ALKALI NE Page 21 to 30

Kud’i ya d’auko dubu d’ari biyar ya mik’a masa yana fad’in ga tawa gudummuwar. Alhaji yace kabarshi Mr. Kallah nagode. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad’in sunyi kad’an ko? Girgiza kai Alhaji yayi. Mr. Kallah yace to ka amsa. Amsa yayi yana masa godiya, haka sukayi sallama ya fito yana jinjina kirki irin na Mr. Kallah.
Mr. Kallah kuwa yana fita yayi murmushi, ya rasa ya akayi duk cikin ma’aikatansa yake jin nauyin Alhaji Maiwada, sosai yake masa kwarjini, duk da abinda yayi masa yayi ne dan ya k’arama kansa yarda awajen mutane amma ya rasa dalilin da yasa baya so Alhaji Marusa ya cutar dashi. Wayarsa ce tayi k’ara hakan yasa ya dawo daga tunanin da ya keyi.
**** ***
Haka Alhaji Maiwada ya koma bakin aikinsa, sosai ya canza daga yanda suka sanshi, babu ruwansa da kowa, abinda ya kamata shi yakeyi, kowa ya raba masa wajen aikinsa, kuma idan kayi aiki dole ka kawo rahoto ya duba, duk abinda ya faru sai anzo an sanar dashi, haka duk wad’an da zasu duba kaya dole su duba su da kyau, kuma dokar amsar cin hanci tana nan, sai dai ba ruwansa da kayan Alhaji Marusa, idan sunzo ma ba shine yake dubasu ba, amma duk da haka ana bincikasu yanda ya kamata, idan akwai abinda aka samu ana cirewa, shima Alhaji Marusan ya rage shigo da miyagun kwayoyi ta bodar Lagos, yace sai abun ya lafa.
Adebayo da Umar kowa yaga sun canza, domin hada sabbin motoci suka sake, sosai suke fantamawa, saboda suna cikin kud’i yasa basu damuwa da dokar ansar cin hanci ba.
A b’oye Alhaji yasa Abubakar da Moses suna bincika masa abinda yake faruwa, dan wannan abun daya faru yasa Moses yaji tausayin Alhaji, domin yasan wani abun daga cikin abinda su Adebayo sukayi, kawai yayi shiru ne saboda beda sheda, kuma yasan halin Alhaji Marusa matuk’ar ya ganoshi zai iya kashe shi, hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru, amma yayi alk’awarin sai ya taya Alhaji sun gano gaskiya koma me zai faru, hakan yasa ya had’e da Abubakar.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣3⃣
*Bayan dogon lokaci*
Wajen wani abokinsa mai suna *Tayo* Moses yaje domin ya taimaka masa, dan wannan hanyar ita kad’ai zasubi domin su gano gaskiyar komai, dan Moses yayi alk’awarin sai ya taimaki Alhaji saboda yasan abubuwa da yawa a wajen su Adebayo kawai beda sheda a hannu ne.
Tayo gurun kamfuta ne, kuma abinda ya karanta kenan. Babu b’ata lokaci ya bama Moses abinda zaiyi amfani dashi, wasu na’urori ya bashi sai yayi masa saitin da wayarsa hada kamfutarsa ta hannu duk ya had’a masa ya nuna masa yanda zaiyi amfani dasu. Godiya Moses yayi masa ya tafi.
A ofis d’in Adebayo ya fara zuwa yasa d’aya daga cikin na’urorin da aka bashi, sai yayi kok’ari yasa a cikin motarsa, daga nan yaje wajen da ake duba kaya nan ma yasa guda d’aya, saura d’aya ta rage kuma yana so ya sata a gidan Alhaji Marusa musamman inda yaga yana ganawa da mutane, duk da yana zuwa gidanshi ada yanzu ya rasa ta yanda zaije yasa wannan na’urar, kuma duk tafi sauran muhimmanci saboda yasan a wajen Alhaji Marusa za’afi sanin komai.
Shiru yayi yana tunanin abunyi sai ga Abubakar yazo, nan yayi masa bayanin abinda yake kok’arinyi. Abubakar yace gaskiya Moses ka kyauta, tun jiya nake tunanin hanyar da zamubi mu taimaki Alhaji, ashe har ka rigani.
Moses yace abinda nakeso shine yanda zan had’a wannan abun agidan Alhaji Marusa. Shiru Abubakar yayi kafin yace akwai maigadin gidansa nasanshi, mai zai hana mu je masa da maganar kila ya amince.
