ALKALI NE Page 21 to 30

A zabure Halima tayi baya tana binsu da wani irin kallo, hannu tasa ta rik’e cikinta jin yanda ya murd’a mata, ganin halin da take ciki yasa wani daga cikin ‘yan sandan yaji tausayinta, duk’awa yayi yana fad’in ki kwantar da hankalin ki, idan akayi bincike beda laifi babu abinda za’ayi masa.
Ajiyar zuciya Halima ta saki tare da sakin wani irin kuka. Tana ji tana gani suka rik’e Malan Sani dan bema iya tafiya saboda mutuwar jiki, sai kallonta yakeyi, yana so yayi magana amma ya kasa, hawaye ne suka zubo mashi, haka sukayi waje Halima tana zaune ta kasa tashi.
Jin k’arar motarsu yasa tayi saurin tashi, mararta ce ta murd’a hakan yasa ta duk’e tana cije baki, ta jima ahaka kafin ta dafa bango har ta kai k’ofa, tsayawa tayi tana kallon kurar motarsu hawaye suna wanke mata fuska. A hankali ta maida k’ofar ta rufe kafin ta koma d’aki ta fashe da kuka.
***
Wai Baffan Naseer har yanzu baka samu wayar tashi ba? Ajiyar zuciya Baffa yayi yana fad’in duk kiran da nakeyi wayarsa akashe take, gaba d’aya hankalina ya tashi domin Naseer baya kai dare awaje.
Mama tace kuma fa gidansu Mannir yace zaije a masallacin unguwar nan ma yayi sallar magriba. Baffa yace ba agida nayi sallah ba da bazan barsa yaje ba, idan ma yace dole yaje sai dai na kaishi da kaina, kinsani sarai bana son yawon dare.
Mama tace kayi hakuri gani nayi yace littafinsa zai amso. Baffa yace wai baki da lambar shi Mannir d’in? Mama tace ina da ita dan Naseer ne ma ya ajeta saboda wata rana yana kiransa da wayata.
Baffa yace bani lambar. Bugu biyu Mannir ya d’auka, bayan sun gaisa suka tambayeshi Naseer. Shiru Mannir yayi yana mamakin Naseer baya gida, yace masa zaizo da yaga shiru ya d’auka ko agida aka hanashi…. Labarin yanda sukayi da Naseer ya fad’a masu.
Jiki asanyaye suka masa godiya. Hawaye ne suka zuboma Mama tana fad’in kada dai ace saceshi akayi. Baffa yace banga ta zama ba bara na kira DPO gara mushigar da k’ara da wuri.
Suna gama waya da DPO yace yajirashi zaisa yaranshi suje su duba. Zama sukayi gaba dayansu jiki amace.
Can wajen sha biyun dare DPO yakira Baffa, yana d’auka yace masa ya tura yaranshi zasuyi bincike, amma wani yace an kai wasu gawawwaki guda biyu d’azu asibiti data babban mutum data yaro, ko zasuje su duba? A zabure Baffa ya tashi yana fad’in yanzu zan fito DPO mu had’u a asibtin. Da sauri DPO ya amsa saboda Baffa babban mutum ne akwai naira.
Tare suka tafi hada Mama sai kuka takeyi domin Naseer shine autan ta, yaranta biyu babban yana can abuja yana karatu.
***
Kuka kawai sukeyi asaman gawar Naseer, Mama tana fad’in su waye ne suka maka haka Naseer? Ya Allah ka saka ma bawanka. DPO yace Alhaji kuyi hak’uri insha Allahu zamuyi bincike, idan muka gano wad’an da suka aikata haka dole ashigar da k’ara kotu.
Jinjina kai Baffa yayai kafin suka wuce domin su amshi gawar. Likita yace zasuyi bincike dole su bari zuwa safiya tunda ba yau za’a rufeta ba. Baffa yace ayanzu zakayi binciken ka bani gawar Yarona, gara naje na kwana ina masa karatu daya kwana anan. Jikin likita yana rawa yace angama.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣6⃣
Washe gari ko da Malan Sani ya farka sai ya dawo cikin hankalinsa, tashi yayi yana dafe kanshi da yake masa ciwo, a hankali abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo masa, tun daga shigarsa gidan Alhaji har abinda ya faru ya fito ya shiga mota har zuwanshi gida, iya nan kawai ya iya tunawa sai kuma yau daya tashi.
