ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

***

Kuka kawai Maman Labiba takeyi alokacin da taga gawar Alhaji Maiwada, Alhaji Mansur kanshi kasa daurewa yayi, juya baya yayi ya saki wani irin kuka, Alhaji Musa ne yayi ta bashi baki. 

Gaba d’aya gawar Alhaji ta canza kama, fuskarsa duk da kumbura, wuyansa yayi wani irin ja gwanin tausayi. Brr. Barau ne tare da d’an sandan da yake kula da case d’in Alhaji suka shigo. 

Hannu suka bama su Alhaji suka gaisa, kallon Alhaji Mansur yayi yana fad’in sunana Brr. Barau, kuma nine lauyen da zan kula da wannan shari’ar ta Alhaji Maiwada, domin nine lauyensu na wajen aiki, bazamu tab’a bari jininsa ya zuba abanza ba, duk wanda yake dasa hannu akisanshi sai mun kamashi, to abun yazo da sauki domin an kama direbansa da ake zargin shine ya kashe shi, saboda an kamashi da laifin yima matar Alhaji fyad’e har yayi sanadiyar zubewar cikinta, yanzu haka yana kulle. 

Tunda ya fara magana Alhaji Mansur ya zuba masa ido har sai da Brr. Barau ya tsargu da kallon da yake masa. Gyaran murya yayi yana fad’in kada ka damu Alhaji zanyi aiki sosai akan mutuwar Alhaji Maiwada. 

Kauda kai Alhaji Mansur yayi yana jin wani irin tukukin bakin ciki, yasan komai akan Brr. Barau, domin babu abinda Alhaji Maiwada ya b’oye masa, amma kaji saboda rainin hankali wai shine zai tsayama Alhaji, gashi sun kullama Malan Sani sharrin da babu mai fitar dashi sai Allah, tabbas yasan sune suka aikata hakan, amma iya abinda ya sani a baki ya tsaya beda sheda ko kad’an a hannu, ita kuma kotu da sheda take amfani, dole yasa ido yaga yanda komai zai kasance, idan aka cutar da Malan Sani sai dai Allah ya saka masa. 

Muryar Alhaji Musa yaji yana fad’in bakomai Brr, mungode sosai, gaskiya ka kyauta da zaka tsaya domin a kwatoma Iyalan Alhaji Maiwada hakkinsu, domin har yanzu ita Hajiyar bata farfad’o ba, shi kuma wannan direba ayi masa hukunci dai-dai dashi domin hakan ya zama darasi a wajen ‘yan baya. 

Brr. Barau yace insha Allahu babu abinda zai gagara. Alhaji Mansur yace yanzu dai muna so a bamu gawar Alhaji muje mu suturta ta. Brr. Barau yace nima abinda yasa nazo kenan saboda nasan Alhaji Maiwada beda kowa a garinnan shiyasa nazo domin an fad’ama wajen aikinsu suna jira suji lokacin jana’izar domin suzo a suturtashi. 

Dan sandan yace ai duk wani bincike mungamashi, duk wani abun daya kamata anyi dan haka zakuje wajen likita ku gama dashi sai abaku gawar, sannan motarsa nasa yarana su kaita gidanshi yanzu. Jinjina kai sukayi kafin suka nufi ofis d’in likita. 

Haka aka gama komai aka basu gawar Alhaji Maiwada, acikin motar asibiti aka d’aukeshi saboda babban mutum ne, a motar Alhaji Musa suka tafi. 

***

Kafin wani lokaci mutuwar Alhaji Maiwada ta yad’u, manyan mutane duk sun halarci k’ofar gidansa domin ayi masa sallah, ‘yan wajen aikinsu gaba d’aya sun halarci wajen, Malan Bala sai kuka yakeyi yana tuna rabuwarsu da Alhaji jiya, ko kud’in daya bashi bai gama kashe su ba amma wai ya rasu. 

Kafin wani lokaci an gama shirya Alhaji, haka mak’udan mutane suka taru aka sallaceshi, kafin Alhaji Marusa ya iso har an sallame, yana zuwa sai dai ya juya domin rakiyar kai gawa. Mr. Kallah kuwa yana gida sai sun dawo zai zo masu gaisuwa, gaba d’aya hankalinsa tashe yake, tunda Alhaji Marusa ya kirashi ya fad’a masa an kashe Alhaji yake jin babu dad’i aransa, amma babu yanda ya iya dole ya bar komai aransa tunda mai faruwa ta faru. 

Hatta da Abubakar sai da yazo jana’izar Alhaji, duk da baya jin dad’in jikinsa amma haka yazo saboda yana tsoron rashin zuwanshi yasa a zargeshi musamman da mutane suka san suna shiri da Alhaji. 

