ALKALI NE Page 21 to 30

Cikin kuka Ummun Ra’eez tace dan Allah Abban Labiba ka barsa ya siyar dashi, kasashi ya aje har aikin mu koma kano da zama wallahi bana son garin nan. Hannu Alhaji yasa ya kamo hannunta yana fad’in kada ki sake fad’ar haka Bilkisu, idan na aje aikina kamar ban yarda da k’addara bane, kuma zuciyarsu zatayi sanyi tunda sun sa na aje aikina, idan kinga na bar aikina to takardar sallama aka bani, amma matuk’ar basu bani ba to mutuwa ce zatasa nabar aikina sai kuma idan lokacin aje aikin yayi, dan haka matuk’ar kina sona ki tayani cin wannan jarabawar da Allah ya d’ora mani.
Jinjina kai tayi tana goge ido tace shikenan Abbun Ra’eez, na amince ka siyar da gidan, ina maka addu’a akan Allah yayi maka sakayya akan zaluncin da akayi maka, kuma ya baka ikon cigaba da aikin ka.
Alhaji Mansur yace amin, nima na amince da abinda kace, bakomai Allah ya shige mana gaba. Alhaji Maiwada yace amin, ka kira DPO ka sanar masa zan siyar da gidana, nasan Alhaji Marusa ne zai siyeshi kaga sai ya fad’a masa, akira dillalai suzo suyima gidan kud’i, idan na biyasu zan sayi wani gidan sai mu koma can da zama.
Kwalla Alhaji Mansur ya goge yana fad’in Allah ya saka maka. Alhaji yace amin.
**** ****
Cikin kwana biyu aka gama komai, dillalai suka yima gida kud’i akan naira miliyon d’ari biyu, tayin farko wanda Alhaji Marusa ya aiko yace ya siya, haka aka gama komai aka mik’a masa takardun gida shedu suka sheda, dama acikin kwana biyun Alhaji ya kwashe kayansa, a unguwar *APAPA* ya samu wani gida mai kyau kuma aka sayar masa akan naira miliyon tamanin, nan take ya amince.
Bayan da aka mik’a masa kud’insa agaban ‘yan sanda da hukumar bincike sukaje shida Alhaji Mansur da Malan Sani suka biya Alhaji Marusa naira miliyon saba’in da biyar da ya buk’ata, bayan da aka gama cike-cike suka bar wajen.
Kud’in gidansa ya biya sauran kud’in yasa a banki. Alhaji Mansur gudummuwar milayan d’aya ya bashi amma da kyar ya amsa, haka abokinsa Alhaji Usman wanda ya tab’a kwatoma kayansa shima sai da ya bashi dubu d’ari biyar, haka mutanan da suke mutunci suka rik’a kawo masa gudummuwa.
Bayan sun maida kayansu zuwa sabon gidansu suka gyara ko ina, gida ne mai kyau, sai dai ba me bene bane, bangare biyu ne, wanda d’ayan bangaren yake kamar d’akunan maza, sai babban b’arin mai d’auke da babban falo, sai kicin mai had’e da sito, sai wani d’aki akusa da kicin mai d’auke da band’aki wanda yake amatsayin na masu aiki, daga can kuma zaka shiga wata hanya mai d’auke da d’akuna biyu dukkansu da band’aki aciki, wannan shine b’angaren matar gidan, daga gefen falo akwai d’aki wanda shine na maigida, sai wajen teburin cin abinci. Daga waje kuma akwai d’akin mai gadi sai harabar gida da wajen aje motoci sai rumfa.
Sosai Ummun Ra’eez taji dad’in gidan dan ya burgeta, haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki duk damuwar da take ciki sai ta tafi. Haka suka gyara komai dama gidan besha wahala ba, Ladi tasa kayanta a d’akin ta, kayan Ra’eez kuma aka aje masa a d’akin da yake na kusa da Ummunsa.
**
Bayan kwana biyu Alhaji Mansur yayi masu sallama ya koma yana mai sake kwantar ma Alhaji Maiwada da hankali, haka ya tafi cike da tausayin abokinsa.
Malan Sani yaji dad’i da suka samu gida a wannan unguwar saboda baya so ace sun bar unguwa mai kyau sun koma marar kyau, sai gashi itama wannan d’in tana da kyau.
Tunda wannan abu ya faru Alhaji be lek’a ofis ba, yana jiran yaji halin da yake ciki, babu inda yake zuwa sai masallaci, sosai hankalinsa ya kwanta dan ya dage da addu’a hakan yasa Allah ya yaye masa damuwar da take ransa yasa masa dangana, duk yanda yake tunanin mutanen gari zasu yaya tashi sai Allah ya kwantar da abun, wanda ba haka su Alhaji Marusa suka so ba.
