ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

Sosai sukaji dad’in abinda yayi masu, kud’i Abubakar ya ciro ya mik’a masa. Malan Hassan yace haba Abubakar, dan zanyi maka aiki sai ka bani kud’i? Abubakar yace ba biyanka nayi ba kawai kyautace. Amsa Malan Hassan yayi yana fad’in nagode sosai. Sallama sukayi masa suka tafi. 

***

Washe gari suka samu Alhaji a ofis sukayi masa bayanin abinda ake ciki. Shiru Alhaji yayi yana tunanin sunan Mr. Kallah da aka fad’a, girgiza kai yayi yana fad’in gaskiya ban yarda akwai sa hannun Mr. Kallah aciki ba, nasan dai abokin Alhaji Marusa ne, kila wani abun yake kaishi gidan amma bana tunanin zai iya aikata mani haka. 

Moses yace Sir, kada kayi saurin yanke hukunci, mujira ai gaskiya zata nuna kanta. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in nagode sosai. Abubakar yace haba Alhaji wannan ba wani abu bane, insha Allahu gaskiya zata fito.

 Alhaji yace wallahi ba saboda kud’ina su dawo nakeso a gano gaskiya ba, ina so na wanke kaina awajen mutane, sannan kowa yasan abinda Alhaji Marusa yake aikatawa. Moses yace zamu kamasu ne zasuci Ubansu. Murmushi Alhaji yayi yana fad’in nagode. 

A daren ranar Malan Hassan ya kira Abubakar ya fad’a masa ya gama komai. Abubakar yace nagode Malan Hassan Allah ya bamu sa’a. Yace amin. 

**** ****

Haka rayuwa tacigaba da tafiya kowa yana aikinsa, duk hutu Ra’eez yana zuwa yayi sati d’aya ya koma saboda islamiya, alokacin da yazo sai da yayita tambayar dalilin da yasa suka canza gida. Ummunsa ce tayi masa dabara tace b’arayi suka matsa masu shiyasa suka tashi. Da wannan suka rufe bakinsa. 

Tun bayan da Alhaji Marusa yayi ma Alhaji Maiwada wannan abun sai ya fara samun matsala a kasuwancinsa, cinikin da yakeyi sosai ya fara raguwa, ga yawan asara da yakeyi a wajen kawo masa kaya, amma da yake ya tara hakan yasa dukiyarsa bata girgiza ba, sai dai duk wacce ya fitar aka saro kaya da wuya ta dawo fiye da yanda take. 

Haka su Umar da Adebayo komai ya fara lalace masu, mata da shaye-shaye ne suke cinye masu kud’i, duk yawan kud’in da suke samu basa masu afki. 

Alhaji Maiwada kuwa tamkar anasa ma dukiyarsa taki, sosai yake samun bud’i, sai dai duk bud’in da yake samu sai yaji tsoron ya sayi kadara a Lagos, hakan yasa ya turama Alhaji Mansur kud’i ya saya masa gidaje a kano ya zuba masa haya, sannan ya bud’ema Ra’eez asusu a banki yana zuba masa kud’i a ciki dan baya son yarik’a tara kud’i a bankinsa dan ya tsorata da abinda ya faru. 

**** ****

Dogon hutu su Ra’eez suka samu saboda sun zana jarabawa ta aji ukku zasu shiga babban aji idan sun koma, hakan yasa ya rok’i Abbunsa akan ya barshi yazo ko wata d’aya yayi tunda hutun dogo ne. 

Alhaji yace Ra’eez wata d’aya yayi maka yawa, Labiba zata wuceka a islamiya da sauran ‘yan ajinku, kuma kaga shirye-shiryen sauka kukeyi. Kuka Ra’eez yasa mashi yana rokonsa. 

Ummu ce tasa baki tana fad’in tunda Ra’eez ya taso baka tab’a zaman sati biyu dashi ba, baka tsoron rashin mu ya tab’a karantunsa? kabarshi tunda har ya fito ya rok’a yakamata muyi masa wannan alfarmar, karatu ba wani abu bane tunda yana da kok’ari zai iske su, idan yazo nan bazai rik’a fita yawo ba sai yarik’a karatu. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in shikenan Uwargida na amince, nima inaso ya zauna akusa dani, rayuwar Lagos d’ince take bani tsoro shiyasa bana son yazo yayi rayuwa acikinta, nafiso sai ya kammala karatunsa yayi hankali kafin yazo muzauna. 

Murmushi tayi tana fad’in nagode. Alhaji yace Ummun Ra’eez nifa ban yarda dake ba, naga kamar kin canza kwana biyu anya babu ajiyata kuwa? Dariya tasa ta rufe fuskarta. Alhaji yace wallahi bazan iya hakura ba tashi muje asibiti aduba idan ma babu komai duk zan gani. 

