muka kaita data wani yaro da muka tsinta itama anjefar, gaba d’aya de suna asibiti kafin mu samu Iyayen yaron.
Wani irin kuka Madu yasa yana fad’in shikenan shima ya kashe shi, kai Malan Sani ina zaka kai alhakin wad’an nan mutanan? Mutum ya d’auko ka cikin talauci ya taimake ka amma kazo kayi masa butulci.
Alhaji Musa ne ya kamo Madu yana fad’in ya isa haka, tunda hukuma tashigo ciki za’ayi bincike. ‘Dan Sandan yace kasan gidan Malan Sanin? Kai Madu ya d’aga yana fad’in sosai ma.
Kallon Alhaji Musa yayi yana fad’in Alhaji zamuje can gidan domin mutafi da Malan Sanin, idan akwai wani d’an uwan Alhaji Maiwada asanar masa domin dole a rufe gidan nan kafin su zo.
Alhaji Musa yace gaskiya danginsa ba anan suke ba, kuma bani da lambar kowa. Madu yace ina da lambar Alhaji Mansur a kano yake. Alhaji Musa yace kawo lambar asanar masa idan yaso sai arufe gidan ku tafi da mukullin wajen ku kafin yazo.
Bugu biyu Alhaji Mansur ya d’auka, ganin bak’uwar lamba yasa gabanshi ya sake fad’uwa. Bayan sun gaisa Alhaji Musa ya fad’a masa halin da ake ciki. Salati kawai Alhaji Mansur yakeyi jikinsa yana rawa, ya dad’e kafin yace gobe zai taho da wuri, sannan ya roki alfarmar Alhaji Musa ya kula da Ummun Ra’eez kafin yazo da matarsa. Alhaji Musa yace bakomai sai kazo.
Haka aka kulle cikin gidan Madu yace zai cigaba da zama kafin ya tafi dan shima bazai iya cigaba da zama ba. Haka ya kulle gate d’in yashiga motar ‘yan sanda suka nufi gidan Malan Sani, sauran ‘yan unguwa sai jimamin abinda ya faru sukeyi.
***
Har sun rufe gida taja Rumaisa d’akinta sun kwanta dan Rumaisa har tayi bacci, ita ko ta kasa baccin, tunanin halin da Malan Sani yake ciki kawai takeyi.
Jin k’arar buga gida yasa tayi saurin tashi tana lallubar fitila, hijabi tasa kafin ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsayawa tayi tana tambayar waye? Daga waje akace ‘yan sanda ne ki bud’e.
Jikinta ne ya tsananta rawa, da kyar ta iya bud’e k’ofar. Madu ta fara gani hakan yasa taji sanyi, kallonshi tayi duk idanuwanshi sunyi ja. ‘Daya daga cikinsu ne yace ina maigidan ki? Halima tace yana ciki ina jin beda lafiya dan ya kule k’ofar d’akinsa kuma ya dawo cikin wani yanayi.
‘Dan sandan yace muje ki nuna mana d’akin munzo tafiya dashi ne. Gabanta ne ya faad’i ta kalli Madu tana fad’in wai meye yake faruwa dan Allah? Matsawa Madu yayi gefe yana goge kwalla ya kasa magana.
Kuka Halima tasa tare da komawa ciki ta fara bubbuga d’akin Malan Sani. Shiru babu alamun motsi hakan yasan d’an sandan yace zamu b’alle k’ofar tunda bai bud’e ba.
Abun buge k’ofa suka samo haka suka bud’eta da k’arfi. Mamaki ne ya kamasu ganinshi kwance kamar gawa, da sauri Halima tayi ciki tana fad’in Malan na shiga ukku me yasame ka haka? Ciki suka shiga suna tsoron kada dai ace shima ya mutu shirin da Brr. Barau yayi ya rushe.
Komawa baya d’aya daga cikinsu yayi ya d’ebo ruwa, yana zuwa ya watsa mashi, a firgice ya tashi sai dai jikinsa babu kwari. Rungumoshi Halima tayi tana kuka tace Malan me yasame ka? Kallonta yayi idanuwansa suna rufewa amma ya kasa magana.
‘Dan Sandan yace Malama ki matsa muyi aikin mu kina b’ata mana lokaci, idan kina son sanin abinda ya aikata zaki iya zuwa ofis d’in mu gobe da safe amma yanzu dashi zamu tafi.
Kuka Halima tasa tana fad’in wallahi mijina ba me laifi bane, dan Allah kada ku tafi dashi. Murmushi d’an sandan yayi yana fad’in idan baki sani ba to mijinki makashi ne, domin ya kashe uban gidansa kuma ya nemi matarsa da alfasha yanzu haka tana asibiti.