Suna kwance ad’aki ya samu kira daga Mr. Kallah, bayan sun gaisa ya sake jajenta masa akan abinda ya faru, anan yake fad’a masa gobe ana nemansa a can abuja. Alhaji Maiwada yace nagode kuma zan zo akan lokaci. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Ajiyar zuciya ya sauke yana fad’in ya Allah ka zab’a mani abinda yafi alkhairi akan wannan aikin. Hannunsa Ummu ta kamo tana fad’in nemanka ake ko? Kai ya d’aga mata. Murmushi tayi tana fad’in nasan mijina mai tawakkali ne, kuma nasan zaka amshi duk abinda yazo maka da hannu biyu, dan haka kada ka damu da kiran da suke maka, idan su basa tare da kai ni da Ra’eez muna tare da kai har abada.
Murmushi ya saki wanda har hak’oransa sai da suka fito, sake matseta yayi yana fad’in nagode Uwar gidana, ina mai tabbatar maki matuk’ar suka barni akan aikina sai na zaluko gaskiya, ko bayan raina sai duniya tasan cewar bani da laifi, sai Allah ya haska su kowa ya gansu.
Ummu tace amma kayi komai a hankali kada su sake maka wani sharrin. Alhaji yace kada ki damu, wannan abun da ya faru alkhairi ne a wajena, domin ya k’ara haska mani duhun da nake ciki, ayanzu zasu gane basu da wayau, domin zanyi aiki ta k’ark’ashin k’asa. Murmushi tayi tana fad’in nasan zakayi fiye da haka.
**** ****
Cike babban d’akin taron yake da manyan mutane masu babban matsayi, bayan da aka gama tattaunawa kowa ya fad’i ra’ayinsa akan Alhaji Maiwada, wasu suna ganin ayi masa canjin wajen aiki tare da rage masa matsayi, wasu suna ganin takardar sallama ce ta dace dashi domin yaci amanar aikinsa, idan aka barshi hakan zai bama wasu dama su aikata irin abinda yayi ko fiye da haka, wasu suna ganin a bashi takardar jan kunne.
Bayan da kowa ya gama kawo tasa shawarar Mr. Kallah ya mik’e yana fad’in naji duk abinda kuka fad’a, kuma a dokar tsarin aiki idan aka kama mutum da laifi abu na farko da akeyi ana duba file d’insa, idan har ba’a tab’a samunsa da wani laifi ba to ana masa uzuri, acikin mu nan babu wanda bai san irin tsarin aiki na Alhaji Maiwada ba, tun yana k’aramin ma’aikaci ake yabon iya aikinsa, yarik’e matsayi kala-kala ba’a tab’a samunsa da karb’ar cin hanci ko so d’aya ba, har kawo warsa wannan matsayin ba’a tab’a kamasa da wani laifi daya sab’a ma doka ba, kuma wannan abu daya faru ina ganin kamar akwai lauje cikin nad’i, koma menene Allah ne yasan gaskiya, be kamata ace mun rufe ido munyi masa haka ba, idan mutum yayi ba dai-dai ba sai ajuya a kalli aikin kwarai nashi sai ayi masa hukunci dashi, dan haka ni dai a tawa shawarar ina ganin aja masa kunne a bashi dama ta biyu, kuma ya tsaya a aikinsa, kada yarik’a shiga aikin wasu, idan ya kiyaye shikenan, idan kuma aka sake kamashi sai ayi masa hukuncin daya dace.
Bayanin Mr. Kallah yayi ma mutane da dama dad’i, kuma sun gamsu da bayaninsa, nan take aka amince da shawararsa. Bayan sun gama rubutu aka rufe taro.
Alokacin Alhaji Maiwada yana zaune a inda aka tanadar ma baki dan ba dashi akayi taron ba, bayan sun fito Mr. Kallah yayi kiransa suka shiga ofis, su ukku ne a ofis d’in. Bayan ya gama karanto masa abinda suka yanke anan kowa yayi masa tashi nasihar.
Bayan sun fita ya rage su biyu Mr. Kallah ya dubeshi yana fad’in kayi hak’uri haka aikin kwastam ya gada, kafin nazo wannan matsayin nasha wahala sosai, matuk’ar kace zakayi gaskiya dole karik’a had’uwa da sharrin mutane, shawarar da zan baka ka tsaya akan aikin ka, kuma duk abinda zakayi karika tanadar kwakkwarar sheda, sannan ka rage shiga harkar Alhaji Marusa dan zai iya b’atar da kai. Alhaji Maiwada yace bakomai zan kiyaye, nagose sosai. Mr. Kallah yace bakomai.