ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

Godiya likita yayi masu, anan sukayi musayar waya Alhaji Mansur yace da anyi sadakar ukku zasu tafi, kafin lokacin yana so su gana da wancan likitan. Murmushi likita yayi yana fad’in babu damuwa. 

Alhaji Musa yace ‘yan sanda sunzo nan kuwa likita? Likita yace sunzo tun a washe garin ranar, sun d’auki hoton shatin hannun Hajiya na dama wanda naga jini acikin k’umbarta, sai sukasa mukayi awon jinin da yake cikin farcanta muka basu sakamakon, sai dai sunce fyad’e akayi mata amma gaskiya babu alamun haka, kila dai garin yin fyad’en ne cikin ya zube, ganin jini yasa sukace fyad’e ne, amma gaskiya babu wani fyad’e. 

Girgiza kai Alhaji Mansur yayi wani takaici ya turnuk’eshi, gashi dai yasan gaskiyar wasu al’amuran amma beda halin magana. Tashi yayi yana fad’in likita mungode sai mun had’u a kotu ranar litinin dan nasan bazasu ja shari’ar ba, idan angama da wuri zamu wuce saboda ranar ne sadakar ukku. Godiya yayi masu suka fita. 

Alhaji Mansur yaso Hajiya Amina tazo su koma gida itama ta huta amma Alhaji Musa yace ai babu komai baza’a bar mai jinya ita kad’ai ba. Haka suka tafi bayan sun aje masu abincin da suka zo dashi. 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button