Da sauri ya d’aga kai yana sake kallon inda yake, mamaki abun ya bashi, yasan dai yashiga d’akinsa amma gashi a wajen ‘yan sanda. Runtse ido yayi yana salati tunawa da abinda ya faru, kada dai sun kashe Ummun Ra’eez? Saurin sa hannu yayi a wuyansa, zafi yaji a wajen dan har yayi fushi saboda yakushin da sukasa Ummun Ra’eez tayi masa, a hannunsa yana jin shatin faratan ta.
Girgiza kai yashigayi hawaye suna zubo masa, tabbas yasan yashiga tsaka mai wuya Allah ne kad’ai zai iya fitar dashi, domin wannan abun daya faru yasan duk shirin su Alhaji Marusa ne. Dafe kai yayi yana kuka, ko a wane hali Halima take ciki yanzu? Jin motsi yasashi saurin d’agowa.
Wani d’an sanda ne yazo wajenshi dan yaga beyi sallah ba kuma shi zai tafi shine ya matso yaji ko yana da buk’atar yayi sallah, dan tunda aka kawoshi jiya yana zaune a ofis kawai yaji ya tausaya mashi, yanayin da aka kawoshi yasan akwai abinda ya sha ko kuma akasa mashi.
Saurin tashi Malan Sani yayi yana fad’in dan Allah inaso nayi sallah kaga har gari yayi haske sosai. Murmushi d’an sandan yayi yana fad’in ai tun d’azu naga kana bacci shiyasa ban tasheka ba, fito ga wajen sallah can.
***
Mota ce ta sauke Alhaji Mansur da Matarsa a k’ofar gidan Alhaji Maiwada saboda ta jirgi suka zo. Idanuwan Maman Labiba har sun kumbura saboda kuka, shikanshi Alhaji Mansur idanuwansa sunyi ja saboda ba k’aramin tashin hnkali yashiga ajiya ba.
Isowar Alhaji Musa ne yasa suka k’arasa cikin gidan saboda da suka zo basu shiga ba. Da sauri Madu ya taso yana masu sannu da zuwa, shima duk jikinsa a sanyaye yasha kuka.
Bayan sun gama gaisawa suka jajanta abinda ya faru, anan Alhaji Mansur yayima Alhaji Musa godiya sannan yace su wuce asibitin domin a gama komai a basu gawar Alhaji ayi masa sutura.
Alhaji Musa yace shikenan bara na d’auko mota ta sai mutafi, zansa a kawo tabarmi saboda zaman gaisuwa, Madu sai ka gyara cikin rumfar can idan suka kawo sai a shimfid’a. Kai Madu ya d’aga yana share kwallah.
***
Sosai Abubakar da Moses suka tsorata da abinda sukaji, gashi su Peter basu kyalesu haka ba sai da suka basu wahala sosai, domin a wajensu suka kwana, sun jigata sosai, haka kuma sunyi kukan mutuwar Alhaji Maiwada da Malan Hassan, Abubakar yanaji kamar laifinsa ne, da be sako Malan Hassan a cikin wannan abun ba da haka bata faru dashi ba, gashi babu halin yaje ya sanar da Iyalinsa yanzu za’a tsareshi ya nuna gawarsa kuma besan inda take ba, hakan kuma zai sashi cikin matsala,, dole ya bar abun sai dai Allah ya basu hak’uri.
Shigowar Lucky da Peter ne yasa sukayi saurin kallon su. Matsowa Lucky yayi fuska babu annuri yana fad’in kunci sa’a ba’a bamu umarnin kashe ku ba, kashedi kawai akace muyi maku, nasan zuwa yanzu jikin ku ya fad’a maku abinda muke nufi, dan haka zaku samu takardar canjin wajen aikin ku da zaran litinin tayi, matuk’ar kuka sake nuna kan ku ko kuma wani yaje neman wata sheda akan ku zamu kashe kowa naku.
Cike da tsoro Moses yace wallayi aboki bazaka sake gani na a lagos ba, tsautsayi ne yasa nayi haka, amma na goge komai bani da wata sheda kada ku kashe ni.
Abubakar yace insha Allahu bazaku sake ganina a lagos ba koda da yawo, kuma babu abinda zan fad’a, bazan barima asan nasan wani abuba, dama bani da iyali anan suna can dan haka ayau zan bar garin.
Murmushi Lucky da Peter sukayi kafin suka kwance su, hannu suka rik’e saboda tsamin da yayi masu, ga kansu da yake ciwo saboda abinda suka shak’a masu. Haka suka d’aure masu fuska suka fita da su.