Moses yace kasan halin mutane da son kud’i, kada muje muna tunanin yasa yaki sakawa yaje ya fad’ama Alaji kasan dai bazai barmu ba.
Abubakar yace kai dai muje, inaji yau ba shine keda aikin kwana ba, idan mun tashi daga nan mu biya ta wajen da yake zama insha Allahu zai amince. Moses yace shikenan.
***
Bayan da suka tashi suka nufi wajen da Maigadin Alhaji Marusa yake zama. Yana ganin Abubakar ya saki murmushi yana fad’in kaga kwastam masu gidan kud’i, murmushi Abubakar yayi yana fad’in *Malan Hassan* bazaka dena fad’a mani wannan abun ba ko, ai ma’aikatan banki sune masu gidan kud’i.
Malan Hassan yace ai dole na fad’a, kowa yasan kwastam kuna morewar ku domin kunfi masu banki ‘yanci. Murmushi yayi anan suka gaishe shi. Malan Hassan yace wannan abokin aikin ka ne? Abubakar yace aikuwa dai Malan Hassan.
Zama sukayi Malan Hassan yana fad’in ina shugaban ku bawan Allah? Abubakar yace yanzu muka rabu ya wuce gida, ashe kaima kana tausaya masa? Malan Hassan yace ai dole na tausaya masa domin kowa yasan sharri akayi masa.
Moses yace Baba kaima kasan sharri akayi masa kenan? Malan Hassan yace ni ganau ne ba jiyau ba. Dariya Moses yayi yana fad’in Baba me kake nufi haka? Shima dariya yayi yana fad’in Abubakar ya fahimci abinda nake nufi ai.
Murmushi Abubakar yayi yana ma Moses bayani. Dariya Moses yayi yana fad’in Baba nima na fahimta yanzu. Abubakar yace wallahi Malan Hassan Alhaji mutumin kirki ne, kawai ya had’u da sharrin su Alhaji ne.
Gyara zama Malan Hassan yayi yana fad’in nan wajen babu tsaro ko zamuje cikin motar ku? Da sauri suka tashi domin abinda suke nema kenan.
Bayan sun zauna Moses ya kunna wayarsa saboda kada Malan Hassan yazo ya k’aryatasu idan lokacin hakan ya taso. Malan Hassan yace Abubakar Alhaji Marusa da kake gani mugun mutum ne, Allah dai yasa a k’ark’ashinsa zanci abinci shiyasa nake zaune a gidansa har yanzu, duk abinda kukaji ance Alhaji Maiwada yayi wallahi k’arya ne, abu ne wanda aka shiryashi, hatta da kayan da sukace sun b’ace ina tunanin k’arya ne, domin akwai abinda nake gani.
Abubakar yace Malan Hassan kaima baka da tabbaci kenan? Malan Hassan yace tunda ban gani da idona ba bazan ce ba, amma akwai abubuwan da nake gani agidanshi.
Mr. Kallah da kuke gani abokin Alhaji ne sosai, domin yana yawan zuwa gidansa idan yazo Lagos, sannan akwai wasu mutane biyu suma irin aikin ku sukeyi ina yawan ganinsu, d’aya bahaushe ne, d’ayan ko hausa bayaji sosai, sai wasu manyan mutane da ganinsu kasan mugaye ne, tunda nake ganinsu hankalina bai kwanta ba, babu yanda za’ayi naje naji abinda suke fad’a saboda acan wajen hutawarsa suke zama, amma tabbas sune suka k’ullama Alhaji Maiwada wannan sharrin.
Abubakar yace muma abinda muke tunani kenan, akwai abinda mukeso asa mana a wajen hutawarsa, babu wanda zaiyi mana wanan aikin idan ba kai ba Malan Hassan, shine nace muzo ko zaka taimaka mana domin Allah.
Malan Hassan yace kome kuke so zanyi maku domin nima nayi aikin lada. Na’urar Moses ya fiddo yana masa bayanin inda suke so yasa. Malan Hassan yace dan wannan ai mai sauki ne, kawai ku koya mani yanda zan sata.
Nan Moses yashiga koya masa yanda zaisa ta, bayan sun gama Malan Hassan yace gobe nine zanyi aikin kwana, kuma agoben zanje na saka kada ku damu, Allah zai taimaka mana, idan na gama zan fad’a maka Abubakar.