Dariya tayi tace dan Allah ka barni bana son tashi. Mikewa yayi yana fad’in abu mai sauki bara na d’auke ki. Rik’eshi tayi tana fad’in zan fad’a maka. Zama yayi yana fad’in to inajinki. Duk’ar da kai tayi tana fad’in maganarka gaskiya ce, Ra’eez zai samu K’anwa ko K’ani. 

Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Alhaji, rungumeta yayi yana fad’in narasa bakin magana, Allah yayi maki albarka Bilkisu, tashi muje a duba aga ko wata nawa ne. Tashi tayi tana fad’in tunda kace sai anje muje. 

Suna zuwa asibiti aka gano cikin watansa ukku, sosai yayi murna nan suka koma gida. Waya ya d’auka ya kira Alhaji Mansur yana masa albishir. Sosai sukayi farin ciki, anan Alhaji yake fad’ama Alhaji Mansur Ra’eez zeyi hutun wata d’aya anan idan yazo. Alhaji Mansur yace wannan yayi dai-dai, amma idan yazo yarik’a karatu bana son a wuceshi. Alhaji yace insha Allah.

**** ***

Tunda Ra’eez yazo baya zuwa ko ina, iyakar yawansa Malan Sani ya kaishi gidansa wajen Rumaisa wacce yanzu tayi wayau tana a aji ukku firamare, duk lokacin da yaje yana koya mata karatu, idan suka gama Malan Sani ya maidashi. 

Sosai yake karatunsa, inda bai gane ba ya tambayi Ummunsa ko Abbunsa, zuwansa hutu suka k’ara shakuwa da Abbunsa, koda yaushe suna tare, yana dawowa ofis suke zama suyi ta fira, wasu abubuwan haka nan Alhaji yake fad’a masa duk da yasan wayonsa bazai d’aukesu ba, amma sanin natsuwar Ra’eez yasa Alhaji yake fad’a masa komai nasa. 

Lokacin da hutu ya k’are haka suka had’a masa komai shida Labiba, alokacin Alhaji ya samu hutu sai suka tafi gaba d’aya kano. Sosai Maman Labiba taji dad’in zuwansu ita da Mijinta. 

Satinsu biyu a Kano sannan suka koma Lagos cike da kewar juna. Haka Ummun Ra’eez ta aika ma Maman Rumaisa da tsaraba mai yawa, sannan ta aika Malan Sani yaje ya d’auko Ladi, itama ta samu tsaraba sai godiya takeyi. 

**** ***

Dube-dube Malan 

Hassan yakeyi a wajen daya aje na’urar da su Abubakar suka bashi amma be gani ba, mamaki ne ya kamashi ganin inda ya aje abun babu komai a wajen. 

Motsin da yaji ne yasa shi saurin juyawa, Alhaji Marusa ya gani da wani mai aikinsa inyamuri. Jikin Malan Hassan ne ya fara rawa ya fara kok’arin barin wajen.

 Alhaji Marusa yace Malan Hassan a iya sanina aikin ka agidan nan shine gadi, ko mai kula da tsaftar wajen nan baya aiki da dare, sai gashi kai kuma kazo wajen da dare bayan nasan bakwa zuwar mani cikin gida, ko dai wani abu ka aje kake nema? Jikin Malan Hassan yana rawa ya fara matsawa da baya. 

Kallon wanda suke tare Alhaji Marusa yayi hakan yasa kawai yaje ya damko Malan Hassan, juyawa Alhaji Marusa yayi ya nufi wani b’angarenashi da yake gefe, haka mutumin ya d’auki Malan Hassan suka nufi wajen. 

*** ***

Mamaki ne yayi ma Alhaji Maiwada yawa ya kasa furta komai saboda abinda idanuwansa suke gani da abinda kunnuwansa suke ji.

 Zaune suke a ofis d’in Alhaji bayan an tashi daga ofis, Moses ne da Abubakar da Alhaji suke kallon abinda Moses ya tara a kamfutarsa wanda ya d’auka. 

***

Abinda yafi basu mamaki d’aukar da akayi wajen da ake duba kaya, wani kwali ne aka bud’e na taliya amma ba taliyar bace aciki duka, rabin kayan miyagun kwayoyi ne aciki hada hodar ibilis. Adebayo ne yake waya da Alhaji Marusa yana fad’in kayan sunzo komai lafiya, bayan ya gama ya kalli Umar yana fad’in Alhaji Marusa yace a fitar da kayan yanzu kada abari Sir, ya dubasu tunda anci sa’a bayanan. Umar yace ai tunda Alhaji Marusa yayi ma Alhaji hankali yanzu ya sakar masa mara, kai ko mutum ya rasa katafaren gida irin wannan ai dole ya tsorata, gaskiya Alhaji Marusa bai da imani, gashi dai ya kulla masa sharri kowa ya yarda ya shashi asarar gida, kuma ya saye gidan sannan ya cabke kud’insa ga kayansa babu wanda yayi ciwon kai muma an raba damu. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button