Bayan an dawo daga binneshi aka shiga yima juna gaisuwa, sauran abokan aikinshi wad’an da ba musulmai ba haka suka fara zuwa suna gaisuwa, Mr. Kallah ma yazo gaisuwa kuma ya zauna a kusa da Alhaji Marusa anan aka cigaba da zaman gaisuwa dasu. 

Cikin gida kuwa Maman Labiba itace Uwar amsar gaisuwa, matan unguwa duk sunzo suna tayata zaman makoki, abinci kuwa azahar tanayi aka fara shigo dashi kuloli, abunka da birni sai dai akawo abinci daga waje, *sab’anin wani wajen da zaka iske masu mutuwa sune suke ciyar da ‘yan zaman makoki, d’an abincin da suka samu sadaka kafin a share makoki mutane sun cinye wasu hada guzirin na gida*.

***

Sai da Ummu tayi kwana d’aya da yini kafin ta farka, Hajiya Amina matar Alhaji Musa tana zaune a gefenta tayi saurin tashi ganin tana motsi, hannu Ummu tasa ta dafe kanta, da k’arfi ta saki ihu tana kiran Abbu. Saurin matsawa Hajiya Amina tayi tana rik’eta. 

Shigowar wata ma’aikaciya ne yasa Hajiya Amina ta matsa domin ta bata waje, ganin yanayin da Ummu take ciki yasa ma’aikaciyar tayi saurin danna wata alama, kafin wani lokaci sai ga likitoci sun shigo. 

Fita Hajiya Amina tayi cike damuwa. Haka suka shiga duba Ummu, ganin ta kasa natsuwa yasa dole sukayi mata allurar bacci kafin suka gungurata zuwa wani d’akin gwaji. 

***

Alhaji Mansur ne da Alhaji Musa suka iso da sassarfa dan Hajiya Amina ta kirashi shine suka taho, Alhaji Mansur yaso ya taho da matarsa amma baya so abar gidan abud’e saboda basu san halin wasu ba. 

**

Zaune suke a ofis d’in babban likita. Bayan ya gama ‘yan rubuce-rubuce ya d’ago kai yana fad’in agaskiya Hajiya ta had’u da lalurar tab’in hankali sakamakon dukan da akayi mata akai da kuma abinda yashiga zuciyarta na tsorata, sannan cikin jikinta ya zube, yanzu haka munyi mata allurar bacci saboda jikinta babu kwari muna buk’atar ta samu hutu shiyasa mukayi mata allura, idan ta samu saukin ciwon jikinta dole zamu maidata asibitin mahaukata wanda nine zan mayar da ita can saboda takasance matar Alhaji Maiwada, tunda na fahimci tana d’auke da wannan lalurar nayi alk’awarin zan kula da ita. 

Salati Alhaji Mansur yayi yana fad’in Allah mungode maka da wannan jarabawa taka, ya Allah ga baiwarka nan Allah kada ka mayar da Ra’eez Maraya gaba da baya, ya Allah ka bata lafiya. Gaba d’ayansu sukace amin. 

Alhaji Mansur yace amma likita ina da magana, inaso idan ta samu sauki zamu maidata Kano domin zatafi samun kulawa akusa damu, kuma haka ne kawai zanyi na kyautata ma Alhaji Maiwada, domin yanzu bani da burin daya wuce na rike iyalinsa, kuma na cika masa burinsa na barin garin nan da yayi niya. 

Gyara zama likita yayi yana fad’in ban tari numfashin ka ba Alhaji, dama tunda naji Alhaji Maiwada beda ‘yan uwa agarin nan nake jiran wani nashi yazo domin na nemi wannan alfarmar, naroke ka da girman Allah ka barni na samu wannan ladar, Alhaji Maiwada yana da muhimmanci agaremu, ta silarsa Yayana Alhaji Usman ya samu kayansa da aka sace suka fito tun yana farkon zuwa garin nan, Yayana tunda yaji wannan labari yace shine zai d’auki nauyin kud’in jinyar Matar Alhaji, ayau da muka gano matsalar da take ciki nayi alk’awarin zan kaita wajen abokina da yake kula da masu irin wannan lalurar, kuma acan asibitin zata zauna har Allah ya bata lafiya, sannan idan tana garin nan zatafi saurin dawowa hankalinta tunda anan abun ya sameta. 

Shiru Alhaji Mansur yayi dan likita ya d’aureshi, ajiyar zuciya ya saki yana fad’in shikenan likita bazan hanaka aikata aikin alkhairi ba, nasan abubuwan alkhairin da Alhaji Maiwada yayi sune suka jawo masa haka, dama ance idan kana aikin alkhairi ko bayan mutuwarka aikinka yana nan, bakomai Allah ya baka lada, kuma zamucigaba da magana ta waya ina jin halin da take ciki. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button